Abin da Za a Ce Game da Mujallun
Oktoba-Disamba
“Wasu aure ba sa daɗewa fiye da shekara ɗaya. Mene ne kake tsammani zai taimaki irin waɗannan auren? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da aka faɗa a nan. [Karanta Matta 19:5, 6.] Allah ne ya kafa aure. Saboda haka wannan talifin da ya soma daga shafi na 10 ya nuna yadda Kalmarsa za ta iya taimaka wa mutane su shawo kan ƙalubale da za su iya tasowa a aure kuma su koya abubuwa da ake bukata don aure ya daɗe.”
Nuwamba
Karanta 2 Timotawus 3:16. Sai ka ce: “Ka amince kuma kana jin cewa za mu iya dogara ga komi da Littafi Mai Tsarki ya ce? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan talifin ya bayyana ko kimiyyar haƙa ƙasa da tahiri sun jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ƙasar Masar ta dā.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 15.
Oktoba-Disamba
“Wasu sun gaskata cewa miyagun ayyuka za su daina wata rana. Wasu kuma suna mamaki ko wannan ranar za ta taɓa zuwa. Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta 2 Timotawus 3:1.] Furcin nan “kwanaki na ƙarshe” yana nuna cewa akwai abin da zai zo ƙarshe. Amma mene ne wannan? Wannan talifin da ya soma daga shafi na 5 ya tattauna yadda Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa ƙarshen miyagun ayyuka zai zo.”
Disamba
“Ka taɓa yin tunanin dalilin da ya sa ake yin bikin Kirsimati a ranar 25 ga Disamba duk da cewa Littafi Mai Tsarki bai faɗa ranar da aka haifi Yesu ba? [Ka bari ya ba da amsa.] Kamar yadda wannan ayar ta nuna, ba zai yiwu ba a haifi Yesu a lokacin ɗari. [Karanta Luka 2:8.] Wannan mujallar ta bayyana tushen wasu sanannun al’adun Kirsimati.”