Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
1. Wane littafi ne za mu tattauna a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya daga makon 19 ga Oktoba?
1 Daga makon 19 ga Oktoba, 2015, za mu soma nazarin littafin nan Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Wannan littafin ya tattauna labaran maza da mata guda 14 da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. An rubuta wannan littafin yadda za mu fahimci labaran waɗannan mutanen sosai, don mu ga cewa su mutane ne kamar mu da suka fuskanci ƙalubale yayin da suke bauta wa Jehobah. An kuma rubuta darussan da za mu iya koya a yau daga labaran waɗannan mutanen.—Ibran. 6:12.
2. Ku faɗi wasu abubuwa da ke littafin nan Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu.
2 Abubuwan da Ke Littafin: Littafin yana ɗauke da jerin shekaru da kuma taswira da za su taimaka mana mu san lokaci da kuma wuraren da waɗannan mutanen suka zauna. Ƙari ga haka, kowane babi na ɗauke da akwatin nan “Don Bimbini . . . .” Akwatin zai taimaka mana mu yi bimbini a kan labarin kuma mu yi amfani da darussan da muka koya. Akwai zane-zane da kuma hotuna masu kyau a cikin littafin da za su taimaka mana mu yi bimbini sosai a kan labaran.
3. Me ya kamata mu yi don mu amfana daga nazarin littafin nan?
3 Yadda Za Ka Amfana: A shafi na farko, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta ƙarfafa mu da wasiƙar nan: “Ka yi tunani da kuma bimbini a kansa. Ka ga abubuwan da maza da mata da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki suka gani kuma ka ji ƙarar da suka ji. Ka yi tunani a kan abin da suka yi sa’ad da suke cikin wani yanayi kuma ka yi tunani a kan abin da za ka yi da a ce kai ne.” Yin tunani da bimbini a kansu ba ya nufin yin tunani a kan abin da bai faru da su ba, amma yana nufin yin tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da su da yadda za mu yi koyi da su. Yin hakan na bukatar lokaci da kuma bimbini. (Neh. 8:8) Idan an soma nazarin daga tsakiyar babi, mai gudanar da taron zai soma da bita ta daƙiƙa 30 zuwa 60 na abin da aka tattauna a makon da ya gabata. Za a iya yin tambaya ɗaya ko biyu a ƙarshen nazarin idan babu akwatin nan “Don Bimbini . . .” a darasin da aka tattauna.
4. Wane amfani za mu samu don yin nazarin littafin nan Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu?
4 Muna rayuwa ne a duniyar da kullum ana nema a raunana bangaskiyarmu. Wannan littafin da kuma sauran talifofin da ake wallafawa a cikin Hasumiyar Tsaro kyauta ce daga Jehobah da za ta sa bangaskiyarmu ta yi ƙarfi. (Yaƙ. 1:17) Bari mu nuna godiya sosai don wannan kyautar ta wajen halartan taron Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya a kai a kai da kuma yin kalami yayin da muke nazarin wannan littafin!