Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/1 pp. 3-7
  • Batsa—Tana da Lahani ko A’a?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Batsa—Tana da Lahani ko A’a?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ta yaya batsa take shafan mutane?
  • Ta yaya batsa take shafan iyalai?
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da batsa?
  • Yadda Za Mu Kāre Kanmu Daga Daya Cikin Dabarun Shaidan
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Na Shaku da Kallon Hotunan Batsa
    Tambayoyin Matasa
  • Me Za Ki Yi Idan Maigidanki Yana Kallon Batsa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/1 pp. 3-7

ABIN DA KE SHAFIN FARKO

Batsa—Tana da Lahani ko A’a?

Batsa ta zama ruwan dare gama-gari a duniya a yau.a Ana iya ganin batsa a tallace-tallace, fina-finai, talabijin, wasannin bidiyo, mujallu, tufafi na yayi, wayoyin zamani, na’urorin tafi-da-gidanka dandalin intane da kuma tsarin sadarwa na aika saƙonnin hotuna ta Intane. Ana kuma jin ta a waƙoƙi. Batsa dai ta zama wani abin yayi yanzu. Mutane a ƙasashe da yawa yanzu suna jin daɗin kallo da kuma sauraron batsa fiye da dā.—Ka duba akwatin nan mai jigo “Sakamakon Binciken da Aka Yi Game da Batsa.”

Yadda ake nuna batsa a yau ma yana canjawa. Farfesa Gail Dines ta rubuta cewa: “Hotunan batsa sun daɗa muni yanzu kuma mutane da yawa suna amince da hakan.”

Mene ne ra’ayinka game da hakan? Kallo da kuma sauraron batsa yana da kyau ne ko abu ne mai lahani? Yesu ya ce: “Kowane itacen kirki ya kan fitar da ’ya’yan kirki; amma mummunan itace ya kan fitar da munanan ’ya’ya.” (Matta 7:17) Wane irin ’ya’ya ne ko sakamako ake samu daga kallo ko sauraron batsa? Don mu sami amsoshin waɗannan tambayoyin, bari mu tattauna wasu tambayoyi da ake yi game da batsa.

Ta yaya batsa take shafan mutane?

ABIN DA MASANA SUKA FAƊA: Batsa jaraba ce sosai, har ma wasu masu bincike da waɗanda suke taimaka wa mutane su fita sha’anin batsa sun kamanta ta da jarabar shaƙar hodar iblis.

Brian,b wanda kallon batsa a Intane ya zama masa jaraba, ya ce: “Babu abin da yake hana ni kallon batsa, kuma sa’ad da nake kallo sai in ji kamar ina wata duniya ne. Jikina yakan yi rawa kuma kaina ya riƙa ciwo. Na yi yunƙurin daina wannan halin, amma da shigewar shekaru ya zama min jiki.”

Mutane masu son batsa ba sa so mutane su san cewa suna da wannan halin. Saboda haka, sukan kalla ko saurare ta a ɓoye. Ba abin mamaki ba ne cewa mutane da yawa a cikin su suna jin kaɗaici da kunya da baƙin ciki da fushi kuma suna alhini sosai. A wani lokaci ma, sukan yi tunanin kashe kansu. Serge, wani mutum da ya saba sauko da hotunan batsa a cikin wayarsa kusan kullum ya ce: “A kowane lokaci, ina tunanin kaina ne kaɗai kuma na damu ƙwarai. Sai na ji kamar ba ni da mutunci, ba ni da gaskiya, na kaɗaita kuma ba ni da mafita. Kunya da tsoro sun hana ni neman taimako.”

Idan mutum ya kalli batsa na ɗan lokaci kawai ko da ba da saninsa ba ne, hakan yakan kawo mummunan sakamako. Judith Reisman, wata masaniya mai bincike a kan batsa ta yi bayani a gaban kwamitin Majalisar Dattijai na Amirka cewa: “Hotunan batsa suna shiga ƙwaƙwalwar mutum su yi tasiri bisa kansa nan da nan, sa’an nan su canja tunaninsa kuma yana da wuya a mance da su.” Susan, wata ’yar shekara 19 da ta ɗan kalli batsa ba da saninta ba ta ce: “Hotunan sun zauna daram a zuciyata. Farat ɗaya nakan tuna da su. Kamar dai ba zan taɓa iya mantawa da su ba.”

GASKIYAR AL’AMARIN: Batsa muguwar jaraba ce da ke ɓata mutum.—2 Bitrus 2:19.

Ta yaya batsa take shafan iyalai?

ABIN DA MASANA SUKA FAƊA: “Batsa tana raba ma’aurata da iyalai gaba ɗaya.”—Littafin nan The Porn Trap, wanda Wendy da kuma Larry Maltz suka wallafa.

Batsa tana raba aure kuma tana ɓata dangantaka da ke cikin iyali ta wajen

  • Sa ma’aurata su daina amince da juna, su daina kusanta da kuma ƙaunar juna.—Misalai 2:12-17.

  • Sa maigida ko matar aure ta kasance da son zuciya, tana kashe zumuncin da ke tsakanin ma’aurata kuma ta sa su daina gamsuwa da juna.—Afisawa 5:28, 29.

  • Sa mutane su kasance da munanan sha’awoyi da kuma tunani marar kyau.—2 Bitrus 2:14.

  • Sa masu kallonta su tilasta wa abokiyar aurensu ta yi jima’i a hanyar da ba ta dace ba.—Afisawa 5:3, 4.

  • Sa ma’aurata kallon waje har ma da yin zina.—Matta 5:28.

Littafi Mai Tsarki ya umurci ma’aurata cewa kada su ‘ci amanar’ juna. (Malakai 2:16) Zina cin amana ne da za ta iya ɓata aure kuma ta kai ga rabuwa da kisan aure. Kuma idan ma’aurata suka rabu da juna, hakan yana jefa yaransu cikin matsala.

Akwai wata mummunar hanya kuma da batsa take shafan yara. Brian, wanda aka yi maganarsa ɗazu ya ce: “Sa’ad da nake wajen ɗan shekara goma, ina wasan ɓuya wata rana sai na tarar da mujallun batsa na mahaifina. Sai kurum na soma kallon waɗannan hotunan a ɓoye. Ta hakan ne na koyi wannan mummunan hali da na ci gaba da yi har na girma.” Bincike ya nuna cewa batsa takan sa matasa su soma jima’i tun lokacinsu bai kai ba, kuma su zama masu lalata, masu jima’i a hanyar da ba ta dace ba, har ma su kasa daidaita tunaninsu da yadda suke ji.

GASKIYAR AL’AMARIN: Batsa tana ɓata dangantaka mai kyau tsakanin mutane kuma tana jawo ɓacin rai da azaba.—Misalai 6:27.

Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da batsa?

KALMAR ALLAH TA CE: ‘Ku matar da gaɓaɓuwanku fa . . . game da fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa, wato bautar gumaka ke nan.’—Kolosiyawa 3:5.

A taƙaice, Jehobahc ya tsani batsa. Ba wai ba ya son mata da miji su yi jima’i ba. Jehobah ya halicci ’yan Adam a hanyar da za su iya yin jima’i domin ma’aurata su faranta wa juna rai, su kusaci juna kuma su iya haifan ’ya’ya.—Yaƙub 1:17.

To, me ya sa muke cewa Jehobah ya tsani batsa? Ka yi la’akari da wasu dalilai:

  • Ya san cewa batsa za ta iya ɓata rayuwar mutum gaba ɗaya.—Afisawa 4:17-19.

  • Yana ƙaunar mu kuma yana so ya kāre mu daga abin da zai iya lahanta mu.—Ishaya 48:17, 18.

  • Jehobah yana so ya kāre aurenmu da kuma iyalinmu.—Matta 19:4-6.

  • Yana so mu kasance da ɗabi’a mai tsabta kuma mu riƙa ɗaukan mutane da mutunci.—1 Tasalonikawa 4:3-6.

  • Yana so mu daraja baiwar haihuwa da ya ba mu kuma mu yi amfani da ita a hanyar da ta dace.—Ibraniyawa 13:4.

  • Jehobah ya san cewa batsa tana sa mutum son zuciya da mugun tunani kuma tana ɗaukaka ra’ayin Shaiɗan game da jima’i.—Farawa 6:2; Yahuda 6, 7.

GASKIYAR AL’AMARIN: Batsa tana ɓata dangantakar mutum da Allah.—Romawa 1:24.

Amma, Jehobah yana da jin ƙai kuma yana so ya taimaka wa waɗanda suke so su fita sha’anin batsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji cike da tausayi ya ke, mai-nasiha, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai kuma. Gama ya san tabi’armu; Ya kan tuna mu turɓaya ne.” (Zabura 103:8, 14) Yana ba wa masu tawali’u damar zuwa wurinsa don su samu ‘jinƙai, a kuma yi musu alherin da zai taimake su a kan kari.’—Ibraniyawa 4:16; ka duba akwatin nan mai jigo, “Matakai da Mutum Zai Ɗauka don Ya Daina Kallon Batsa.”

Mutane da yawa sun sami taimako daga wurin Allah. Wannan taimakon yana da amfani kuwa? Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wasu da suka iya daina munanan halaye: “Aka wanke ku, . . . aka tsarkake ku, . . . aka baratar da ku cikin sunan Ubangiji Yesu Kristi, cikin ruhun Allahnmu kuma.” (1 Korintiyawa 6:11) Kamar manzo Bulus, waɗannan mutane za su iya cewa: “Allah ne cetona: . . . ba kuwa zan ji tsoro ba: gama Ubangiji Yahweh ƙarfina ne da waƙata: ya kuma zama cetona.”—Ishaya 12:2.

Susan, wadda ta iya shawo kan jarabar kallon batsa ta ce: “Jehobah ne kaɗai zai iya taimaka maka ka fita sha’anin batsa. Idan ka roƙe shi ya taimake ka kuma ya ja-gorance ka, zai taimake ka ka kasance da dangantaka mai kyau da shi. Ba zai ƙyale ka ba.”

Matakai da Mutum Zai Ɗauka don Ya Daina Kallon Batsa

Ka san wani da yake ƙoƙari ya shawo kan jarabar kallon batsa? Ka yi la’akari da wasu matakai da suka taimaka wa mutane da yawa su daina kallon batsa.

1. Ka yi addu’a ga Allah.

“Abu mafi muhimmanci da mutum zai yi don ya daina kallon batsa shi ne neman taimakon Jehobah ta yin addu’a.”—Franz.

Jehobah zai iya ba mutumin ruhu mai tsarki don ya ƙarfafa shi ya ‘nufi abin da ke kyakkyawan nufinsa, kuma ya aikata shi.’ (Filibiyawa 2:13, Littafi Mai Tsarki) Idan mutumin ya bar ruhu mai tsarki ya ja-gorance shi, hakan zai taimaka masa ya shawo kan ‘guri da sha’awoyi’ da ba su dace ba.—Galatiyawa 5:16, 24.

2. Ka nemi taimako daga wurin wasu.

“Da yake jarabar kallon batsa abin kunya ne da ake yi a ɓoye, hakan zai iya hana mutum neman taimako. Za ka ɗauka cewa za ka iya shawo kan jarabar da kanka. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Sai dai an taimake ka ne za ka iya shawo kan jarabar. Saboda haka, na ƙasƙantar da kaina kuma na gaya wa matata. Na kuma nemi taimako daga wani aminina. Wannan shi ne abu mafi wuya da na taɓa yi a rayuwata, amma na sami taimakon da nake bukata.”—Yoshi.

Mutum na bukatar ya ƙudura aniya kuma ya kasance da gaba gaɗi kafin ya iya gaya ma wasu. Duk da haka, gaya wa mutane mataki ne mai kyau da mutum zai ɗauka don ya shawo kan wannan jarabar kuma ya kyautata dangantakarsa da iyalinsa da abokansa. Susan, wadda aka yi maganarta ɗazu ta ce: “Daga baya, sai na ji kamar na sauke wani babban kaya. Ko da yake na ji nauyin neman taimako, amma yanzu na sami kwanciyar hankali da kuma lamiri mai kyau.”—Yaƙub 5:16.

3. Ka san abubuwan da za su iya tayar da sha’awar kuma ka guje su.

Wane irin yanayi ko tunani ne zai iya tayar da wannan mummunar sha’awar? Shiga dandalin Intane ne ko kallon talabijin da daddare ko karanta wasu irin mujallu ko zuwa shaƙatawa a bakin teku ko yunwa ko fushi ko kaɗaici ko gajiya ne? Sven ya ce: “Ka fahimci abubuwan da za su iya sa ka faɗa a cikin wannan halin kuma ka yi ƙoƙari don ka guje su.” Yesu ya ce: “Idan idonka na dama yana sa ka yi tuntuɓe, ka cire shi, ka yar.”—Matta 5:29.

Franz ya bayyana cewa: “A duk lokacin da zuciyata ta motsa ni in kalli mace da sha’awa, ina addu’a ga Jehobah nan da nan kuma in kawar da idanuna.” Wannan uban iyali mai aminci, Ayuba ma ya ce: “Na yi wa’adi da idanuna; yaya fa zan yi sha’awar budurwa?”—Ayuba 31:1.

4. Ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah.

Franz ya ƙara da cewa: “Ka riƙa tunanin abubuwa masu kyau kuma ka duƙufa a yin ayyukan da za su kyautata dangantakarka da Allah.”

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Iyakar abin da ke mai-gaskiya, iyakar abin da ya isa bangirma, iyakar abin da ke mai-adalci, iyakar abin da ke mai-tsabta, iyakar abin da ke jawo ƙauna, iyakar abin da ke da kyakkyawan ambato; idan akwai kirki, idan akwai yabo, ku maida hankali ga waɗannan . . . , Allah kuwa na salama za ya zauna tare da ku.”—Filibiyawa 4:8, 9.

a “Batsa” tana nufin duk wani abin da ake karantawa ko kallo ko saurarawa, da aka shirya musamman don ta da sha’awar lalata. Waɗannan abubuwan sun ƙunshi hotuna da bidiyon tsirarun mutane, littattafai da kuma sauti game da lalata.

b An canja ainihin sunayen mutanen da aka ambata a wannan talifin.

c Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.

SAKAMAKON BINCIKEN DA AKA YI GAME DA BATSA

KOWANE SAKAN: Mutane kusan 30,000 ne suke shiga dandalin batsa.

KOWANE MINTI: Masu amfani da Intane suna aika wa mutane saƙonnin imel na batsa fiye da MILIYAN 1.7.

KOWACE AWA: Bidiyoyin batsa kusan guda BIYU ne ake ƙaddamarwa a Amirka.

KOWACE RANA: A ƙasar Amirka kaɗai, mutane suna karɓan hayan bidiyon batsa fiye da MILIYAN BIYU.

KOWANE WATA: Kusan kashi 90 na samari da kashi 30 na ’yan mata ne suke kallon batsa a ƙasar Amirka.

KOWACE SHEKARA: Masana’antun yaɗa batsa a faɗin duniya suna samun wajen DALA BILIYAN 100.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba