Tsarin Ayyuka na Makon 3 ga Maris
MAKON 3 GA MARIS
Waƙa ta 112 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 3 sakin layi na 19-21 da akwatin da ke shafi na 34 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Farawa 36-39 (minti 10)
Na 1: Farawa 37:1-17 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Yin Magana da Harsuna Dabam-dabam Alamar Amincewar Allah Ce?—td 42D (minti 5)
Na 3: Wasu Sun Fi Mu Matsayi—lr babi na 8 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 117
Minti 10: Ku Ba da Mujallu a Watan Maris. Tattaunawa. Ka sa a yi gwajin da zai nuna yadda za a iya ba da mujallu ta wajen yin amfani da gabatarwa da ke wannan shafin. Sa’an nan ka tattauna kowanne cikin gabatarwar, daga farko har ƙarshe. A ƙarshe, ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda za su so su ba da mujallun tare da takardar gayyata zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu, a ƙarshen mako na huɗu da na biyar na wannan watan.
Minti 10: Bukatun Ikilisiya.
Minti 10: Mene Ne Muka Cim Ma? Tattaunawa. Ka ba masu shela dama su faɗi yadda suka amfana daga bin shawarar da ke talifin nan “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Ta Wajen Rubuta Bayani Game da Wanda Ya So Saƙonmu,” kuma su faɗi labarai masu daɗi da suke da su.
Waƙa ta 95 da Addu’a