Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Disamba
“Mutane da yawa sun ɗauka cewa lokaci yana zuwa da Allah zai yi wa mutane shari’a bisa ga ayyukansu. Shin, kana ganin ya kamata mu yi marmarin zuwan ranar shari’a ne ko kuma mu yi fargaba? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka duba abin da aka ce a nan.” Ka ba mutumin Hasumiyar Tsaro ta Oktoba-Disamba, kuma ku tattauna ƙaramin jigo na farko da ke shafi na 24 tare, sa’an nan ka karanta aƙalla nassi ɗaya. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa za ka dawo don ku tattauna tambayar da ke gaba.
Hasumiyar Tsaro Oktoba-Disamba
“Mutane da yawa suna ganin cewa sai sun je sama ne za su more Aljanna. Shin, kana ganin zai yiwu mutane su ji daɗin rayuwa a duniya har abada? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka ga abin da Kalmar Allah ta ce game da wannan batun. [Ka karanta Zabura 37:10, 11.] Talifin da ya soma daga shafi na 13 na wannan mujallar ya ba da amsa ga wasu tambayoyi game da zuwa sama da wataƙila ka taɓa yi.”
Awake! Disamba
“Muna ziyartar ku ne domin mutane da yawa suna cikin wani hali na damuwa kuma hakan yana sa su fushi da juna. Kana ganin mutane a yanzu sun fi hasala ne fiye da dā? [Ka bari ya ba da amsa.] Wasu sun amince cewa muna rayuwa ne a wannan mawuyacin zamani da Littafi Mai Tsarki ya annabta a 2 Timotawus 3:1. [Ka karanta] Wannan mujallar ta tattauna haɗarurrukan da ke tattare da yin hasala, ya kuma ba da shawara a kan yadda za mu riƙa kasancewa da haƙuri.”