Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Nuwamba
“Mutane daga ƙasashe da kuma imani dabam-dabam suna addu’a kowacce rana. Kana tsammani cewa Allah yana ji da kuma amsa dukan addu’o’i?” Ka bari ya ba da amsa. Sai ka ba shi Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, kuma ku tattauna batun da ke kan magana na farko da ke shafi na 16 da kuma aƙalla nassi guda da aka yi ƙaulinsa. Ka ba da mujallun kuma ka shirya don koma ziyara don ku tattauna tambaya ta gaba.
Hasumiyar Tsaro Oktoba-Disamba
“Yana wa ma’aurata da yawa wuya su tattauna da juna. Kana tsammani mene ne zai taimaka musu? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. [Karanta 1 Bitrus 3:7 da Afisawa 5:33.] Mene ne mutum zai iya yi don ya tattauna cikin ladabi da aboki ko abokiyar aurensa? Wannan talifin da ya soma a shafi na 26 zai taimaka maka ka ga wasu shawarwari masu kyau daga Littafi Mai Tsarki.”
Awake! Nuwamba
“Idan muka kalli sararin samaniya sosai, kana ganin za mu kammala cewa da akwai Mahalicci ko kuwa kome sun wanzu ne farat ɗaya? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga abin da wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya kammala sa’ad da ya kalli sararin samaniya. [Karanta Romawa 1:20.] Wannan mujallar ta bayyana abin da masana kimiyya suka gano game da ƙwayoyin halitta na jiki da ya ƙara bayyana wannan batun.”