Za Ku Iya Yin Wa’azi da Yamma?
1. Mene ne wani littafi ya ce game da wa’azi gida-gida da Bulus ya yi?
1 Bisa ga littafin nan Daily Life in Bible Times, manzo Bulus ya yi wa’azi daga ƙarfe 4 na rana har dare. Ba mu san ko a wannan lokacin ne Bulus ya saba yin wa’azi ba, amma abin da muka sani shi ne, shi mai “yin abu duka sabili da bishara,” ne. (1 Kor. 9:19-23) Wataƙila, hakan ya haɗa da yin shiri don fita wa’azi gida-gida a lokacin da zai sami mutane a gida.
2. Me ya sa yin wa’azi da yamma yake da amfani?
2 Masu shela a wurare da yawa sun saba fita wa’azi da safe a cikin mako. Shin, a yankinku, ana samun mutane a gida ne sa’ad da aka fita wa’azi da safe? Wani majagaba ya ce game da yankinsu: “Ba a cika samun mutane a gida da safe sai da yamma.” Fita wa’azi da yamma zai ba mu zarafi sosai na yi wa maza wa’azin bishara. A lokacin, hankalin mutane na kwance kuma za su so su tattauna da mu. Dattawa su fara shirya taron fita wa’azi da yamma idan hakan zai taimaka.
3. Ta yaya za mu nuna sanin yakamata sa’ad da muka fita wa’azi da yamma?
3 Ku Nuna Sanin Yakamata: Zai dace ku nuna sanin yakamata sa’ad da kuke wa’azi da yamma. Idan kuka ziyarci mutum a lokacin da yana wasu hidimomi, alal misali, sa’ad da yake cin abinci, zai dace ku dawo bayan ya gama cin abincin. Ku nuna hikima ta yin tafiya bibiyu kuma kada ku yi nesa da sauran waɗanda kuke wa’azi tare. Kada ku ziyarci mutane da dare sosai sa’ad suke shirin kwanciya. (2 Kor. 6:3) Idan zai kasance da haɗari ku yi wa’azi a wani unguwa da dare, zai dace ku yi wa’azi a wurin da yamma.—Mis. 22:3.
4. Wane albarka ne za mu samu idan muka fita wa’azi da yamma?
4 Albarka da Za Mu Samu: Muna samun albarka sa’ad da muka sami mutane a gida kuma muka yi musu wa’azi. Idan muka yi amfani da duka zarafin da muka samu don yin wa’azi, hakan zai ba mu dama sosai na taimaka wa mutane su “tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:3, 4) Shin, za ka iya tsara al’amuranka don ka riƙa fita wa’azi da yamma?