Tsarin Ayyuka na Makon 14 ga Satumba
MAKON 14 GA SATUMBA
Waƙa ta 50 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 30 sakin layi na 10-18 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Sarakuna 16-18 (minti 8)
No. 1: 2 Sarakuna 17:12-18 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
No. 2: Ta Yaya Za Ka Amfana Sosai Daga Karatun Littafi Mai Tsarki?—igw 32 (minti 5)
No. 3: Ta Yaya Za Mu Sa Idanunmu Su Riƙa Gani “Sarai”?—Mat. 6:22, 23 (minti 5)
Taron Hidima:
JIGON WATA: ‘Ku shaida bishara’ sosai.—A. M. 20:24.
Waƙa ta 23
Minti 10: ‘Ku Shaida Bishara’ Sosai. Jawabin da ke bayyana jigon wata da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 2014, shafi na 3, sakin layi na 4 zuwa shafi na 5.—A. M. 20:24.
Minti 20: “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Wa’azi a Wuraren Kasuwanci.” Tattaunawa. Ka sa a yi gwaji guda biyu. A gwaji na farko, ka sa mai shela ya yi wa’azi a hanyar da ba ta dace ba a wurin kasuwanci. Bayan haka, ka sa a sake yin gwajin, a wannan karon a yi wa’azin a hanyar da ta dace. A ƙarshe, ka ba ’yan’uwa dama su faɗi dalilin da ya sa gwaji na biyu ya fi kyauc.
Waƙa ta 96 da Addu’a