Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • jl darasi na 10
  • Mece Ce Bauta ta Iyali?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mece Ce Bauta ta Iyali?
  • Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Makamantan Littattafai
  • Taimako ga Iyalai
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Mene ne Zai Sa Iyaye da Yara Farin Ciki?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ku Bauta wa Jehobah a Matsayin Iyali
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Ku Sa Ibada ta Iyalinku ta Yi Armashi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
jl darasi na 10

DARASI NA 10

Mece Ce Bauta ta Iyali?

Wata iyali tana jin daɗin bauta ta iyalinta

Koriya ta Kudu

Wasu ma’aurata suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki

Brazil

Wani Mashaidi yana yin nazarin Littafi Mai Tsarki

Ostareliya

Wata iyali tana tattauna wani batu a cikin Littafi Mai Tsarki

Gini

Tun a zamanin dā, Jehobah ya bukaci kowace iyali ta keɓe lokaci domin ta ƙarfafa dangantakarta da Shi kuma iyalin ta ƙarfafa ƙaunar da suke yi wa juna. (Kubawar Shari’a 6:6, 7) Shi ya sa Shaidun Jehobah suke keɓe lokaci a kowane mako don kowace iyali ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma ta tattauna batutuwan da suka shafi dangantakarta da Allah, hankali kwance. Ko da kana zaune ne kai kaɗai, kana iya yin amfani da wannan damar don ka ƙarfafa dangantakarka da Allah ta wajen yin nazarin batutuwan da kake so daga Littafi Mai Tsarki.

Lokaci ne na ƙara kusantar Jehobah. “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” (Yaƙub 4:8) Muna ƙara sanin Jehobah sa’ad da muka koyi halinsa da kuma ayyukansa daga Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Hanya mai sauƙi ta fara bauta ta iyali a lokacin da kuka keɓe a kowane mako ita ce, ku yi amfani da wasu daga cikin wannan lokacin ku karanta Littafi Mai Tsarki tare, kuna iya bin tsarin taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu na kowane mako. Kuna iya sa kowa a iyalinku ya karanta wani sashen Littafi Mai Tsarki da za a karanta a makon, bayan haka, sai ku tattauna abubuwan da kuka koya daga Nassin a matsayin iyali.

Lokaci ne da ke sa iyali su ƙara kusantar juna. Mazaje da matansu, da kuma iyaye da ’ya’yansu suna ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin su sa’ad da suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Ya kamata hakan ya zama abin da kowa a cikin iyalin zai riƙa sa rai a kowane mako. Iyaye za su iya zaɓan batutuwa masu amfani da za su tattauna daga wasu talifofin Hasumiyar Tsaro da sauran littattafai ko kuma daga dandalin jw.org daidai da shekarun yaransu. Kuna iya tattauna matsalar da yaranku suke fuskanta a makaranta da kuma yadda za su warware su. Ban da haka ma, zai yi kyau ku riƙa duba tashan da muke yaɗa shirye-shiryenmu a JW (tv.jw.org) kuma ku tattauna wasu darussa tare. Kuna iya yin waƙoƙin da za a rera a taro a makon kuma kuna iya jin daɗin ci-da-sha bayan bauta ta iyali.

Wannan lokaci na musamman da kuka keɓe a kowane mako don ku bauta wa Jehobah tare zai taimaka wa kowa a iyalin ya riƙa jin daɗin karanta Kalmar Allah, kuma Jehobah zai albarkaci ƙoƙarin da kuke yi.—Zabura 1:1-3.

  • Me ya sa muke keɓe lokaci don bauta ta iyali?

  • Ta yaya iyaye za su sa kowa a cikin iyali ya ji daɗin bauta ta iyali?

KA ƘARA BINCIKE

Kana iya tambayar wasu a cikin ikilisiya abubuwan da suke tattaunawa a bautarsu ta iyali. Ƙari ga haka, za ka iya bincika ka ga irin littattafan da muke da su a Majami’ar Mulki don ka yi amfani da su wajen koyawa yaranka game da Jehobah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba