Tsarin Ayyuka na Makon 21 ga Satumba
MAKON 21 GA SATUMBA
Waƙa ta 53 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 30 sakin layi na 19-23, da akwatin da ke shafi na 309 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 2 Sarakuna 19-22 (minti 8)
No. 1: 2 Sarakuna 20:12-21 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
No. 2: Abin da Ya Sa Kalmomin Bulus A Romawa 14:7-9 Suna da Ban Ƙarfafa (minti 5)
No. 3: Me Ya Sa Ya Kamata Mu San Sunan Allah Kuma Mu Yi Amfani da Shi?—wp13 1/1 16 sakin layi na 1-4 (minti 5)
Taron Hidima:
JIGON WATA: ‘Ku shaida bishara’ sosai.—A. M. 20:24.
Waƙa ta 97
Minti 10: Mene ne Muka Cim ma a Shekarar Hidima da Ta Shige? Jawabin da mai kula da hidima zai yi. Ka yi bitar abubuwan da ikilisiyar ta cim ma a shekarar hidima da ta shige. Ka jawo hankalin ’yan’uwa ga abubuwa masu kyau da aka cim ma kuma ka yaba musu. Ka ambata fanni ɗaya ko biyu na wa’azi da ya kamata ’yan’uwa a ikilisiyar su ƙara ƙoƙari a kai a wannan shekarar hidima kuma ka faɗa yadda za su yi hakan.
Minti 10: Sakamakon Shaida Bishara Sosai. Tattaunawa da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu 2008, shafi na 19, sakin layi na 13 da shafi na 20, sakin layi na 16 da kuma Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba, 2008, shafi na 20, sakin layi na 14-16. Bayan ka tattauna kowane labari, ka ba ’yan’uwa dama su faɗi darussan da suka koya.
Minti 10: “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu.” Tambayoyi ana ba da amsoshi.
Waƙa ta 81 da Addu’a