Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Disamba
“Mutane suna bin addinai iri-iri kuma suna bauta wa Allah a hanyoyi dabam-dabam. A ganin ka, mene ne ra’ayin Allah game da hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Yesu ya koyar game da wannan batun.” Ka miƙa wa maigidan kofi na Hasumiyar Tsaro ta Oktoba-Disamba kuma ka tattauna batun da ke ƙarƙashin kan magana na farko a shafi na 16 da kuma ka karanta aƙalla ɗaya daga cikin nassosin da aka yi ƙaulinsu. Ka ba shi mujallun, kuma ka gaya masa cewa za ka komo wurinsa don ku tattauna tambaya ta gaba.
Hasumiyar Tsaro Oktoba-Disamba
“Domin ajizanci, mutane suna yin zunubi sau da yawa. Kana tsammanin cewa Allah yana gafarta wa mutane zunubansu gaba ɗaya? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da wani nassin da ya ƙarfafa mutane da yawa. [Karanta Zabura 103:14.] Ta yaya Allah yake tuna cewa mu turɓaya ne? Wannan talifin da ke shafi na 23 ya tattauna wannan batun.”
Awake! Disamba
Karanta 2 Timotawus 3:16. Sai ka ce: “Wasu sun yarda cewa Allah ne ya hure Littafi Mai Tsarki, wasu kuma ba su yarda ba. Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Ko da yake ra’ayi ya bambanta a kan wannan tambayar, an yarda a ko’ina cewa babu littafin da ya sha gwagwarmaya sosai kamar Littafi Mai Tsarki. Wannan mujallar ta tattauna wasu ƙoƙarce-ƙoƙarcen da aka yi don a halaka Littafi Mai Tsarki da kuma hana karanta shi a ƙarnuka da dama. Ta kuma bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba a iya halaka shi ba.”