Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 4/1 pp. 7-11
  • “Ka Yi Aikin Mai-bishara”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ka Yi Aikin Mai-bishara”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Masu Bishara da Himma na Dā
  • Masu Bishara da Himma a Yau
  • Yin Wa’azi Gida Gida
  • Me Ya Sa Za a Ci Gaba da Yin Wa’azi?
  • Muna Samun Amfani ta Wa’azin Bishara
  • Ku Ajiye wa Kanku Dukiya a Sama
  • Ka Yi Aikin Da Aka Ba Ka Na Mai-bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Dukan Kiristoci Na Gaskiya Masu Wa’azin Bishara Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Kana Cika Hidimarka ga Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Fa’idodin Bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 4/1 pp. 7-11

“Ka Yi Aikin Mai-bishara”

“Ka natsu cikin dukan abu, . . . ka yi aikin mai-bishara.”—2 Timothawus 4:5.

1. Wane umurni Yesu ya ba mabiyansa?

ANA shelar sunan Jehovah da nufe-nufensa a dukan duniya. Wannan haka yake domin mutanen Allah da suka keɓe kansu sun ɗauki umurnin da Yesu Kristi ya ba mabiyansa da muhimmanci, sa’ad da ya ce: “Ku tafi . . . ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.”—Matta 28:19, 20.

2. Wane umurni aka ba wa Timothawus mai kula, kuma wace hanya ɗaya ce Kiristoci masu kula za su cika hidimarsu?

2 Almajiran Yesu na ƙarni na farko sun ɗauki wannan umurni da muhimmanci. Alal misali, manzo Bulus ya aririce ɗan’uwansa Timothawus Kirista mai kula: “Ka yi aikin mai-bishara, ka cika hidimarka.” (2 Timothawus 4:5) A yau, hanya ɗaya da mai kula yake cika hidimarsa ita ce ta zama mai shelar Mulki da himma, wanda yake sa hannu a hidimar fage a kai a kai. Alal misali, mai kula da Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya yana da zarafi mai kyau na ja-gora a aikin wa’azi da kuma koya wa mutane. Bulus ya cika hakkinsa na shelar bishara kuma ya taimaka a koya wa mutane hidimar.—Ayukan Manzanni 20:20; 1 Korinthiyawa 9:16, 17.

Masu Bishara da Himma na Dā

3, 4. Menene Filibbus mai bishara ya shaida?

3 An san cewa Kiristoci na farko masu bishara ne da himma. Ka yi la’akari da mai bishara Filibbus. Yana cikin “mutum bakwai . . . waɗanda a ke shaidarsu, cike da Ruhu Mai-tsarki da hikima kuma” da aka zaɓa ya riƙa rarraba abinci kowacce rana ban da son kai tsakanin gwauraye Kiristoci Helenawa da Ibraniyawa a Urushalima. (Ayukan Manzanni 6:1-6) Bayan wannan aiki na musamman ya ƙare, kuma tsanantawa ya sa dukan Kiristoci suka watse ban da manzannin, sai Filibbus ya tafi Samariya. A wajen ya yi shelar bishara kuma ruhu mai tsarki ya ba shi ƙarfi ya fitar da aljannu, ya kuma warkar da guragu da naƙasassu. Samariyawa da yawa suka amince da saƙon Mulki kuma suka yi baftisma. Da suka ji game da wannan, manzanni a Urushalima suka aika da manzanni Bitrus da Yohanna zuwa Samariya don masu bi sababbi da suka yi baftisma su samu ruhu mai tsarki.—Ayukan Manzanni 8:4-17.

4 Ruhun Allah ya ja-goranci Filibbus ya sadu da Habashi bābā a hanya zuwa Gaza. Bayan Filibbus ya bayyana masa annabcin Ishaya ƙwarai, wannan “mai-sarauta dayawa ƙarƙashin Kandakatu, sarauniyar Habashawa” ya ba da gaskiya ga Yesu Kristi kuma aka yi masa baftisma. (Ayukan Manzanni 8:26-38) Bayan haka, Filibbus ya tafi Ashduda daga nan ya je Kaisariya yana “wa’azin bishara ga dukan birane” a kan hanya. (Ayukan Manzanni 8:39, 40) Babu shakka ya kafa misali mai kyau na yin aikin bishara!

5. Menene musamman ’ya’yan Filibbus mata huɗu suke yi?

5 Filibbus har ila yana da ƙwazo a hidima a Kaisariya bayan misalin shekaru 20. Sa’ad da Bulus da Luka suka sauka a gidansa, “yana da ’ya’ya huɗu mata, budurwai, suna yin annabci.” (Ayukan Manzanni 21:8-10) Babu shakka an koyar da su sosai a ruhaniya, suna da himma a hidima, har ma suna da gatar yin annabci. Himmar iyaye a hidima za ta kawo sakamako mai kyau ga yaransu a yau, zai sa su yi aikin bishara da himma a rayuwarsu.

Masu Bishara da Himma a Yau

6. Wace nasara masu wa’azin bishara na ƙarni na farko suka yi?

6 A cikin annabcinsa mai girma game da zamaninmu da kuma lokacin ƙarshe, Yesu Kristi ya ce: “Dole kuma sai an yi wa’azin bishara ga al’ummai duka tukuna.” (Markus 13:10) Ƙarshen zai zo bayan an yi wa’azin bishara “cikin iyakar duniya.” (Matta 24:14) Da Bulus da wasu masu wa’azin bishara na ƙarni na farko suka yi shelar bishara, mutane da yawa suka zama masu bi, kuma aka kafa ikilisiyoyi a wurare da yawa a dukan Daular Roma. Dattawa da aka naɗa su yi hidima a waɗannan ikilisiyoyi sun yi aikin bishara tare da ’yan’uwansu kuma suka yaɗa aikin wa’azi a ko’ina. Maganar Jehovah ta ci gaba da yawaita da yin nasara a waɗancan kwanaki, yadda yake a yau domin miliyoyin Shaidun Jehovah suna aikin wa’azin bishara. (Ayukan Manzanni 19:20) Kana cikin waɗannan masu yabon Jehovah da farin ciki?

7. Menene masu shelar Mulki suke yi a yau?

7 Masu shelar Mulki da yawa a zamanin yau suna amfani da zarafi da suke da shi don su ƙara sa hannu a aikin wa’azin bishara. Mutane dubbai sun shiga hidimar wa’azi a ƙasar waje, majagaba dubbai na kullum da na ɗan lokaci suna wa’azin bishara na cikakken lokaci. Kuma maza da mata, da yara da suke hidima na masu shelar Mulki da himma suna aiki mai kyau! Hakika, dukan mutanen Jehovah, Kiristoci masu bishara suna more albarkarsa mai girma yayin da suke bauta masa da zuciya ɗaya.—Zephaniah 3:9.

8. Wane aikin sa shaida ake yi yanzu, kuma su waye suke yi?

8 Allah ya ba mabiyan Yesu shafaffu hakkin su yi shelar bishara a dukan duniya. “Waɗansu tumaki” na Kristi da suke ƙaruwa suna tallafa musu a wannan aikin bishara. (Yohanna 10:16) A hanyar annabci, an kamanta wannan aiki na ceton rai da sa shaida a goshin waɗanda suke ajiyar zuciya suna kuwa damuwa saboda dukan ƙazanta da ake yi. Ba da daɗewa ba, za a halaka miyagu. Amma kafin lokacin, gata ce mu gaya wa mazaunan duniya gaskiya mai ceton rai!—Ezekiel 9:4-6, 11.

9. Ta yaya za a taimaki sababbi a hidima?

9 Idan da daɗewa muna aikin wa’azin bishara, babu shakka za mu iya taimakon sababbi cikin ikilisiya. Wani lokaci, za mu iya zuwa aikin bishara tare da su. Ana ƙarfafa dattawa su yi iyakacin ƙoƙarinsu su ƙarfafa ’yan’uwa masu bi a ruhaniya. Ƙoƙarce-ƙoƙarcen masu kula masu tawali’u zai taimake wasu su kasance da himma kuma su zama masu bishara da suke ba da ’ya’ya.—2 Bitrus 1:5-8.

Yin Wa’azi Gida Gida

10. Kristi da mabiyansa na farko sun kafa wane misali a hidima?

10 Yesu Kristi mai wa’azin bishara ya kafa wa mabiyansa misali mafi kyau. Game da hidimar Kristi da manzanninsa, Kalmar Allah ta ce: “Ya yi ta yawo a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azi, yana kawo bishara ta mulkin Allah, tare da shi kuma su goma sha biyu.” (Luka 8:1) Manzannin kuma fa? Bayan an cika su da ruhu mai tsarki a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., “kowace rana fa, cikin haikali da cikin gida, ba su fasa koyarwa da yin wa’azi kuma Yesu Kristi ne.”—Ayukan Manzanni 5:42.

11. Bisa ga Ayukan Manzanni 20:20, 21, menene manzo Bulus ya yi a hidimarsa?

11 Domin himmarsa a aikin wa’azin bishara, manzo Bulus ya gaya wa dattawa Kirista na Afisus: “Ban ji nauyin bayyana muku kowane abu mai-amfani, gida gida ni ke bin ku, ina koya muku a sarari.” Sa’ad da Bulus yake ‘koyarwa gida gida,’ yana ziyarar gidajen ’yan’uwa masu bauta wa Jehovah ne, ko kuwa yana ziyarar kiwon masu bi ne? A’a, ya ci gaba da bayani: “Ina shaida ga Yahudawa da Helenawa tuba zuwa ga Allah, da bangaskiya ga Ubangijinmu Yesu Kristi.” (Ayukan Manzanni 20:20, 21) Galibi, waɗanda sun riga sun keɓe kansu ga Jehovah ba sa bukatar koyarwa game da “tuba zuwa ga Allah, da bangaskiya ga Ubangijinmu Yesu Kristi.” Bulus ya koyar da dattawa Kiristoci na Afisus a hidimar gida gida, kuma ya koya wa marasa bi game da tuba da kuma bangaskiya. Ta yin haka, Bulus yana kwaikwayon yadda Yesu ya yi.

12, 13. Daidai da Filibbiyawa 1:7, menene mutanen Jehovah suka yi game da ’yancinsu na wa’azi?

12 Hidimar gida gida za ta iya kasance da wuya. Alal misali, wasu suna jin fushi sa’ad da muka zo gidansu da saƙon Littafi Mai Tsarki. Ba ma son mu sa mutane fushi. Duk da haka, hidimar gida gida ta fito daga Nassi, kuma ƙaunar Allah da maƙwabta ce ke motsa mu mu yi shaida a wannan hanyar. (Markus 12:28-31) Don mu ‘kāre’ ’yancinmu na wa’azi gida gida ‘bisa doka,’ mun kai ƙara zuwa kotu, har da Babban Kotu na Amirka. (Filibbiyawa 1:7) Kusan koyaushe muna yin nasara a wannan kotu. Ga wani misalin yadda aka yanke shari’a:

13 “Da daɗewa ana rarraba warƙoƙi na addini a bishara na mishan—daɗewarsa daidai yake da daɗewar lokacin da aka ƙaga maɗaba’a. Abin motsawa ne a ƙungiyoyin addini dabam dabam shekaru da yawa. Ɗarikoki addinai dabam dabam suna amfani da wannan hanya sosai a yau, waɗanda majagabansu suna jawo mabiya ga imaninsu ta wajen ziyarar dubbai a gidajensu da kuma yi musu wa’azi. . . . Irin wannan aiki na addini har ila yana da muhimmanci a ƙarƙashin dokar ’Yancin Addini [a tsarin doka ta Amirka] yadda bauta a coci da wa’azi a bagadi yake da muhimmanci.”—Murdock v. Pennsylvania na shekara ta 1943.

Me Ya Sa Za a Ci Gaba da Yin Wa’azi?

14. Menene zai zama sakamakon hidimarmu?

14 Akwai dalilai da yawa da ya sa za a yi wa’azi gida gida. Kowane lokaci da muka ziyarci wani, muna ƙoƙari mu dasa iri na gaskiya ta Nassi. Ta wajen koma ziyara, muna zuba ma shukin ruwa. Kuma wannan zai kawo sakamako mai kyau, domin Bulus ya rubuta: “Ni na dasa, Apollos ya yi ban ruwa; amma Allah ne ya bada amfani.” (1 Korinthiyawa 3:6) Saboda haka, bari mu ci gaba da ‘dasa da kuma ba da ruwa,’ da gaba gaɗi cewa Jehovah ‘zai sa ya ba da amfani.’

15, 16. Me ya sa muke ziyarar gidajen mutane a kai a kai?

15 Muna aiki na masu wa’azin bishara domin rayuka suna cikin haɗari. Ta wa’azi za mu ceci kanmu da masu sauraronmu. (1 Timothawus 4:16) Idan muka san cewa rayuwar mutum tana cikin haɗari, za mu yi ɗan ƙoƙari ne kawai mu taimake shi? Da ƙyar! Tun da yake za a ceci mutum ta ziyararmu, za mu riƙa ziyarar gidajen mutanen a kai a kai. Yanayi na canjawa. Wanda ba ya son ya saurara don ya taƙure, zai so ya ji saƙon Littafi Mai Tsarki a wani lokaci. Za mu iya sadu da wani dabam cikin iyalin, sa’ad da muka ziyarci gidan da muka je dā, kuma wannan zai sa a tattauna Nassi.

16 Ba kawai yanayinsu ba amma kuma halin waɗanda suke gidajen za su iya canjawa. Alal misali, rashin waɗanda ake ƙauna cikin mutuwa zai iya sa mutum ya saurari saƙon Mulki. Za mu ta’azantar da mutumin, mu sa ya san bukatarsa ta ruhaniya, kuma mu nuna masa yadda za a ƙosar da shi.—Matta 5:3, 4.

17. Menene dalili na musamman da ya sa muke aikin wa’azi?

17 Dalili na farko da ya sa muke wa’azi gida gida ko kuma sa hannu a wasu hanyar hidima ta Kirista shi ne cewa muna son mu sa a san sunan Jehovah. (Fitowa 9:16; Zabura 83:18) Yana da ban albarka sa’ad da aikinmu na wa’azin bishara ya taimaki masu son gaskiya da adalci su zama masu yabon Jehovah! Mai Zabura ya rera: “Samari da ’yan mata; tsofaffi da yara: Bari su yabi sunan Ubangiji; gama sunansa kaɗai maɗaukaki ne: darajatasa tana bisa kan duniya da sama.”—Zabura 148:12, 13.

Muna Samun Amfani ta Wa’azin Bishara

18. Ta yaya muke samun taimako daga yin aikin wa’azin bishara?

18 Yin aikin mai bishara na taimakonmu a hanyoyi dabam dabam. Yin wa’azin bishara gida gida na taimaka mana mu koya tawali’u, musamman sa’ad da ba a marabce mu ba da kyau. Don mu zama masu wa’azin bishara da kyau, muna bukatar mu zama kamar Bulus, wanda ya ‘zama dukan abu ga dukan mutane, domin ya ceci waɗansu.’ (1 Korinthiyawa 9:19-23) Abubuwa da muke fuskanta a hidima na taimakonmu mu kasance da basira. Ta wajen dogara ga Jehovah da faɗan kalmomi da sun dace, za mu iya amfani da gargaɗin Bulus: “Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.”—Kolossiyawa 4:6.

19. Yaya ruhu mai tsarki ke taimakon masu bishara?

19 Aikin wa’azin bishara na motsa mu mu dogara ga ruhu mai tsarki na Allah. (Zechariah 4:6) ’Ya’ya da yake bayarwa—“ƙauna . . . farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa”—waɗannan za su bayyana a hidimarmu. (Galatiyawa 5:22, 23) Suna shafan yadda muke bi da mutane, bin ja-gorar ruhun na taimaka mana mu nuna ƙauna, farin ciki da kuma salama, mu kasance da tsawon jimrewa da nasiha, mu yi nagarta da aminci, mu kasance da tawali’u da kamewa sa’ad da muke shelar bishara.

20, 21. Waɗanne albarka da fa’idodi ake da su na shagala cikin aikin bishara?

20 Wata albarka da muke samu da yake mu masu wa’azin bishara ne ita ce muna daɗa tausayawa. Sa’ad da mutane suka gaya mana damuwarsu—kamar su ciwo, rashin aiki, damuwa ta gida—ko da yake mu ba masu ba da shawara ba ne, muna nuna musu nassosi da ke ƙarfafawa kuma ke yi musu ta’aziyya. Muna damuwa game da mutane da suka makanta a ruhaniya amma kamar suna ƙaunar adalci. (2 Korinthiyawa 4:4) Kuma abin farin ciki ne mu taimaki waɗanda aka “ƙaddara [zuciyar kirki] ga rai na har abada” a ruhaniya!—Ayukan Manzanni 13:48.

21 Sa hannu a aikin bishara a kai a kai na taimakonmu mu mai da hankali a kan abubuwa na ruhaniya. (Luka 11:34) Babu shakka, wannan na da ban amfani, domin idan ba mu yi haka ba za mu iya fāɗa cikin jaraba na son dukiya da ke ko’ina a wannan duniya. Manzo Yohanna ya aririce Kiristoci: “Kada ku yi ƙaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya. Idan kowa ya yi ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa ba. Gama dukan abin da ke cikin duniya, da kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne. Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yohanna 2:15-17) Da yake mu masu wa’azin bishara ne, shagala da kuma himmantuwa cikin aikin Ubangiji na taimaka mana kada mu yi ƙaunar duniya.—1 Korinthiyawa 15:58.

Ku Ajiye wa Kanku Dukiya a Sama

22, 23. (a) Wace dukiya Kiristoci masu wa’azin bishara suka ajiye? (b) Ta yaya talifi na gaba zai taimake mu?

22 Yin aikin wa’azin Mulki da himma na kawo fa’idodi na dindindin. Yesu ya nuna wannan sa’ad da ya ce: “Kada ku ajiye wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke cinyewa, inda ɓarayi kuma ke hudawa suna sata: amma ku ajiye wa kanku dukiya cikin sama, inda asu da tsatsa ba su cinyewa, ɓarayi kuma ba su hudawa su yi sata ba: gama wurinda dukiyarka ta ke, can zuciyarka za ta kasance kuma.”—Matta 6:19-21.

23 Bari mu ci gaba da ajiye wa kanmu dukiya a sama, da sanin cewa ba za mu iya samun gata da ya fi zama Shaidu masu wakiltan Ubangiji Jehovah Mai Ikon Mallaka ba. (Ishaya 43:10-12) Yayin da muke cika aikinmu na masu hidima na Allah, mai yiwuwa za mu ji kamar wata mata Kirista mai shekara 90, da ta ce haka game da hidimarta da daɗewa ga Allah: “Na gode wa Jehovah da ya jimre da ni a dukan waɗannan shekarun, kuma na yi addu’a cewa zai zama Ubana mai ƙauna har abada.” Idan mu ma muna son dangantakarmu da Allah haka, babu shakka za mu so mu yi aiki na mai bishara sosai. Talifi na gaba zai taimake mu ga yadda za mu cika hidimarmu.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa za mu yi aikin mai wa’azin bishara?

• Me za ka iya faɗa game da aikin masu wa’azin bishara na dā da kuma na yanzu?

• Me ya sa muke wa’azi gida gida?

• Ta yaya kake amfana a yin aikin mai bishara?

[Hotuna a shafi na 7]

Masu bishara kamar Filibbus da ’ya’yansa mata suna da takwarar masu farin ciki a zamanin yau

[Hoto a shafi na 11]

Yaya kake amfana yayin da kake yi wa mutane bishara?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba