Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Janairu
“Muna son mu ji ra’ayinka game da wannan tambayar. Mene ne sunan Allah? [Ka bari ya ba da amsa.] Duba abin da wurin nan ya ce.” Sai ka ba mai gidan Hasumiyar Tsaro ta Janairu-Fabrairu, ka nuna masa talifin da ke bangon baya na mujallar, kuma ku tattauna tambaya ta farko. Ka karanta aƙalla nassi ɗaya. Ka ba da mujallun, kuma ka shirya yadda za ka koma ziyara a wurinsa don ku tattauna tambaya ta biyu.
Hasumiyar Tsaro Janairu-Fabrairu
“Mutane da yawa sun damu da yadda ƙarshen duniya zai kasance. Shin, kana ganin ya kamata mu ji tsoron zuwan ƙarshen duniya ne? [Ka bari ya ba da amsa.] Bisa ga bayanin da ke Littafi Mai Tsarki, akwai waɗanda za su tsira. [Ka karanta 1 Yohanna 2:17.] Wannan mujallar tana ɗauke da amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya bayar game da tambayoyi huɗu da mutane da yawa suke yi game da ƙarshen duniya.”
Awake! Janairu
“Muna ziyartar iyalai don mu tattauna bayanai masu muhimmanci da su. Shin, kana ganin iyalai za su amfana ne idan sun bi abin da Yesu ya faɗa a nan?” [Ka karanta Ayyukan Manzanni 20:35b. Sai ka bari ya ba da amsa.] Koya wa yara tarbiyya mai kyau bai da sauƙi a wannan duniya da aka cika nuna son kai. Wannan talifin ya tattauna hanyoyi uku da iyaye za su tarbiyyartar da yaransu don su riƙa girmama mutane.”