Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 1/11 pp. 3-6
  • Taimako ga Iyalai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taimako ga Iyalai
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Sa Ibada ta Iyalinku ta Yi Armashi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • “Ku Yi Shiri” A Matsayin Iyalan Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Mece Ce Bauta ta Iyali?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Bauta Ta Iyali Tana Da Muhimmanci Don Tsira!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 1/11 pp. 3-6

Taimako ga Iyalai

1. Ta yaya assabaci na mako-mako ya amfane iyalan Isra’ilawa?

1 Kiyaye Assabaci tanadi ne na ƙauna daga wurin Jehobah da zai amfani iyalai. Isra’ilawa suna hutawa daga ayyukansu na kullum kuma suna da lokacin yin bimbini a kan alherin Jehobah da kuma dangantakarsu da shi. Iyaye za su iya amfani da wannan zarafin don su koya wa yaransu Dokar. (K. Sha 6:6, 7) Assabaci ya ba da lokaci kowane mako don mutanen Jehobah su mai da hankali ga ruhaniyarsu.

2. Mene ne Assabaci ya koya mana game da Jehobah?

2 Hakika, yanzu Jehobah ba ya bukatar iyalai su kiyaye Assabaci. Amma, wannan dokar ta koya mana wani abu game da Allahnmu. A ko da yaushe yana son abin da zai amfani mutanensa a ruhaniya. (Isha. 48:17, 18) A yau, hanya ɗaya da Jehobah yake nuna cewa yana son abin da zai amfani mutanensa ita ce ta wurin Bauta ta Iyali da yamma.

3. Mene ne manufar Bauta ta Iyali da yamma?

3 Mene ne Manufar Bauta ta Iyali da Yamma? A watan Janairu ta shekara ta 2009, an soma yin Taron Rukunin Nazari na Ikilisiya a yamman da ake Makarantar Hidima ta Allah da Taron Hidima. Dalili ɗaya da ya sa aka yi wannan gyara shi ne a ba iyalai zarafin ƙarfafa ruhaniyarsu ta wajen keɓe wani yamma a kowane mako don bauta ta iyali. An ƙarfafa kowace iyali ta sa nazari na iyalinsu da yamman a lokacin da ake taron rukuni a dā idan zai yiwu, kuma su yi amfani da wannan lokacin don su tattauna Littafi Mai Tsarki ban da yin hanzari da kuma nazari da aka tsara don ya taimaki iyalin.

4. Dole ne iyali ta tsara tattaunawarsu ta zama na awa ɗaya kawai? Ka ba da misali.

4 Domin mu halarci Taron Rukunin Nazari na Ikilisiya a dā, mun bukaci lokaci don mu saka tufafi, mu yi tafiya, da sauransu. Ga mutane da yawa, kai da kawowa don halartan wannan taro na awa guda yana ɗaukan fiye da ainihin awa ɗaya na taron. Saboda wannan gyaran da aka yi a tsarinmu na taro, muna da wannan yamman don mu bauta wa Jehobah a matsayin iyali. Domin wannan, ba ma bukatar mu tsara Bautarmu ta Iyali da yamma ya zama awa ɗaya kawai. Maimakon haka, ya kamata mu yi tunani game da bukatu da kasawa na iyalinmu kuma mu tsai da yawan lokaci yadda ya dace da za mu yi don mu cim ma manufa na Bautarmu ta Iyali.

5. Dole ne a yi amfani da dukan lokaci don tattaunawa tare? Ka ba da bayani.

5 Dole ne a Yi Amfani da Dukan Lokaci don Tattaunawa na Rukuni? Sa’ad da ma’aurata da iyalai masu yara suka tattauna batutuwa na Nassi tare, suna ƙarfafa juna. (Rom. 1:12) Iyalin tana kusantar juna sosai. Saboda haka, tattaunawa na Nassi ya kamata ya zama sashe mafi muhimmanci na Bauta ta Iyali da yamma. Amma, kowanne mutum da yake cikin iyali zai iya ba da lokaci sosai a yin nazari na kansa. Alal misali, bayan tattaunawa na rukuni, iyalin suna iya kasancewa tare yayin da kowannensu zai ci gaba da yin nazarinsa dabam, wataƙila ya kammala shiri don taro ko kuma karanta mujallu. Wasu iyalai ba sa kunna talabijin a wannan yamman.

6. Yaya za a iya gudanar da tattaunawar?

6 Yaya Za a Gudanar da Tattaunawar? Bai kamata ya zama tambayoyi ana ba da amsoshi a kowane lokaci ba. Domin a sa Bauta ta Iyali ta yi daɗi, iyalai da yawa suna bin tsari da ya yi kama da taron da muke yi a tsakiyar mako. Suna raba tattaunawarsu zuwa ɓangarori dabam dabam kuma su yi shi a hanyoyi dabam dabam. Alal misali, suna iya karanta Littafi Mai Tsarki tare, su shirya wani sashe na taron, kuma su yi gwaji don hidima. Shafi na 6 ya ba da wasu shawarwari.

7. Wane yanayi ya kamata iyaye su yi ƙoƙari a kasance da shi?

7 Wane Yanayi Ne Ya Kamata Iyaye Su Yi Ƙoƙari Su Sa a Kasance da Don Nazari? Iyalinku za su fi koyo a yanayi da ake nuna ƙauna kuma kowa ya saki jiki. A wani lokaci kuna iya zama a waje idan yanayin yana da kyau. Ku ɗan huta sa’ad da ake bukata hakan. Wasu iyalai suna shaƙatawa bayan nazarin. Ko da yake iyaye za su guji yin amfani da Bauta ta Iyali da yamma don su tsauta wa yaransu ko kuma yi musu horo, za su iya keɓe wasu cikin lokacin don yin magana a kan wani hali ko matsala da suka lura da shi. Amma, zai fi kyau a tattauna wasu batutuwa masu wuya da yaron a wani lokaci cikin makon don kada ya ji kunya a gaban ’yan’uwansa. Bai kamata lokacin Bauta ta Iyali da yamma ya zama lokacin cin rai ko na baƙin ciki ba amma ya kamata ya nuna cewa muna bauta wa Allah mai farin ciki.—1 Tim. 1:11.

8, 9. Wane shiri ne ya kamata shugaban iyalai su yi?

8 Yaya Shugaban Iyali Zai Yi Shiri? Iyalin za ta fi amfana idan shugaban iyalin ya shirya kowace Bauta ta Iyali da yamma tun da wuri ta wajen tsai da shawara a kan abin da ya kamata a tattauna da kuma yadda zai fi kyau a tattauna shi. (Mis. 21:5) Yana da kyau miji ya tuntuɓi matarsa game da wannan. (Mis. 15:22) Shugaban iyalai, yana da kyau a wani lokaci ku nemi shawarwari daga wajen yaranku. Idan kuka yi hakan, za ku san abin da suke so da kuma damuwarsu.

9 Shugaban iyali ba zai ɗau lokaci da yawa yana yin shiri a yawancin makonnin ba. Wataƙila, iyalin za su ji daɗin yin wasu fannoni a kai a kai kowane mako, kuma shugaban iyalin ba zai bukaci ya yi sabon tsari gabaki ɗaya a kowane lokaci ba. Yana iya ganin cewa ya fi kyau ya yi shiri bayan an kammala kowane nazari sa’ad da yake tunanin bukatu na ruhaniya na iyalinsa. Wasu shugaban iyalai suna rubuta ɗan ajanda kuma su manna ta inda iyalin za su iya ganinta, kamar a jikin firiji. Hakan yana sa su riƙa sauraronsa da farin ciki kuma ya ba iyalin lokacin shiri idan suna bukatar yin hakan.

10. Ta yaya waɗanda suke zama su kaɗai za su iya yin amfani da lokacinsu na Bauta ta Iyali da yamma?

10 Idan Ni Kaɗai Ne Kuma Fa? Waɗanda suke zama su kaɗai suna iya yin amfani da lokacinsu na Bauta ta Iyali da yamma don nazari na kansu. Tsarin nazari na kai ya kamata ya haɗa da karatun Littafi Mai Tsarki, shiri don tarurruka, da karatun Hasumiyar Tsaro da Awake! Wasu masu shela suna haɗawa da yin bincike na kansu. A wani lokaci, suna iya gayyatar wani mai shela ko kuma wata iyali su bi su don tattaunawa na Nassi mai ban ƙarfafa.

11, 12. Waɗanne amfani ake samu don yin Bauta ta Iyali da yamma a kai a kai?

11 Wane Amfani Ne Ake Samu Don Yin Bauta ta Iyali da Yamma a Kai a Kai? Waɗanda suke yin bauta ta gaskiya da dukan zuciyarsu suna kusantar Jehobah. Ƙari ga hakan, iyalai waɗanda suke bauta tare suna ƙarfafa gaminsu na iyali. Wasu ma’aurata sun rubuta game da albarka da suka more: “A matsayin ma’aurata majagaba da ba su da yara, muna ɗokin lokacin da muke Bauta ta Iyali da yamma. Muna ji kamar mun jawo kusa da juna da kuma Ubanmu na samaniya. Yanzu sa’ad da muka tashi daga barci a ranar da muke nazari tare, muna gaya wa juna: ‘Ka san abin da za a yi da yamman nan? Muna da Bauta ta Iyali da yamma!’”

12 Tsarin yin bauta ta iyali da yamma yana taimakon iyalai da suka taƙure ainun. Wata uwa gwauruwa da take renon yara maza biyu kuma tana hidimar majagaba na kullum ta rubuta: “A dā, da kyar muke nazari na iyali. Ba ma yin nazarin a kai a kai domin ina yawan gajiya. Ban san yadda zan yi kome ba. Saboda haka, na rubuta don na gode muku sosai don Bauta ta Iyali da yamma. Mun yi nasara a yin nazari na iyali a kai a kai kuma muna samun amfani.”

13. Mene ne yake nuna yawan yadda iyalinku za ta amfana daga wannan tsari?

13 Kamar Assabaci, Bauta ta Iyali da yamma baiwa ce daga wurin Ubanmu na samaniya da za ta iya taimaka wa iyalai. (Yaƙ. 1:17) Yadda iyalai na Isra’ila suke yin amfani da Assabaci zai nuna yawan yadda suka amfana wajen kyautata dangantakarsu da Jehobah. Hakazalika, yadda muke yin amfani da yamma da aka ba mu don bauta ta iyali yana nuna yadda iyalinmu za ta amfana. (2 Kor. 9:6; Gal. 6:7, 8; Kol. 3:23, 24) Ta wajen yin amfani da wannan shiri da kyau, iyalinku za su faɗa kamar marubucin wannan zabura: “Amma ya yi mani kyau in kusanci Allah: Na maida Ubangiji Yahweh mafakata.”—Zab. 73:28.

[Bayanin da ke shafi na 5]

Bai kamata lokacin Bauta ta Iyali da yamma ya zama lokacin cin rai ko na baƙin ciki ba amma ya kamata ya nuna cewa muna bauta wa Allah mai farin ciki

[Akwati da ke shafi na 6]

KU ADANA

Wasu Shawarwari don Bauta ta Iyali da Yamma

Littafi Mai Tsarki:

• Ku karanta wani wuri a karatun Littafi Mai Tsarki na mako-mako tare. Wani yana iya karanta labarin, wasu kuma su karanta kalamai dabam dabam na waɗanda aka ambata cikin labarin, idan an rubuta wasu labaran Littafi Mai Tsarki hakan.

• Ku sake gwada wani sashe na karatun Littafi Mai Tsarki.

• Ku ba kowane cikin iyalin sashe da zai karanta a surorin Littafi Mai Tsarki tun da wuri kuma ya rubuta tambayoyi ɗaya ko kuma biyu daga cikin labarin. Sai ku bincika tambayoyin kowane mutum tare.

• Kowane mako ku shirya katin da aka rubuta ayar Littafi Mai Tsarki a ciki kuma ku yi ƙoƙari ku haddace shi da kuma bayyana ta. Ku tara katuna da yawa, kuma ku maimaita su kowane mako don kuma ku ga nassosi nawa da za ku iya tunawa.

• Ku saurari karatun Littafi Mai Tsarki na faifai yayin da kuke bi naku Littafi Mai Tsarkin.

Tarurruka:

• Ku shirya wani sashen tarurruka tare.

• Ku rera waƙoƙin Mulki da za a yi amfani da su a mako na gaba.

• Idan wani yana da jawabi a Makarantar Hidima ta Allah ko kuma gwaji a Taron Hidima, ku tattauna yadda za a gabatar da shi, ko kuma a maimaita shi a gaban iyalin.

Bukatu na Iyalin:

• Ku tattauna wani darasi daga littattafan nan Questions Young People Ask Answers That Work ko kuma Ka Koya Daga Wurin Babban Malami.

• Ku gwada yadda za a bi da wani yanayi da wataƙila zai taso a makaranta.

• Ku yi gwaji inda iyaye da yara za su canja matsayi. Yaran za su yi bincike a kan wani batu kuma su tattauna da iyayensu.

Hidima:

• Ku yi gwaji don ku shirya gabatarwa don ƙarshen mako.

• Ku tattauna maƙasudai masu yiwuwa da iyalin za ta iya kafa don su sa hannu sosai a hidima a lokacin Tuna Mutuwar Yesu ko kuma lokacin hutu.

• Ka ba kowane da ke cikin iyali ’yan mintoci don ya yi bincike a kan yadda zai amsa tambayoyin da za a iya yi a hidima, sai kuma ku yi gwaji.

Ƙarin Shawarwari:

• Ku karanta wani talifi daga sababbin mujallu tare.

• Ku sa wani cikin iyalin ya karanta tun da wuri wani talifi da ya ji daɗinsa daga sababbin mujallu, kuma ya ba da bayani a kai.

• A jifa-jifa ku gayyaci wani mai shela ko kuma ma’aurata su yi Bauta ta Iyali da yamma tare da ku kuma wataƙila ku gana da su.

• Ku kalli kuma ku tattauna ɗaya cikin bidiyonmu.

• Ku tattauna talifofin “Young People Ask” tare ko kuma “For Family Review” daga Awake!

• Ku tattauna talifofin “Ku Koyar da Yaranku” tare ko kuma “Don Matasa” daga Hasumiyar Tsaro.

• Ku karanta kuma ku tattauna wani wuri daga Yearbook na shekarar ko kuma wani sabon littafi da muka samu daga taron gunduma na kwanan baya.

• Bayan kun halarci taron gunduma ko kuma babban taro, ku maimaita darussan.

• Ka lura da halittun Jehobah, kuma a matsayin iyali, ku tattauna abin da suka koya mana game da Jehobah.

• Ku yi wani bincike tare, kamar wani misali, da taswira.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba