Ka Yi Koyi Da Mai Wa’azi Mafi Girma Na Ƙasashen Waje
“Ku zama masu-koyi da ni, kamar yadda ni kuma na Kristi ne.”—1 KOR. 11:1.
1. Me ya sa muke bukatar mu yi koyi da Yesu Kristi?
MANZO Bulus ya yi koyi da Mai wa’azi mafi girma, Yesu Kristi. Bulus ya aririci ’yan’uwansa Kiristoci: “Ku zama masu-koyi da ni, kamar yadda ni kuma na Kristi ne.” (1 Kor. 11:1) Bayan Yesu ya koya wa manzanninsa darassi game da tawali’u ta wajen wanke ƙafafunsu, ya gaya musu: “Na yi muku kwatanci, domin ku kuma ku yi kamar yadda na yi muku.” (Yoh. 13:12-15) Mu Kiristoci na zamani, dole ne mu yi koyi da Yesu Kristi a kalamanmu, a ayyukanmu da kuma halayenmu na yau da kullum.—1 Bit. 2:21.
2. Ko da Hukumar Mulki ba ta naɗa ka ka zama mai wa’azi a ƙasashen waje ba, wane irin hali ne za ka iya nunawa?
2 A talifin da ya gabata, mun koyi cewa mai wa’azi a ƙasashen waje mutumi ne da aka aika ya je ya yi bishara ga wasu. Bulus ya yi wasu tambayoyi masu muhimmanci game da wannan. (Ka karanta Romawa 10:11-15.) Za ka lura cewa manzon ya yi wannan tambayar: “Ƙaƙa za su ji . . . in ba mai-yin wa’azi?” Bayan haka, sai ya yi ƙaulin waɗannan kalaman daga annabcin Ishaya: “Duba! ga ƙafafun mai-kawo bishara, daɗin gani garesu!” (Isha. 52:7) Ko da ba a aika ka yin wa’azi a ƙasashen waje ba, kana iya kasancewa mai yin bishara mai ƙwazo, ta wajen yin koyi da Yesu. A shekarar da ta shige, masu shelar Mulki guda 6,957,852 ne suka yi “aikin mai-bishara” a ƙasashe 236.—2 Tim. 4:5.
“Mun Bar Abu Duka, Mun Bi Ka”
3, 4. Menene Yesu ya bari a sama, kuma menene muke bukatar mu yi don mu zama mabiyansa?
3 Don ya cika aikin da aka ce ya yi a duniya, Yesu “ya wofinta kansa da ya ɗauki surar bawa, yana kasancewa da sifar mutane.” (Filib. 2:7) Duk abin da muka yi ta wajen yin koyi da Kristi bai kai abin da Yesu ya yi sa’ad da zai zo duniya ba. Amma a matsayinmu na mabiyansa, muna iya kasancewa da aminci, ban da mai da hankali ga abubuwan da muka ƙyale a duniyar Shaiɗan.—1 Yoh. 5:19.
4 Akwai lokacin da manzo Bitrus ya gaya wa Yesu: “Ga mu, mun bar abu duka, mun bi ka.” (Mat. 19:27) Bitrus, Andarawus, Yaƙub, da Yohanna sun jefar da tarunsu sa’ad da Yesu ya gayyace su su zama mabiyansa. Sun ƙyale sana’ar kamun kifi da suke yi kuma suka mai da yin wa’azi sana’arsu. In ji labarin da ke cikin Linjilar Luka, Bitrus ya ce: “Ga mu, mun bar namu, mun bi ka.” (Luka 18:28) Yawancinmu ba ma bukatar mu bar dukan ‘abubuwanmu’ don mu bi Yesu. Amma muna bukatar mu yi ‘musun kanmu’ don mu zama mabiyan Kristi da kuma bayin Jehobah masu bauta masa da zuciya ɗaya. (Mat. 16:24) Irin wannan tafarkin ya kawo albarka mai yawa. (Ka karanta Matta 19:29.) Nuna ƙwazo a wajen yin bishara don yin koyi da Kristi yana faranta mana zuciya, musamman idan muka ɗan saka hannu wajen taimaka wa wani ya kusanci Allah da kuma Ɗansa ƙaunatacce.
5. Ka faɗi labarin da ke nuna abin da baƙon haure zai iya yi idan ya koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki.
5 Valmir, wani ɗan Brazil wanda ke zaune a tsakiyar ƙasar Suriname, yana sana’ar haƙan zinariya. Mashayi ne kuma yana lalata. Sa’ad da yake zaune a cikin birni, Shaidun Jehobah sun soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ya soma yin nazari a kullum, ya canja rayuwarsa, kuma ya yi baftisma. Sa’ad da ya ga cewa aikinsa ba ya son ya ƙyale shi ya yi rayuwar da ta jitu da bangaskiyarsa, ya sayar da sana’ar da take kawo masa kuɗi sai ya ƙaura zuwa Brazil don ya taimaka wa iyalinsa su sami gaskiya. Da zarar sun sami gaskiya, yawancin bakin haure sukan daina yin aiki a manyan ƙasashe don su koma ƙasarsu da niyyar taimaka wa ’yan’uwansu da sauran mutane su sami gaskiya. Irin waɗannan masu shelar Mulki suna nuna ƙwazo sosai a aikin bishara.
6. Menene za mu iya yi idan ba za mu iya ƙaura zuwa inda ake bukatar ƙarin masu wa’azin Mulki ba?
6 Shaidu da yawa sun koma yankunan da ake bukatar ƙarin masu wa’azin Mulki. Wasu suna hidima a ƙasashen waje. Wataƙila, mu ba za mu iya yin hakan ba, amma za mu iya yin koyi da Yesu ta wajen yin iya ƙoƙarinmu a hidima.
Jehobah Yana Yin Tanadin Koyarwar da Muke Bukata
7. Waɗanne makarantu ne ake da su don koyar da waɗanda suke son su faɗaɗa iyawarsu a matsayinsu na masu shelar Mulki?
7 Kamar yadda Yesu ya sami koyarwa daga Ubansa, mu ma muna iya yin amfani da ilimin da Jehobah yake tanadinsa a yau. Yesu da kansa ya ce: “A cikin Annabawa an rubuta, Dukansu kuwa Allah za ya koya musu.” (Yoh. 6:45; Isha. 54:13) A yau, akwai makarantu na musamman da aka tsara don su taimaka mana mu zama ƙwararrun masu shelar Mulki. Babu shakka, dukanmu mun amfana daga Makarantar Hidima ta Allah a ikilisiyoyinmu. Majagaba sun sami gatan halartar Makarantar Hidima ta Majagaba. Ƙwararrun majagaba da yawa sun sake samun damar halartar wannan makarantar a karo na biyu. Dattawa da bayi masu hidima sun halarci Makarantar Hidima na Mulki don su kyautata iya koyarwarsu da kuma hidimar da suke yi wa ’yan’uwa masu bi. Yawancin dattawa da bayi masu hidima da ba su yi aure ba sun halarci Makarantar Koyar da Masu Hidima, wadda take koyar da su su taimaka wa mutane a aikin wa’azi. Kuma yawancin ’yan’uwa maza da mata da aka tura ƙasashen waje su yi wa’azi sun sami koyarwa a Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead.
8. Menene wasu ’yan’uwa suke sadaukarwa domin koyarwar da Jehobah yake tanadinsa?
8 Yawancin Shaidun Jehobah sun yi canje-canje don su halarci waɗannan makarantun. Don ya halarci Makarantar Koyar da Masu Hidima a Kanada, Yugu ya ajiye aikin da yake yi domin mai kamfanin ya hana shi ɗaukan hutu. “Ban yi da na sanin yin hakan ba,” in ji Yugu. “Da a ce ma sun yarda in ɗauki hutu, da za su so in ci gaba da yin aiki na dindindin da kamfanin. Amma a yanzu a shirye ni ke ga duk wani aikin da zan iya samu daga Jehobah.” Domin su amfana daga koyarwar da Allah ke tanadinsa, yawanci da son rai sun sadaukar da abubuwan da suke ɗauka da tamani sosai a dā.—Luka 5:28.
9. Ka ba da misalin da ke nuna amfanin koyarwar Nassi da kuma ƙwazo.
9 Koyarwa na Nassi da ƙwazo suna da amfani sosai. (2 Tim. 3:16, 17) Yi la’akari da abin da ya sami Saulo da ke zaune a Guatemala. An haife shi yana da ɗan taɓuwa a ƙwaƙwalwarsa, kuma wata a cikin malamansa ta gaya wa mamarsa cewa ba za ta iya matsa wa yaron ya koyi yadda ake yin karatu ba, domin hakan zai jawo masa taƙaici ne kawai. Saulo ya bar makaranta ba tare da sanin yadda ake karatu ba. Amma, wani Mashaidi ya koya wa Saulo yadda ake karatu, ta wajen yin amfani da littafin nan Apply Yourself to Reading and Writing. Daga baya, Saulo ya sami ci gaba har ya soma ba da jawabai a Makarantar Hidima ta Allah. Wata rana mamar Saulo ta sadu da malamarsa sa’ad da take hidima na gida-gida. Sa’ad da ta ji cewa Saulo ya koyi yadda ake yin karatu, malamar ta gaya wa mamar ta zo tare da shi a mako mai zuwa. Sa’ad da makon ya zagayo, malamar ta tambayi Saulo, “Menene za ka koya mini?” Sai Saulo ya soma karanta sakin layi daga littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? “Na yi mamakin cewa kai ne ke koyar da ni a yanzu,” in ji malamar. Cike da hawaye a idanunta, sai ta rungumi Saulo.
Koyarwar da ke Motsa Zuciya
10. Wane kayan aiki mai kyau ne muke da shi na koyar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki?
10 Yesu ya koyar ne kawai da abubuwan da Jehobah ya koya masa da kuma abubuwan da ke cikin rubutacciyar Kalmar Allah. (Luk 4:16-21; Yoh. 8:28) Muna bin misalin Yesu ta wajen bin shawararsa da kuma manne wa Nassosi. Shi ya sa dukanmu muke magana da kuma tunani iri ɗaya, kuma hakan na sa mu ƙara kasancewa da haɗin kai. (1 Kor. 1:10) Muna godiya sosai domin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yana yin tanadin littattafan da aka wallafa bisa ga abubuwan da ke cikin Littafi Mai Tsarki don su taimaka mana mu ci gaba da koyar da abu ɗaya mu kuma cim ma aikinmu na masu bishara! (Mat. 24:45; 28:19, 20) Ɗaya daga cikin waɗannan littattafan shi ne Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa, wanda a yanzu akwai shi a harsuna 179.
11. Ta yaya ne wata ’yar’uwa a Habasha ta sha kan hamayya ta wajen yin amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
11 Yin nazarin Nassosi ta wajen yin amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa zai iya canja zuciyar ’yan hamayya. Akwai lokacin da Lula, wata ’yar’uwa majagaba da ke ƙasar Habasha take nazarin Littafi Mai Tsarki da wata, sai ’yar’uwar ɗalibar ta faɗa dakin kuma ta ce su daina nazarin. Lula ta ɗan tattauna da ita ta wajen yin amfani da kwatancin jabun kuɗi da ke babi na 15 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa. Sai matar ta daina fushi kuma ta ƙyale su su ci gaba da nazarin. Ta hallara sa’ad da suka yi nazari na gaba kuma ta ce tana son a soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ita, har ma ta ce za ta biya kuɗi. Ta soma yin nazari sau uku a mako kuma ta sami cin gaba a ruhaniya sosai.
12. Ka ba da misalin da ke nuna yadda matasa za su iya koyar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki.
12 Matasa suna iya taimaka wa mutane ta wajen yin amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa. Sa’ad da Keanu ɗan shekara 11 da ke Hawaii yake karanta wannan littafin a makaranta, ɗaya daga cikin ’yan ajinsa ya tambaye shi, “Me ya sa ba ka kiyaye ranaku masu tsarki?” Sai Keanu ya karanta amsar daga cikin rataye mai jigo “Ya Kamata Ne Mu Kiyaye Ranaku Masu Tsarki?” Sai ya buɗe sashen da ke ɗauke da abubuwan da ke cikin littafin kuma ya tambayi yaron bayanin da ya fi so. Sai suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki. A shekarar hidimar da ta shige, Shaidun Jehobah sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 6,561,426 kuma yawancinsu sun yi amfani ne da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa. Kana amfani da wannan littafin sa’ad da ka ke nazarin Littafi Mai Tsarki?
13. Ta yaya ne nazarin Littafi Mai Tsarki zai iya yin tasiri a kan mutane?
13 Yin nazarin Nassosi ta wajen yin amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa zai iya yin tasiri sosai a kan waɗanda suke son su yi nufin Allah. Wasu majagaba na musamman waɗanda ma’aurata ne da ke zaune a ƙasar Norway sun soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wata iyali ’yan Zambiya. Ma’auratan ’yan Zambiya suna da yara mata uku kuma ba sa son su sake haihuwa. Sa’ad da matar ta sami ciki, sai suka tsai da shawara cewa za su zubar da cikin. ’Yan kwanaki kafin su je su ga likita, sun yi nazarin babin nan mai jigo “Ra’ayin Allah Game da Rai.” Hoton ɗan tayin da ke cikin babin ya taɓa zuciyar ma’auratan sosai, wanda hakan ya sa suka yanke shawara cewa ba za su zubar da cikin ba. Sun sami ci gaba a ruhaniya kuma suka sa ma ɗansu sunan wanda ya yi nazari da su.
14. Ka ba da misalin yadda yin rayuwar da ta jitu da abin da muke koyarwa za ta iya kawo sakamako mai kyau.
14 Wani abu mai muhimmanci game da koyarwar Yesu shi ne yin abin da ya koyar. Mutane da yawa suna son hali mai kyau na Shaidun Jehobah, waɗanda suke yin koyi da halin Yesu. A ƙasar New Zealand, wani ɗan kasuwa ya ajiye jakarsa a cikin motarsa sai ɓarayi suka zo suka sace ta. Ya kai ƙara wajen ’yan sanda, sai suka ce masa: “Za ka iya samun jakarka ne kawai da abubuwan da ke ciki idan Mashaidin Jehobah ne ya tsince ta.” Wata Mashaidiyar da take sayar da jaridu ta tsinci jakar. Sa’ad da ya sami labarin hakan, sai mai jakar ya je gidan ’yar’uwar. Ya yi farin ciki da ya ga cewa wata takarda mai muhimmanci a gare shi tana ciki. ’Yar’uwar ta ce masa, “Ya dace in mayar maka da kayanka tun da yake ni Mashaidiyar Jehobah ce.” Ɗan kasuwan ya yi mamaki, domin ya tuna abin da ɗan sandan ya gaya masa da safe. Babu shakka, Kiristoci na gaskiya suna yin rayuwar da ta jitu da na Littafi Mai Tsarki kuma suna yin koyi da Yesu.—Ibran. 13:18.
Ka Yi Koyi da Irin Halin da Yesu Ya Nuna wa Mutane
15, 16. Ta yaya za mu sa mutane su so saƙon da muke wa’azinsa?
15 Irin halin da Yesu ya nuna wa mutane ne ya sa suka saurari saƙonsa. Alal misali, ƙauna da tawali’u da yake nuna musu ne ya sa talakawa suka kusance shi. Ya nuna juyayi ga waɗanda suka zo wurinsa kuma ya ƙarfafa su, ya kuma warkar da mutane marasa lafiya da yawa. (Ka karanta Markus 2:1-5.) Ba za mu iya yin mu’ujizai ba, amma za mu iya nuna ƙauna, tawali’u, da kuma juyayi, wato halayen da za su taimaka wajen jawo mutane zuwa gaskiya.
16 Juyayi ya taimaka sa’ad da wata majagaba na musamman mai suna Tariua ta je gidan wani tsoho mai suna Beere, wanda ke zaune a can cikin wani tsibiri a ƙasar Kiribati da ke Kudancin Tekun Pasifik. Ko da yake mutumin ba ya son ya saurari wa’azin da za a yi masa, Tariua ta lura cewa wani gefe a jikin mutumin ya shanye, sai ta ji tausayinsa. Ta tambaye shi, “Ka taɓa jin alkawarin da Allah ya yi wa mutanen da suke ciwo da kuma tsofaffi kuwa?” Sai ta karanta wata aya daga annabcin Ishaya. (Ka karanta Ishaya 35:5, 6.) Cike da mamaki, mutumin ya ce: “Na yi shekaru da yawa ina karanta Littafi Mai Tsarki kuma wani mai wa’azi na addininmu ya yi shekaru yana ziyara na, amma ban taɓa ganin wannan a cikin Littafi Mai Tsarki ba.” An soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Beere, kuma ya samu ci gaba sosai a ruhaniya. Hakika, shi naƙasasshe ne, amma yanzu ya yi baftisma, shi ne ke kula da wani rukunin da ke a ware, kuma yana yin wa’azin bishara a cikin dukan tsibirin.
Ka Ci Gaba da Yin Koyi da Kristi
17, 18. (a) Ta yaya za ka iya zama mai bishara wanda ya yi nasara? (b) Menene waɗanda suka ɗauki hidimarsu da muhimmanci za su samu?
17 Kamar yadda abubuwan farin ciki da ake shaidawa a hidima suka nuna, za mu iya zama masu bishara da suka yi nasara idan muka nuna irin halayen Yesu. Shi ya sa yake da kyau mu yi koyi da Kristi a matsayin masu shelar bishara da ƙwazo.
18 Sa’ad da wasu suka zama mabiyan Yesu a ƙarni na farko, Bitrus ya yi wannan tambayar: “Me za mu samu fa?” Sai Yesu ya ce: “Kowanene ya bar gidaje, ko ’yan’uwa maza, ko ’yan’uwa mata, ko uba, ko uwa, ko ’ya’ya, ko ƙasashe, sabili da sunana, za ya sami riɓi ɗari; za ya kuma gāji rai na har abada.” (Mat. 19:27-29) Mu ma za mu shaida hakan idan muka ci gaba da yin koyi da Mai wa’azi mafi girma, Yesu Kristi.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya ne Jehobah yake koyar da mu mu zama masu bishara?
• Me ya sa littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa yake da amfani a hidimarmu?
• Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu a halayenmu ga mutane?
[Hoto a shafi na 17]
Sa’ad da Yesu ya gayyaci Bitrus, Andarawus, Yaƙub, da Yohanna su zama mabiyansa, sun amsa babu ɓata lokaci
[Hoto a shafi na 19]
Littattafai kamar “Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa” yana taimaka mana mu kasance da haɗin kai a koyarwarmu