Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 11/14 p. 4
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 11/14 p. 4

Gabatarwa

Don Soma Nazari da Mutane a Asabar ta Farko a Watan Disamba

“Muna ɗan tattaunawa da maƙwabtanmu game da Mulkin Allah. Kana ganin Mulkin Allah zai amfani ’yan Adam kuwa?” [Ka bari ya ba da amsa.] Ka nuna masa bangon baya na Hasumiyar Tsaro ta Nuwamba–Disamba, kuma ku tattauna batun da ke ƙarƙashin tambaya ta biyu da kuma aƙalla ɗaya daga cikin nassosin da aka rubuta a wurin. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna sakin layi na gaba.

Hasumiyar Tsaro Nuwamba–Disamba

“Dalilin da ya sa na zo wurinka shi ne, ina so mu tattauna a kan yadda Littafi Mai Tsarki zai magance matsalolin ’yan Adam. Mai yiwuwa ka riga ka lura cewa matsalolinmu na daɗa ƙaruwa duk da ƙoƙarin da ake yi don a magance su. Shin kana ganin za a taɓa magance su kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga wani furuci mai ban ƙarfafa a cikin Littafi Mai Tsarki. [Karanta Ru’ya ta Yohanna 11:17, 18.] Shin ka lura da yadda za a magance matsalolinmu? Shafuffuka na 6 da 7 a cikin wannan mujallar sun nuna abin da Mulkin Allah zai cim ma a duniyar nan.”

Awake! Disamba

“Muna ziyartar ku ne saboda wani irin rashin lafiya da ya zama ruwan dare. Ƙungiyar Lafiya ta Duniya ta ce cututtuka da ke shafan ƙwaƙwalwa kamar baƙin ciki za su shafi mutum ɗaya cikin huɗu. Kana ganin ciwon ƙwaƙwalwa tana daɗa zama gama gari? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari cewa a nan gaba, ba za a sake yin rashin lafiya a duniya ba. [Karanta Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.] Wannan mujallar ta yi bayani a kan wasu abubuwa da ya kamata kowa ya sani game da taɓuwar hankali.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba