Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 3/15 pp. 30-31
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Batsa—Tana da Lahani ko A’a?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Yadda Za Mu Kāre Kanmu Daga Daya Cikin Dabarun Shaidan
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Me Za Ki Yi Idan Maigidanki Yana Kallon Batsa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Na Shaku da Kallon Hotunan Batsa
    Tambayoyin Matasa
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 3/15 pp. 30-31

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Shin za a iya yi wa Kirista yankan zumunci domin ya shaƙu da kallon hotunan batsa?

▪ Hakika. Shi ya sa yake da muhimmanci mu guji kallon kowanne irin hotunan batsa. Wannan ya haɗa da littattafai da jaridu da hotuna da fina-finai da dandalin Intane da ke nuna ko kuma bayyana batsa.

Ana iya ganin hotunan batsa a ko’ina a duniya yau. Intane ya sa ya kasance da sauƙi sosai mutane su kalli hotunan batsa, kuma ya sa wannan hali marar kyau ya ƙaru sosai. Wasu mutane sun ga hotunan batsa a Intane ba tare da son ransu ba. Amma wasu da gangan sun nemi waɗannan hotunan batsa. Suna samun sauƙin yin hakan a ofishinsu ko kuma gidajensu inda babu wanda ke kallonsu. Me ya sa hakan yake da lahani sosai ga Kirista?

Gargaɗin da Yesu ya ba da ya bayyana dalilin: “Dukan wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Mat. 5:28) Gaskiya ne cewa jima’i tsakanin mata da miji ya dace kuma suna iya mora yin hakan. (Mis. 5:15-19; 1 Kor. 7:2-5) Amma ba hakan yake da hotunan batsa ba. Maimakon haka, hotunan batsa suna sa mu riƙa tunanin yin lalata, kuma abin da Yesu ya yi mana gargaɗi a kai ke nan. Saboda haka, karanta ko kuma kallon batsa ya saɓa wa dokokin Jehobah: “Ku matar da gaɓaɓuwanku fa waɗanda ke a duniya; fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa, wato bautar gumaka ke nan.”—Kol. 3:5.

Amma, mene ne zai iya faru idan Kirista ya kalli hotunan batsa sau ɗaya ko biyu fa? Za a iya kwatanta yanayinsa da na wani marubucin zabura mai suna Asaph: “Amma ni dai ƙafafuna sun kusa su zāme. Saura kaɗan takawata ta zame.” Idan Kirista ya kalli hotunan da ke nuna maza ko mata da ke tsirara ko kuma mutanen da ke yin jima’i, ba zai samu lamiri mai kyau kuma ya kasance da salama da Allah ba. Zai ji kamar Asaph, wanda ya ce: “Duk yini masifa ni ke sha, da horo kuma kowace safiya.”—Zab. 73:2, 14.

Ya kamata Kiristan da ke kallon hotunan batsa ya san cewa hakan yana shafar dangantakarsa da Jehobah kuma yana bukatar taimako. Zai iya samun wannan taimakon daga wurin dattawa a ikilisiya: “’Yan’uwa, idan an iske mutum a cikin kowane laifi, ku da kuke masu-ruhaniya, cikin ruhun tawali’u ku komo da irin wannan; kana lura da kanka.” (Gal. 6:1) Dattijo guda ko kuma biyu suna iya taimaka masa. Suna iya masa addu’a kuma su kasance da bangaskiya cewa Jehobah zai ‘ceci mai-ciwon, kuma za a gafarta masa.’ (Yaƙ. 5:13-15) Waɗanda suka nemi taimako don su daina kallon hotunan batsa za su amfana domin za su samu dangantaka mai kyau da Jehobah.—Zab. 73:28.

Amma, manzo Bulus ya ce wasu sun yi zunubi kuma ba su tuba ‘ga barin ƙazanta da fasikanci da mugun gurin ba.’a (2 Kor. 12:21) Farfesa Marvin R. Vincent ya rubuta game da kalmar Hellas da Bulus ya yi amfani da ita ga “ƙazanta.” Ya ce yana nufin ƙazanta da ba ta da tsabta ko kuma take da dauɗa. Akwai hotunan batsa masu bala’in dauɗa, kuma a cikinta ana nuna yadda namiji da namiji ko mace da mace suke jima’i, ko yadda mutane da yawa suke jima’i, ko yadda mutum da dabba suke jima’i, ko yin amfani da ƙananan yara don batsa, mutane da yawa su yi wa mutum fyaɗe, ko kuma yi wa mata mugunta, ko kuma zalunta ko ɗaure mutum don a yi jima’i da shi. Bulus ya ce wasu a zamaninsa suna da “duhun hankali.” Kuma, ‘sun wuce gaban su ji, har sun ba da kansu ga lalata, domin su aika dukan ƙazanta tare da kwaɗayi.’—Afis. 4:18, 19.

Bulus ya kuma ambata “ƙazanta” a Galatiyawa 5:19. Wani masani Ɗan Biritaniya ya ce “ƙazanta” da aka ambata a nan yana nufin yin sha’awar da ba ta dace ba. Kowanne Kirista zai yarda cewa irin batsa da muka ambata suna da dauɗa kuma suna sa mutane su yi sha’awar da ba ta dace ba. Bulus ya bayyana a Galatiyawa 5:21 cewa waɗanda suke waɗannan abubuwan “ba za su gaji mulkin Allah ba.” Hakazalika, idan mutum ya saba kallon hotunan batsa masu bala’in dauɗa da daɗewa, kuma bai tuba da barin wannan halin ba, ba zai iya ci gaba da kasancewa cikin ikilisiyar Kirista ba. Za a yi masa yankan zumunci domin a kāre ikilisiyar daga ƙazanta.—1 Kor. 5:5, 11.

Abin farin ciki ne sanin cewa wasu da suka kalli hotunan batsa sun nemi taimako daga wurin dattawa kuma sun canja halayensu. Yesu ya aririce Kiristocin da ke birnin Sardis na dā: “Ka ƙarfafa abin da ya rage, abin da yana bakin mutuwa . . . Ka tuna fa yadda ka karɓa da ka ji kuma; ka kiyaye shi kuma, ka tuba. Idan fa ba ka yi tsaro ba, . . . ba kuwa za ka san sa’an da zan auko maka ba.” (R. Yoh. 3:2, 3) Zai yiwu mutum ya tuba kuma a fizge shi daga cikin wuta.—Yahu. 22, 23.

Yana da kyau kada mu ƙyale hotunan batsa su gurɓata mu. Bari kowannenmu ya ƙuduri aniya cewa ba zai kalli hotunan batsa ba.

[Hasiya]

a Don sanin bambanci tsakanin “ƙazanta da fasikanci da kuma mugun guri” ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2006, shafuffuka na 29-31 na Turanci.

[Bayanin da ke shafi na 30]

Ya kamata Kiristan da ke kallon hotunan batsa ya san cewa hakan yana shafar dangantakarsa da Jehobah kuma yana bukatar taimako

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba