Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Agusta
“Duniya a yau tana cike da ƙiyayya da kuma rashin aminci. Kana ganin zai yiwu mu yi rayuwa a duniya inda kowa zai amince da juna kuma mu yi zaman lafiya da juna kuwa?” [Ka bari ya ba da amsa.] Sai ka nuna masa bangon baya na mujallar Yuli–Agusta kuma ka tattauna sakin layi na farko a ƙarƙashin tambaya ta 2. Ka karanta aƙalla nassi guda ɗaya daga cikin waɗanda aka rubuta a wurin. Ka ba mutumin mujallun kuma ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna sakin layi da ke biye.
Abin lura: A nuna yadda za a yi amfani da wannan gabatarwar sa’ad da ake taron fita wa’azi a ranar 3 ga Agusta.
Hasumiyar Tsaro Yuli–Agusta
“Muna ƙarfafa mutane su yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Shawara da ake samu daga cikinsa ta taimaka wa mutane da yawa su kusaci Allah kuma su kyautata dangantakarsu da juna a cikin iyali. Alal misali, ka lura da labarin wani mutum da Littafi Mai Tsarki ya taimaka masa ya daina fushi da yin faɗa da aka rubuta a shafuffuka na 8 da 9.” Ka nuna masa talifin.
Awake! Agusta
“Yawancinmu muna son mu riƙa rayuwa ba iyaka. Shin kana ganin ci gaba da ake samu a kimiyya zai sa mu yi rayuwa har abada a nan gaba? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da wannan alkawari mai ban sha’awa. [Ka karanta 1 Korintiyawa 15:26.] Amma ta yaya Allah zai cim ma hakan, ta kimiyya ne ko ta wata hanya dabam? Kuma me ya sa muke tsufa kuma mu mutu? Wannan mujallar ta ba da amsoshin waɗannan tambayoyin.”