“Ku Yi Shiri” A Matsayin Iyalan Kirista
“Ku yi shiri: gama cikin sa’a da ba ku sa tsammani ba, Ɗan mutum yana zuwa.”—LUK 12:40.
1, 2. Me ya sa za mu riƙa tunawa da gargaɗi na Yesu na “ku yi shiri”?
“SA’ANDA Ɗan mutum za ya zo cikin darajassa” kuma ya rarraba mutane “da juna,” mene ne zai faru da kai da iyalinka? (Mat. 25:31, 32) Tun da yake hakan zai faru ne a lokacin da ba mu zata ba, yana da muhimmanci mu mai da hankali ga wannan faɗakarwa ta Yesu “ku yi shiri”!—Luk 12:40.
2 Talifin da ya gabata ya tattauna yadda kowanne da ke cikin iyali zai iya taimaka ya sa iyalin ta kasance a faɗake a ruhaniya ta wajen ɗaukan hakkinsa ko nata da muhimmanci. Bari mu yi la’akari da wasu hanyoyi da za mu iya kāre ruhaniyar iyalinmu.
Ka Sa Idonka Ya Kasance “Sarai”
3, 4. (a) Ya kamata iyalan Kiristoci su yi hattara da mene ne? (b) Me yake nufi mu sa idonmu ya kasance “sarai”?
3 Don iyalai su kasance da shiri don zuwan Kristi, dole ne su mai da hankali don kada wasu abubuwa da ba su shafi bauta ta gaskiya ba su janye hankalinsu. Suna bukatar su kāre kansu daga abubuwa da za su iya janye hankalinsu. Tun da yake son abubuwan mallaka tarko ne da ya kama iyalai da yawa, ka yi la’akari da abin da Yesu ya faɗa game da sa idonmu ya kasance “sarai.” (Karanta Matta 6:22, 23.) Kamar yadda fitila za ta iya haskaka hanyarmu kuma mu yi tafiya ba tare da faɗuwa ba, abin da muka kalla da ‘idanunmu na zuci’ na alama zai iya wayar da mu kuma ya taimaka mana mu bi da kanmu ba tare da yin tuntuɓe ba.—Afis. 1:18.
4 Mene ne yake nufi mu sa idanunmu na zuci su kasance sarai. Sa idonmu ya kasance sarai a alamance yana nufin mu mai da hankali ga nufi ɗaya. Ya kamata mu mai da hankali ga batutuwa na ruhaniya maimakon yin rayuwa da ke mai da hankali ga abubuwan duniya kuma mu riƙa damuwa da yadda za mu kula da bukatun zahiri na iyalinmu. (Mat. 6:33) Wannan yana nufin mu yi wadar zuci ga tanadi na zahiri da aka mana kuma mu sa hidimar Allah farko a rayuwarmu.—Ibran. 13:5.
5. Ta yaya wata matashiya ta nuna cewa ta mai da hankali ga bauta wa Allah?
5 Za a samu sakamako mai kyau idan aka koyar da yara su sa idonsu ya kasance sarai! Ka yi la’akari da misalin wata matashiya a ƙasar Habasha. Ta yi ƙoƙari sosai a aikin makarantarta kuma hakan ya sa sa’ad da ta sauƙe karatun sakandare aka ba ta sukolashif don ƙarin ilimi. Amma, ta ƙi sukolashif da aka ba ta don ta mai da hankali ga bauta wa Jehobah. Ba da daɗewa ba, ta samu aikin da za a biya ta daloli 4,200 a wata, kuɗin yana da yawa sosai idan aka gwada da kuɗin da ake biyan ma’aikata a ƙasarsu. Amma matashiyar ta mai da hankali ga hidimar majagaba. Ba ta bukatar ta tuntuɓi iyayenta don ta ƙi aikin. Yaya iyayenta suka ji sa’ad da suka samu labarin abin da ’yarsu ta yi? Sun yi farin ciki sosai da ita kuma suka gaya mata cewa suna alfahari da ita!
6, 7. Ya kamata mu “lura” da wane haɗari?
6 Yesu yana ba da kashedi ne game da haɗama a kalamansa da ke rubuce a Matta 6:22, 23. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalaman nan ‘lafiyayyen ido’ da ‘Ido mai lahani.’ ‘Ido mai lahani’ yana ƙyashi ko haɗama. (Mat. 6:23) Yaya Jehobah yake ji game da ƙyashi ko kuma haɗama? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Fasikanci, da dukan ƙazanta, ko sha’awa [ko “ƙyashi”], kada a ko ambata a cikinku.”—Afis. 5:3.
7 Ko da yake zai iya kasance da sauƙi mu gane cewa wasu suna da ƙyashi, amma ba shi da sauƙi mu gane cewa mu masu ƙyashi ne. Saboda haka, yana da kyau mu yi biyayya da gargaɗin Yesu: “Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan ƙyashi.” (Luk 12:15) Don mu yi hakan, muna bukatar mu bincika kanmu don mu ga abin da yake cikin zuciyarmu. Ya kamata iyalan Kirista su yi tunani sosai game da lokaci da kuɗi da suke kashewa a kan nishaɗi da liyafa da kuma tara dukiya.
8. Idan ya zo ga yin sayayya, ta yaya za mu “yi lura”?
8 Kafin ka yi sayayya, kana bukatar yin wani abu, ba kawai yin tunani ko kana da kuɗin saya ko babu. Ka yi la’akari da abubuwa kamar waɗannan: ‘Zan samu lokaci da zan yi amfani da kayan a kai a kai kuma na kula da shi? Har tsawon wane lokaci ne zai ɗauka kafin na koya yin amfani da shi da kyau?’ Matasa, kada ku gaskata da dukan tallace-tallace na duniya game da kayayyaki kuma da haka ku riƙa bukatar tufafi ko kuma wasu kayayyaki masu tsada. Ku kame kanku. Dukan waɗanda suke cikin iyali za su yi tunanin ko sayan wani kaya zai taimaka wa iyalinsu su kasance a shirye don zuwan Ɗan mutum. Su kasance da bangaskiya ga alkawarin da Jehobah ya yi: “Daɗai ba ni tauye maka ba, daɗai kuwa ba ni yashe ka ba.”—Ibran. 13:5.
Ku Biɗi Maƙasudai na Ruhaniya
9. Yaya biɗan maƙasudai na ruhaniya zai taimaka wa iyali?
9 Wata hanya da waɗanda suke cikin iyali suke ƙarfafa bangaskiyarsu kuma su kāre ruhaniyar dukan iyalin ita ce su kafa maƙasudai na ruhaniya kuma su biɗe su. Yin hakan zai taimaka wa iyalai su san yadda suke samun ci gaba a hidimarsu ga Jehobah kuma su san ayyuka da ya kamata su fi muhimmanci a rayuwarsu.—Karanta Filibiyawa 1:10.
10, 11. A matsayin iyali, waɗanne maƙasudai na ruhaniya ne kuke biɗa, kuma waɗanne maƙasudai za ku so ku kafa a nan gaba?
10 Kusan kowane mutum da ke cikin iyali zai samu sakamako mai kyau idan ya kafa maƙasudai da za su yiwu. Alal misali, maƙasudin tattauna nassosi yini a kowace rana. Shugaban iyalin zai san yawan ruhaniyar waɗanda suke cikin iyalin ta wurin kalamansu. Maƙasudin karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai a matsayin iyali zai ba yaran zarafi mafi kyau su kyautata karatunsu da kuma fahiminsu game da saƙon Littafi Mai Tsarki. (Zab. 1:1, 2) Kuma ya kamata mu kafa maƙasudi na kyautata addu’o’inmu. Koyan nuna fannoni na ’yar ruhu sosai zai iya zama maƙasudi mafi kyau da mutum zai biɗa. (Gal. 5:22, 23) Neman hanyoyi na nuna juyayi ga waɗanda muka haɗu da su a hidima yana da kyau. Ƙoƙarta yin hakan a matsayin iyali zai taimaka wa yaran su koya yin juyayi, kuma hakan zai sa su yanki sha’awar yin hidimar majagaba na kullum ko kuma zama masu wa’azi a ƙasashen waje.
11 Ya dace kai da iyalinka ku bincika wasu maƙasudai da za ku iya biɗa. Shin iyalinka za su iya kafa maƙasudi na ƙara yawan lokaci da kuke yi a hidima? Shin za ka yi ƙoƙari ka sha kan jin tsoro game da yin wa’azi da tarho, a kan titi, ko kuma wuraren sana’o’i? Yin wa’azi inda ake bukatar masu shelar Mulki kuma fa? Shin wani a cikin iyalin zai iya koyon wani yare domin ya samu yi wa waɗanda suka fito daga wasu ƙasashe wa’azi?
12. Mene ne shugaban iyalai za su iya yi don su taimaka wa iyalansu su samu ci gaba a ruhaniya?
12 A matsayin shugaban iyali, ka bincika wuraren da iyalinka za su iya samun ci gaba a ruhaniya. Sai ka kafa takamammun maƙasudai da za su taimaka maka ka cim ma su. Ya kamata maƙasudai da kuka kafa a matsayin iyali su zama waɗanda za su yiwu da za su yi daidai da yanayinku da kuma iyawarku. (Mis. 13:12) Hakika, yin ƙoƙari a cim ma maƙasudi mai kyau yana ɗaukan lokaci. Saboda haka, ka yi amfani da lokacin da kake kallon talabijin don ka yi ayyuka na ruhaniya. (Afis. 5:15, 16) Ka yi ƙoƙari ka cim ma maƙasudai da ka kafa don iyalinka. (Gal. 6:9) Iyalin da ke biɗe-biɗen maƙasudai na ruhaniya za su sa ci gabansu ya “bayanu ga kowa.”—1 Tim. 4:15.
Ku Riƙa Yin Bauta ta Iyali da Yamma
13. Wane canji ne aka yi a tsarin tarurruka na mako-mako na ikilisiya, kuma waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi bimbini a kan su?
13 Abin da zai fi taimaka wa iyalai “su yi shiri” don zuwan Ɗan mutum shi ne canji na musamman da aka yi ga tsarin taro na mako-mako da aka soma a ranar 1 ga Janairu, 2009. An kawar da taron Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya da ake yi a wata rana dabam ta wajen haɗa wannan taron da Makarantar Hidima ta Allah da kuma Taron Hidima. An yi wannan gyaran don a ba iyalan Kirista zarafin ƙarfafa ruhaniyarsu ta wajen tsara wata yamma a kowane mako don bauta ta iyali. Yanzu da lokacin da aka yi wannan gyara ya ɗan shige, muna iya tambayar kanmu: ‘Ina yin amfani da lokacin da aka keɓe don Bauta ta Iyali da yamma ko kuma yin nazari na kaina? Na yi nasara ne wajen cim ma manufar wannan tsarin?’
14. (a) Mene ne ainihin manufar yin Bauta ta Iyali da yamma ko kuma nazari na kanmu? (b) Me ya sa keɓe wata yamma don nazari yake da muhimmanci?
14 Kusantar Allah ne ainihin manufar yin Bauta ta Iyali da yamma ko kuma nazari na kanmu. (Yaƙ. 4:8) Sa’ad da muka ba da lokaci sosai a nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai kuma muka ƙara sanin Mahaliccin, za mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. Idan muka ci gaba da kusantar Jehobah, za mu ƙara ƙaunarsa da ‘dukan zuciyarmu, da dukan ranmu, da dukan azancinmu, da dukan ƙarfinmu.’ (Mar. 12:30) Babu shakka, muna ɗokin yin biyayya ga Allah kuma mu zama masu yin koyi da shi. (Afis. 5:1) Saboda haka, yin Bauta ta Iyali da yamma yana da muhimmanci don a taimaka wa dukan waɗanda suke cikin iyalinmu su “yi shiri” a ruhaniya yayin da muke jiran “ƙunci mai-girma” da aka annabta. (Mat. 24:21) Yana da muhimmanci don mu tsira.
15. Yaya Bauta ta Iyali da yamma za ta iya shafan yadda waɗanda suke cikin iyali suke ji game da juna?
15 Wani dalili kuma na Bauta ta Iyali shi ne don ya taimaki waɗanda suke cikin iyali su kusaci juna. Kasancewa tare don tattauna batutuwa na ruhaniya a kowane mako yana shafan yadda waɗanda suke cikin iyali suke ji game da juna. Ma’aurata suna kasancewa da haɗin kai sosai sa’ad da suke jin daɗin koyon Littafi Mai Tsarki tare! (Karanta Mai-Wa’azi 4:12.) Iyaye da yara da suke bauta tare za su fi kasancewa da haɗin kai cikin ƙauna “magamin kamalta.”—Kol. 3:14.
16. Ka ba da labarin yadda ’yan’uwa mata uku na ruhaniya suka amfana ta wajen keɓe wata yamma don yin nazarin Littafi Mai Tsarki.
16 Ka yi la’akari da yadda ’yan’uwa mata uku suka amfana daga tsarin keɓe wata yamma don nazarin Littafi Mai Tsarki. Ko da yake ba su danganci juna ba, waɗannan gwauraye tsofaffi suna zama a birni ɗaya kuma su aminai ne na shekaru da yawa. Da yake suna son yin cuɗanya tare sosai kuma su samu amfani na ruhaniya ba yin tarayya kawai ba, sun tsai da shawara su keɓe wata yamma don su haɗu kuma su yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Sun soma yin hakan ta yin amfani da littafin nan “Bearing Thorough Witness” About God’s Kingdom. “Muna jin daɗin lokacin sosai har nazarinmu yana wuce awa guda,” in ji ɗaya cikinsu. “Muna ƙoƙarin yin tunanin yanayin da ’yan’uwanmu na ƙarni na farko suke ciki a zuciyarmu kuma mu tattauna abin da za mu yi idan muna cikin irin wannan yanayin. Kuma mun yi ƙoƙari mu yi amfani da darussa da muka koya daga tattaunawarmu. Hakan ya sa aikinmu na wa’azin Mulki da almajirtarwa ya fi yin daɗi da kuma ba da amfani fiye da dā.” Ban da ilimantar da su a ruhaniya, shirin ya sa waɗannan aminai uku su kusaci juna sosai. Sun ce: “Muna ɗaukan wannan shirin da tamani.”
17. Waɗanne abubuwa ne za su sa Bauta ta Iyali da yamma ta yi nasara?
17 Kai kuma fa? Ta yaya kake amfana ta wajen keɓe wata yamma don bauta ta iyali ko kuma nazari na kai? Idan ana yi a wasu lokatai ne kawai, wannan shirin ba zai cim ma abin da ake so ba. Ya kamata kowane mutum da ke cikin iyali ya kasance a shirye ya yi nazari a lokacin da aka tsara. Bai kamata a ƙyale batutuwa da ba su da muhimmanci su hana nazarin a yamma da aka keɓe ba. Bugu da ƙari, ka zaɓi littafin da za a nazarta da iyalinka za su yi amfani da shi a rayuwarsu na kullum. Mene ne za ka iya yi don ka sa nazarin ya yi daɗi? Ka yi amfani da hanyoyin koyarwa masu kyau, kuma ka sa yanayin ya zama na daraja da lumana.—Yaƙ. 3:18.a
‘Ku Zauna a Faɗake’ Kuma “Ku Yi Shiri”
18, 19. Ta yaya sanin cewa zuwan Ɗan mutum ya kusa ya kamata ya shafe ka da iyalinka?
18 Babu shakka, yanayin duniya da ke taɓarɓarewa a zamaninmu ya nuna cewa tun shekara ta 1914, muguwar duniyar Shaiɗan ta shiga kwanakinta ta ƙarshe. Armageddon ya yi kusa. Ba da daɗewa ba Ɗan mutum zai zo ya zartar da hukuncin Jehobah a kan waɗanda ba sa bauta wa Allah. (Zab. 37:10; Mis. 2:21, 22) Ya kamata sanin hakan ya shafe ka da iyalinka?
19 Kana yin biyayya da shawarar Yesu na ka sa idonka ya kasance “sarai”? Iyalinka suna biɗan maƙasudai na ruhaniya kuwa yayin da mutane na wannan duniya suke neman arziki da suna ko kuma iko? Kana amfana daga tsarin Bauta ta Iyali da yamma ko kuma lokacin nazari na kanka? Shin ya taimaka wa iyalinka su kusaci Jehobah da kuma juna sosai? Kamar yadda aka tattauna a talifin da ya gabata, kana cika hakkinka na Nassi a matsayin maigida, mata, ko kuma yaro da hakan kana taimaka wa dukan iyalinka su “zauna a faɗake”? (1 Tas. 5:6, Littafi Mai Tsarki) Idan haka ne, za ka kasance da “shiri” don zuwan Ɗan mutum.
[Hasiya]
a Don samun shawarwari a kan abin da za a yi nazarinsa da kuma yadda za a sa Bauta ta Iyali da yamma ya kasance da amfani kuma a ji daɗinsa, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2009 shafuffuka na 29-31.
Me Ka Koya?
• Ka bayyana yadda iyalan Kirista za su iya kasancewa da “shiri” ta wurin . . .
sa idonsu ya kasance “sarai.”
kafa da kuma biɗan maƙasudai na ruhaniya.
yin Bauta ta Iyali da yamma.
[Hoton da ke shafi na 13]
Sa idonmu ya kasance “sarai” zai sa mu ƙi abubuwan duniya da ke janye hankali