Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 3/15 pp. 17-19
  • Ku Sa Ibada ta Iyalinku ta Yi Armashi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Sa Ibada ta Iyalinku ta Yi Armashi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KU TATTAUNA BATUTUWA DABAM-DABAM BISA GA BUKATUNKU
  • YIN SHIRI YANA DA MUHIMMANCI
  • KU RIƘA YIN IBADAR A KAI A KAI
  • Taimako ga Iyalai
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ku Bauta wa Jehobah a Matsayin Iyali
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • “Ku Yi Shiri” A Matsayin Iyalan Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ku Taimaki Iyalinku Su Bauta wa Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 3/15 pp. 17-19

Ku Sa Ibada ta Iyalinku Ta Yi Armashi

Wani mahaifi a ƙasar Brazil ya ce: “Muna jin daɗin Ibadarmu ta Iyali sosai, har wani lokaci mukan manta cewa dare ya yi.” Wani mahaifi kuma a Jafan ya ce ɗansa mai shekara 10 yana jin daɗin Ibada ta Iyali da suke yi sosai har ba ya sanin cewa lokaci ya ƙure. Me ya sa? Mahaifin ya ce: “Domin bautar tana ratsa zuciyarsa sosai kuma hakan na sa shi farin ciki.”

Hakika ba dukan yara ba ne suke jin daɗin Ibada ta Iyali ba. Me ya sa? Wani mahaifi a ƙasar Togo ya ce: “Bai kamata bauta wa Jehobah ta zama abu mai kashe jiki ba.” Idan ta zama haka, wannan alama ce cewa ba a gudanar da ita a hanyar da ta kamata. Iyalai da yawa sun shaida cewa Ibada ta Iyali tana iya zama abin “marmari” kamar yadda annabi Ishaya ya ambata game da ranar Assabaci.—Isha. 58:13, 14.

Wajibi ne Kiristoci magidanta su fahimci cewa suna bukatar su kwantar da hankalin iyalinsu a lokacin Ibada ta Iyali idan suna son iyalin ta ji daɗin ibadar sosai. Ralf, wani mahaifi mai ’ya’ya mata uku da namiji ɗaya ya ce suna ba wa kowannensu dama ya furta ra’ayinsa cikin kwanciyar hankali a lokacin da suke Ibada ta Iyali. A gaskiya, ba zai kasance da sauƙi a tattara hankalin kowa a cikin iyalin sa’ad da ake Ibada ta Iyali ba. Wata mahaifiya ta ce: “A wasu lokatai, ba na iya sa Ibadarmu ta Iyali ta zama da armashi kamar yadda nake so.” Me za ka yi don ka iya shawo kan wannan ƙalubalen?

KU TATTAUNA BATUTUWA DABAM-DABAM BISA GA BUKATUNKU

Wani mahaifi mai ’ya’ya biyu a ƙasar Jamus ya ce: “Wajibi ne mu kasance a shirye mu canja batun da za mu tattauna bisa ga yanayinmu.” Wata mahaifiyar ’ya’ya biyu mai suna Natalia kuma ta ce: “Tattauna batutuwa dabam-dabam yana da muhimmanci sosai ga iyalinmu.” Yawancin iyalai suna raba ibadarsu ta iyali zuwa sassa dabam-dabam. “Hakan yana sa kowa a cikin iyalin ya sami aikin yi, kuma ibadar ta zama mai ƙayatarwa,” in ji Cleiton, mahaifin matasa biyu a Brazil. Idan iyaye suka raba lokacin ibadarsu ta iyali zuwa sassa dabam-dabam, za su sami damar mai da hankali ga bukatun dukan yaransu. Iyaye za su iya mai da hankali ga bukatun kowa a iyalin, su zaɓi batun da zai yi daidai da bukatun iyalin kuma su gudanar da ibadar a salon da suke so.

Mene ne wasu iyalai suke yi a ibadarsu ta iyali? Wasu suna somawa da rera waƙar yabo ga Jehobah. Wani mahaifi a ƙasar Meziko mai suna Juan ya ce: “Hakan yana shirya zukatanmu ga batun da za mu tattauna.” Iyalinsa sukan zaɓi waƙar da ta dace da abin da za su tattauna a ranar.

Wasu iyalai kuma suna karanta Littafi Mai Tsarki tare. Ƙari ga hakan, kowannenmu a cikin iyalin yana ɗaukan matsayin mutanen da ake ba da labarinsu a cikin Littafi Mai Tsarki. Wani mahaifi a ƙasar Jafan ya ce bai “saba da irin wannan karatun ba” amma yaransa biyu maza suna jin daɗi domin iyayensu suna ibada tare da su. Wasu iyalai sukan yi wasan kwaikwayo na Littafi Mai Tsarki. Wani mahaifi mai ’ya’ya biyu a Afirka ta Kudu mai suna Roger ya ce: “Yara sukan ga wani abin marmari a cikin Littafi Mai Tsarki waɗanda iyaye ba za su iya gani ba.”

Wata hanya ta yin ibada ta iyali ita ce yin aiki tare, kamar su ƙera Jirgin Nuhu ko haikalin Sulemanu. Irin waɗannan aikin na sa a yi bincike masu daɗi. Alal misali a Asiya, wata ’yar shekara biyar da iyayenta da kuma kakarta sun gwada wannan. Sun kirkiro wani wasa game da tafiye-tafiyen da manzo Bulus ya yi yana wa’azi a ƙasashen waje. Wasu iyalai sun kirkiro wasa game da labarin da ke littafin Fitowa. Wani ɗan ƙasar Togo mai shekara 19 mai suna Donald ya ce: “Kirkiro abubuwa dabam-dabam a lokacin ibadarmu ta iyali ta sa muna jin daɗin ibadar sosai.” Shin za ka iya yin tunanin wani abu da zai sa ibada ta iyalinku ta yi armashi?

YIN SHIRI YANA DA MUHIMMANCI

Ko da yake yin ibada ta iyali a ɓangarori dabam-dabam tana da daɗi, amma yin shiri kafin wannan ibadar tana da muhimmanci sosai. A wasu lokuta, yara suna gajiya, saboda haka, ya kamata magidanta su zaɓi littafin da ya dace don ibadar kuma su yi shiri sosai. Wani magidanta ya ce: “Idan na yi shiri sosai, kowa yana amfana daga ibadar.” Wani magidanta kuma a ƙasar Jamus ya ce yana gaya wa iyalinsa abin da za su tattauna a wata na gaba tun da wuri. Wata iyali mai yara shida a ƙasar Benin suna kallon dibidi da ƙungiyar Jehobah ta wallafa a lokacin ibada ta iyalinsu a wasu lokuta. Ta yaya suke yin shiri? Tun da wuri, baban yana ba su tambayoyin da za su amsa bayan sun gama kallon bidiyon. Babu shakka, yin shiri tana sa kowa ya amfana daga ibada ta iyali.

Idan iyalin sun san abin da za su tattauna tun da wuri, hakan zai ba su zarafin yin hira a kan batun kafin ranar ibadar. Yin hakan zai sa su ƙosa ranar ibadar ta iso da wuri-wuri kuma idan kowa yana da aikin da zai yi a lokacin ibadar, zai ji cewa ba a bar shi a baya ba.

KU RIƘA YIN IBADAR A KAI A KAI

Yana yi wa iyalai da yawa wuya su yi ibadarsu a kai a kai. Me ya sa?

Magidanta da yawa suna daɗewa sosai a wurin aiki don su yi wa iyalinsu tanadi. Alal misali, wani magidanci a ƙasar Meziko yana barin gida da ƙarfe shida na safiya kuma ba ya dawowa sai ƙarfe takwas na dare. Bugu da ƙari, wani abu zai iya tasowa da zai sa a yi gyara ga lokacin da suke yin Ibada ta Iyalinsu saboda ziyarar mai kula da da’ira ko taron gunduma.

Ko da mene ne ya faru, ya kamata mu riƙa yin ibadarmu ta iyali a kai a kai. Loïs ’yar shekara 11 daga ƙasar Togo ta bayyana yadda suke amfana daga yin ibadar a kai a kai. “Ko da muna soma ibadarmu a makare a wasu lokuta saboda wani yanayin da ya taso, amma duk da haka, muna yin ta a ka a kai.” Saboda haka, yana da kyau ku riƙa yin ibadar a farkon mako. Me ya sa? Domin wata larura za ta iya faruwa da zai sa a tura ranar ibadar gaba cikin makon.

Me ya sa ake kiran wannan tattaunawar “ibada ta iyali?” Domin wani fanni ne na bautarmu ga Jehobah. Dukanmu a cikin iyali za mu iya ba da hadayu na “bajimai,” wato mu yabi Jehobah. (Hos. 14:2) Bari kowa a cikin iyali ya ji daɗin ibada ta iyalinsu, domin “farin ciki na Ubangiji shi ne ƙarfin ku.”—Neh. 8:9, 10.

YA KAMATA IBADA TA IYALINKU TA ZAMA:

  • Mai Daɗi

  • Mai Sauƙi

  • Mai Fasaloli Dabam-dabam

  • Wadda Aka shirya

  • A Kai a Kai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba