Wa’azi a Kan Titi Mai Ba da Amfani
1. A wacce hanya ɗaya ce za mu iya yin koyi da Yesu?
1 Sa’ad da Yesu yake hidimarsa a duniya, bai yi jinkirin yin wa’azi ga mutanen da ya tarar da su a kan titi da kuma wuraren da akwai jama’a sosai ba. (Luk 9:57-61; Yoh. 4:7) Yana son mutane da yawa su ji wannan saƙo mai muhimmanci. A yau, yin hidima a kan titi hanya ce mai kyau na taimaka wa mutane su samu hikima daga wurin Allah. (Mis. 1:20) Za mu yi nasara sosai idan muka je wurin mutane kuma muka yi amfani da fahimi.
2. Ta yaya ake bukatar ɗaukan mataki sa’ad da ake hidima ta kan titi?
2 Ka Ɗauki Mataki: Ya fi dacewa a je a samu mutane maimakon tsayawa ko zaunawa a ɓangare guda don waɗanda suke wucewa su zo su same mu. Ka yi murmushi, ka kalle su a fuska kuma ka yi musu magana cikin fara’a. Idan kana tare da wasu masu shela, ya fi dacewa ku yi wa mutane ɗai-ɗai magana. Kana kuma bukatar ka yi ƙoƙari don ka koma ziyara wurin waɗanda ka tattauna da su. Idan zai dace, ka tambayi mutumin yadda za ku iya haɗuwa kuma. Wasu masu shela suna hidima ta kan titi a kai a kai a unguwa ɗaya, kuma hakan yana sa su samu zarafin yi wa mutum guda magana sau da yawa kuma hakan yana sa mutumin ya samu ci gaba.
3. Ta yaya za mu iya yin amfani da sanin ya kamata sa’ad da muke hidima ta kan titi?
3 Ka Yi Amfani da Sanin Ya Kamata: Ka yi amfani da sanin ya kamata don sanin ɓangaren da za ka tsaya a kan titi da kuma wanda za ka yi wa magana. Ba lallai sai ka yi wa dukan waɗanda suke wucewa magana ba. Ka yi lura. Alal misali, idan mutumin yana hanzari, zai fi dacewa ka ƙyale shi ya wuce. Idan kana wa’azi a wurin sana’a, ka mai da hankali don kada ka sa hankalin mai kula da wurin ya tashi. Ya fi dacewa ka yi wa waɗanda suke fitowa daga shagon magana ba waɗanda za su shiga ba. Ka je wurin mutane a hanyar da ba za su birkita ba. Kuma ka lura sosai sa’ad da kake ba da littattafai. Idan mutanen ba su da marmari sosai, za ka iya ba su warƙa maimakon mujallu.
4. Me ya sa hidima ta kan titi take ba da amfani kuma take da daɗi?
4 Hidima ta kan titi tana ba mu zarafin shuka iri na gaskiya mai yawa a ƙanƙanin lokaci. (M. Wa. 11:6) Wasu mutanen da muka tarar da su suna iya zama waɗanda ba ma ganinsu sa’ad da muke hidimar gida zuwa gida. Zai dace ka yi shiri don saka hannu a hidima ta kan titi kuma ka more hidimar fage mai daɗi da kuma mai amfani.