Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/15 pp. 29-31
  • Bauta Ta Iyali Tana Da Muhimmanci Don Tsira!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bauta Ta Iyali Tana Da Muhimmanci Don Tsira!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Muhimmancin Keɓe Lokaci Don Bauta ta Iyali
  • Ku Riƙa Yi a Kai a Kai
  • Ka sa Ya Zama Mai Amfani
  • Ka sa Ya Yi Daɗi
  • Taimako ga Iyalai
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Abin da Zai Taimaka wa Matasa Su Tuna da Mahaliccinsu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • “Ku Yi Shiri” A Matsayin Iyalan Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/15 pp. 29-31

Bauta Ta Iyali Tana Da Muhimmanci Don Tsira!

KA YI tunanin yadda “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka” za ta kasance da ban tsoro! (R. Yoh. 16:14) Ta wajen yin amfani da fasahar magana, manzo Mikah ya rubuta: “Duwatsu kuma za su narke . . . kwaruruka kuma za su tsagu, kamar kakin zuma a gaban wuta, kamar ruwa da an zubar da shi a magangari mai-zurfi.” (Mi. 1:4) Wane mugun abu ne zai faru da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah? Kalmar Allah ta ce: “Za a ga kisassun Ubangiji tun daga wannan iyakar duniya zuwa wannan iyaka.”—Irm. 25:33.

Domin irin waɗannan gargaɗin, zai yi kyau shugabannin iyalai, waɗanda yawancinsu iyaye gwauraye ne, su tambayi kansu game da yaransu da suka isa yin tunani, ‘Za su tsira a Armagedon kuwa?’ Littafi Mai Tsarki ya ba da tabbaci cewa za su tsira idan suna da dangantaka mai ƙarfi da Jehobah daidai da shekarunsu.—Mat. 24:21.

Muhimmancin Keɓe Lokaci Don Bauta ta Iyali

A matsayin iyaye, ku tabbata cewa kun yi iyakar ƙoƙarinku ku yi renon yaranku ‘cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.’ (Afis. 6:4) Yin nazarin Littafi Mai Tsarki da yaranku yana da muhimmanci sosai. Muna son matasanmu su zama kamar Kiristocin da ke Filibbi, waɗanda Bulus ya yaba musu don yin biyayya ga Jehobah da son rai. Ya rubuta: “Ƙaunatattuna, kamar yadda kun yi biyayya kullum, ba a gabana kaɗai ba, balle fa yanzu da ba ni nan, ku yi aikin cetonku da tsoro da rawan jiki.”—Filib. 2:12.

Yaranka suna bin dokokin Jehobah a lokacin da ba ka nan? Sa’ad da suke makaranta fa? Ta yaya za ka iya taimaka wa yaranka su tabbata cewa dokokin Jehobah suna da amfani domin dokokin su yi musu ja-gora har a lokacin da ba ka tare da su?

Bauta ta iyali za ta iya taimakawa sosai wajen ƙarfafa bangaskiyar yaranka a wannan batun. Saboda haka, bari mu tattauna abubuwa guda uku masu muhimmanci da za su sa ka yi nasara a nazarin Littafi Mai Tsarki da iyalinka.

Ku Riƙa Yi a Kai a Kai

A yare na asali na Littafi Mai Tsarki, furcin da aka fassara “wata rana” a Ayuba 1:6, ya nuna cewa an gayyaci mala’iku ’ya’yan Allah su bayyana a gabansa a wasu lokatai da aka keɓe. Ka yi hakan da yaranka. Ka keɓe rana da lokaci don Bauta ta Iyalinka da yamma, kuma ka manne wa hakan. Ƙari ga haka, ka keɓe wani lokaci dabam saboda aukuwar da ba a zato.

Da shigewar lokaci, kada ka koya halin yin nazarin Littafi Mai Tsarki a duk lokacin da aka ga dama ya shafe ku. Ka tuna, yaranka ne ɗalibanka na Littafi Mai Tsarki da suka fi muhimmanci. Duk da haka, Shaiɗan zai so su faɗa hannunsa. (1 Bit. 5:8) Idan ba ka yin amfani da Bauta ta Iyali da yamma sosai ba amma ka soma yin amfani da wannan lokacin don kallon talabijin ko kuma wasu ayyuka da ba su da muhimmanci, Shaiɗan ya yi nasara ke nan.—Afis. 5:15, 16; 6:12; Filib. 1:10.

Ka sa Ya Zama Mai Amfani

Bai kamata Bauta ta Iyali da yamma ya zama lokacin koyan abubuwa kawai ba. Ka haɗa tattaunawar da abubuwan da za a iya yin amfani da su a rayuwa ta yau da kullum. Ta yaya? A wasu lokatai, ka zaɓi batutuwan da suka shafi abubuwan da yaronka zai fuskanta a kwanaki ko kuma makonni masu zuwa. Alal misali, me zai sa ba za ka haɗa hakan da gwada yadda za a gabatar da hidimar fage ba? Yara suna jin daɗin yin abubuwa da suke yi da kyau. Gwada gabatarwa da kuma yin tunanin hanyoyin da za su bi da mutanen da suke ƙin saurarawa zai taimaka musu su kasance da gaba gaɗi yayin da suke saka hannu a fannoni dabam-dabam na aikin wa’azin Mulki.—2 Tim. 2:15.

Za ka kuma iya gwada abubuwan da za su taimaka wa yaranka su bi da matsi na tsara. Ka riƙa tattauna abubuwan da za su sa yaranka su ga damar mai da martanin da shi ko ita ta ga cewa ya dace. Hakan zai iya haɗa da tambayar yaranka irin ƙalubalen da suke fuskanta, inda suke fuskantarsu, abin da zai faru idan ya yi tasiri a kansu, da kuma abin da zai faru idan suka guji yin hakan. A lokaci-lokaci, ka sa wannan tattaunawar ta kasance sashen Bauta ta Iyali da yamma!

Bauta ta iyali tana ba iyaye zarafin nanata amfanin kafa makasudai na ruhaniya. Game da wannan, warƙar nan Matasa—Me Za Ku Yi da Rayuwarku? tana ɗauke da bayanai masu kyau. Sa’ad da kuke tattauna wannan warƙar, ka taimaka wa yaronka ya san cewa mai da hankali ga bauta wa Jehobah shi ne tafarki mafi kyau da zai bi. Ka taimaka wa yaronka ya yi sha’awar yin hidima ta majagaba, hidima a Bethel, halartan Makarantar Koyar da Bayi Masu Hidima, ko kuma su biɗi wasu fasaloli na hidima ta cikakken lokaci.

Yana da kyau a tuna cewa wasu iyaye da suke son abu mafi kyau ga yaransu suna yin kuskuren mai da hankali ainun ga abin da suke son yaransu su zama har su manta su yaba wa yaran don abin da suke yi yanzu. Hakika, yana da kyau ka ƙarfafa yaranka su kafa makasudai masu kyau kamar hidima a Bethel, da kuma aikin wa’azi a ƙasar waje. Amma, sa’ad da kake yin hakan, ka mai da hankali kada ka ƙuntata wa yaronka da abubuwan da kake son shi ko ita ya ko ta yi kuma ka sa shi ko ita ta yi sanyin gwiwa. (Kol. 3:21) A kowane lokaci, ka riƙa tunawa cewa dole ne ɗanka ko ’yarka ta ko ya yi ƙaunar Jehobah da nasa ko nata dukan zuciya, ba naka ba. (Mat. 22:37) Saboda haka, ka nemi hanyoyin yaba wa ɗanka ko ’yarka don abin da shi ko ita yake yi da kyau, kuma ka guji mai da hankali ga abin da shi ko ita ba ya yi. Ka nuna godiya ga dukan abin da Jehobah ya yi. Kuma ka sa yaronka ya amince da nagartar Jehobah.

Ka sa Ya Yi Daɗi

Sashe na uku mai muhimmanci da zai sa a yi nasara a Bauta ta Iyali da yamma shi ne, ka sa nazarin ya yi daɗi. Ta yaya za ka cim ma hakan? Wataƙila a wani lokaci kuna iya sauraron ɗaya daga cikin wasan kwaikwayo na kaset ko kuma ku kalli ɗaya daga cikin bidiyon da Shaidun Jehobah suka wallafa kuma ku tattauna shi. Ko kuma, kuna iya karanta wani sashe na Littafi Mai Tsarki tare, ka rarraba sashen ga kowanne da ke cikin iyalin ya karanta.

Da akwai talifofin da ke cikin Hasumiyar Tsaro na wa’azi da suka ƙunshi batutuwa masu kyau da iyalai za su iya tattaunawa. Kowace fitowa na Hasumiyar Tsaro yana ɗauke da wannan talifin domin ƙananan yara maza da mata mai jigo “Ku Koyar da Yaranku.”

Saboda haka, labaran rayuwa na mutane masu aminci da ke cikin mujallun mu sun yi tanadin batutuwa masu kyau da za su taimaka wa yaronku ya fahimci cewa yin amfani da rayuwa a bautar Jehobah ita ce tafarki mafi kyau da ya kamata a bi.

Amma dai, ka mai da hankali kada ka mai da nazari na iyali ya zama sashen matsa wa yaro ya amsa jerin tambayoyi. Alal misali, an ba da shawarar cewa iyaye su ƙarfafa yaransu su riƙa rubuta batutuwan da suke so, su rubuta abin da ke zuciyarsu da kuma yadda suke ji game da abin da suka tattauna a matsayin iyali da kuma yadda za su yi amfani da shi a rayuwarsu. Amma, kada ka tilasta wa yaronka ya karanta wa dukanku ku ji abin da shi ko ita ta rubuta a ɗan ƙaramin littafin ta. Domin hakan zai iya hana yaronka ya rubuta ainihin abin da ke zuciyarsa. Ka ɗan sa wa yaronka labule.

Idan kuna yin bautarku na iyali a kai a kai, kuna sa ya kasance mai amfani, kuma kuna sa ya yi daɗi, Jehobah zai albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenku sosai. Wannan lokaci mai muhimmanci ga iyali zai sa waɗanda kake ƙauna su kasance da ruhaniya sosai.

[Akwati da ke shafi na 31]

Ka Haɗa da Sababbin Abubuwa

“Sa’ad da muke bautarmu ta iyali, ni da mijina mun bincika batun da za a tattauna a taron ikilisiya tare da yaranmu mata biyu, kuma mun gaya wa yaranmu mata su zana hoton da ya taƙaita darassin. A wasu lokatai, muna sake gwada wasu abubuwa da suka faru a Littafi Mai Tsarki ko kuma mu gwada gabatarwa na hidimar fage. Muna sa nazarin ya yi daidai da shekarunsu, ya yi daɗi, ya amfane su, kuma ya sa su farin ciki.”—J.M., Amirka.

“Don na taimaka wa yaron ɗalibina na Littafi Mai Tsarki ya fahimci yadda ake amfani da naɗaɗɗen littafi a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, mun buga littafin Ishaya bayan mun cire surorin da ayoyin. Mun haɗa shafofin kuma mun saka abin riƙewa a ƙarshensu. Sai yaron ya yi ƙoƙarin yin abin da Yesu ya yi a majami’ar da ke Nazarat. Labarin da ke Luka 4:16-21 ya ce Yesu ya “buɗe littafi [na Ishaya], ya iske wurin” da yake nema. (Isha. 61:1, 2) Amma, sa’ad da yaron ya yi ƙoƙarin yin hakan, ganin Ishaya sura ta 61 ya yi masa wuya ta wajen yin amfani da wannan dogon naɗaɗɗen littafi da bai da sura da ayoyi. Domin yadda Yesu ya yi amfani da naɗaɗɗen littafin ya burge shi sosai, yaron ya furta: ‘Yesu yana da ban al’ajabi!’”—Y.T., Japan.

[Hotunan da ke shafi na 30]

Yin gwaji zai taimaka wa yaranka su san yadda za su bi da matsi na tsara

[Hotunan da ke shafi na 31]

Ka yi ƙoƙari ka sa Bauta ta Iyali da yamma ta yi daɗi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba