Tsarin Ayyuka na Makon 19 ga Janairu
MAKON 19 GA JANAIRU
Waƙa ta 47 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 19 sakin layi na 1-8 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Alƙalawa 1-4 (minti 8)
Na 1: Alƙalawa 3:1-11 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Ta Yaya Za Ka Iya Koya Game da Allah?—igw 4 sakin layi na 1-4 (minti 5)
Na 3: A Wace Hanya Ce Ruhu Yake Komawa Wurin Allah?—M. Wa. 12:7 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata:Ku Yi Hidimar “Ubangiji da Iyakacin Tawali’u.”—Ayyukan Manzanni 20:19.
Waƙa ta 77
Minti 10: Kuna Yin Amfani da Ƙasidar Nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah Kuwa? Ku tattauna tambayoyin da ke gaba: (1) Ta yaya ƙasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah za ta taimaka mana sa’ad da muke karanta littafin (a) Alƙalawa 16:1-3, (b) Luka 6:17, da (c) Romawa 15:19? (2) Ta yaya ƙasidar za ta taimaka mana mu fahimci waɗannan kalmomin (a) “omer” da “ephah” (Fit. 16:32, 36), (b) “talanti” (Mat. 25:15) da (c) “Abib” da “Nisan” (K. Sha. 16:1)? Ka kammala tattaunawar ta wajen ƙarfafa kowa ya yi amfani da wannan kayan aikin.
Minti 10: Yi wa Ubangiji Hidima Yana Bukatar Naciya da Dabara. Tattaunawa daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2014, shafi na 31, sakin layi na 19. Ka ba masu sauraro dama su faɗi darussan da suka koya.
Minti 10: “Ku Ci Gaba da Ƙwarewa a Matsayinku na Masu Shelar Bishara.” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 20 da Addu’a