Abin da Za a Ce Game da Mujallun
Afrilu-Yuni
“Mutane suna da ra’ayi dabam-dabam game da Yesu. Menene wasu abubuwan da ka sani game da Yesu? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi a nan. [Karanta Kolosiyawa 1:16.] Wannan ɗaya ne cikin abubuwa da yawa da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu. Talifin da ke shafi na 5 na wannan mujallar ya tattauna wasu abubuwa da ya kamata ka sani game da Yesu.”
Yuni
“Akan karɓi kuɗi a coci don yin baftisma, bikin aure, da jana’iza. Kana tsammani cewa hakan ya dace kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka dubi wannan umurni da Yesu ya ba almajiransa. [Karanta Matta 10:7, 8b.] Wannan talifin ya nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da karɓar kuɗaɗe don ayyukan addini.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 22.
Yuli-Satumba
“Yawancinmu muna da namu addinin. Kana tsammanin cewa Allah ya damu da yadda muke bauta masa kuwa? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta Matta 15:9.] Wannan talifin ya tattauna ɓangarori huɗu na bauta ta gaskiya kamar yadda Yesu ya nuna.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 16.
Yuli
“Wannan tattalin arziki ya jawo alhini da yawa. Waɗanda sun daina yin aiki suna alhini, kuma waɗanda suke aiki suna alhini don kada su ɓatar da aikinsu. Kana tsammani cewa wannan shawara mai kyau ce da za ta iya taimaka mana mu jimre kuwa? [Karanta Matta 6:34. Sai ka bari ya ba da amsa.] Wannan mujallar ta ba da shawarwari masu aiki game da yadda za mu yi amfani da dukiyarmu da motsin ranmu yadda ya dace.”