Ya Kamata Ku Tashi da Wuri Ne?
Wasu masu shela sun saba tashi daga wa’azi da rana domin wataƙila wannan ne lokacin da suka saba tashiwa a wa’azi. Hakika, domin yanayinsu ya bambanta, wasu suna iya tashiwa a wannan lokacin da suka ayana a duk ranar da suka fita wa’azi. Kuna tashiwa daga wa’azi domin wasu sun tashi ne kawai ko kuma domin wannan ne lokacin da aka saba tashi daga wa’azi a yankinku? Za ku iya ƙara ɗan lokaci a kan lokacin da kuka saba yi don ku yi wa’azi a inda mutane sun yi yawa, kamar a kan titi? Shin, sa’ad da kuka tashi kuma kuna hanyar komawa gida, za ku iya ziyarci mutum ɗaya ko biyu don ku yi nazari da su? Ku yi tunanin albarkar da za ku samu idan kuka sami mutum ɗaya mai sha’awar saƙon Littafi Mai Tsarki ko kuma idan kuka ba wani da ke wucewa mujallu! Idan ba mu tashi daga wa’azi da wuri ba, waɗannan ’yan mintocin da za mu ƙara a wa’azi hanya ce mai sauƙi na “yabon” Allah.—Ibran. 13:15.