Ka Yi Aikin Da Aka Ba Ka Na Mai-bishara
“Ka yi aikin mai-bishara, ka cika hidimarka.”—2 TIM. 4:5.
1. Me ya sa Jehobah ne mai-bishara na farko?
MAI-BISHARA mutum ne da ke yin shelar albishiri. Jehobah ne mai-bishara na farko. Ba da daɗewa ba bayan Adamu da Hawwa’u suka yi tawaye, Jehobah ya sanar da wani albishiri. Ya ce za a halaka macijin, wato Shaiɗan Iblis. (Far. 3:15) Shekaru da yawa bayan wannan sanarwar, Jehobah ya hure mazaje masu aminci su rubuta dalla-dalla yadda za a kawar da zargin da ake wa sunansa da yadda za a halaka ayyukan Shaiɗan da kuma yadda ’yan Adam za su sake kasancewa cikin aljannar da iyayenmu na fari suka ɓatar.
2. (a) Mene ne matsayin mala’iku a aikin yin bishara? (b) Wane misali ne Yesu ya kafa wa masu-bishara?
2 Mala’iku ma masu-bishara ne. Suna yin shelar bishara kuma suna taimaka wa wasu ma su yi hakan. (Luk 1:19; 2:10; A. M. 8:26, 27, 35; R. Yoh. 14:6) Sarkin mala’iku kuma fa? Sa’ad da Yesu yake duniya, ya kafa wa ’yan Adam masu-bishara misali. Yin wa’azi ne aiki mafi muhimmanci a rayuwar Yesu.—Luk 4:16-21.
3. (a) Mece ce bisharar da muke yaɗawa? (b) Waɗanne tambayoyi ne suke da muhimmanci a gare mu?
3 Yesu ya dokaci almajiransa su zama masu-bishara. (Mat. 28:19, 20; A. M. 1:8) Manzo Bulus kuma ya aririce amininsa Timotawus, ya ce: “Ka yi aikin mai-bishara, ka cika hidimarka.” (2 Tim. 4:5) Mece ce bisharar da ya kamata mu yaɗa a matsayin mabiyan Yesu? Wannan bisharar ta haɗa da gaskiya mai daɗaɗawa cewa Ubanmu na sama Jehobah yana ƙaunarmu. (Yoh. 3:16; 1 Bit. 5:7) Hanya ta musamman da Jehobah yake nuna wannan ƙaunar ita ce ta Mulkinsa. Saboda haka, muna gaya wa mutane cewa idan suka goyi bayan Mulkin Allah, suka yi biyayya ga Allah kuma suka kasance da aminci, za su zama aminansa. (Zab. 15:1, 2) Hakika, nufin Jehobah shi ne ya kawar da dukan wahala. Zai kuma kawar da dukan baƙin ciki da muke yi idan mun tuna da wahalar da muka sha a dā. Hakan bishara ce ƙwarai! (Isha. 65:17) Tun da mu masu-bishara ne, bari mu tattauna amsoshin muhimman tambayoyi biyu. Na ɗaya, me ya sa mutane suke bukatar bishara a yau? Na biyu, ta yaya za mu iya cim ma aikinmu a matsayin masu-bishara?
ME YA SA MUTANE SUKE BUKATAR BISHARA?
4. Wace ƙarya ce ake wa mutane a wasu lokatai game da Allah?
4 A ce an gaya maka cewa mahaifinka ya gudu ya bar ka da sauran ’yan’uwanka da mahaifiyarka. Kuma mutanen da suka ce sun san shi sun ce wai shi mai fahariya ne da ɓoye-ɓoye da kuma mugunta. Wasu suna ma iya ce kada ka ɓata lokaci kana nemansa domin ya riga ya mutu. Hakazalika, irin abin da ake gaya wa mutane da yawa ke nan game da Allah. Ana koya musu cewa ba zai yiwu a san Allah da gaske ba kuma shi mugu ne. Alal misali, wasu limamai suna da’awa cewa Allah zai azabta mugaye har abada a cikin wutar jahannama. Wasu kuma sun ce Allah ne yake jawo wahalar da muke sha sanadiyyar tsarar bala’i. Ko da yake bala’i yana shafan masu adalci da marasa adalci, sun ce hakan horo ne daga Allah.
5, 6. Ta yaya koyarwar bayyanau da kuma wasu koyarwar ƙarya suka shafi mutane?
5 Wasu sun ma ce Allah bai wanzu ba. Ka yi la’akari da koyarwar bayyanau. Mutane da yawa da suka gaskata da wannan koyarwar sun ce babu wanda ya halicci abubuwa. Wasu sun ce ’yan Adam wata irin dabba ce, shi ya sa suke yi kamar dabba a wasu lokatai. Sun ce idan masu iko suka zalunta marasa ƙarfi hakan halin halitta ne. Shi ya sa mutane da yawa suka gaskata cewa ba za a taɓa daina rashin adalci ba. Saboda haka, waɗanda suka gaskata da ra’ayin bayyanau ba su da bege.
6 Babu shakka, koyarwar bayyanau da kuma wasu koyarwar ƙarya sun daɗa sa matsalolin ’yan Adam su yi tsanani sosai a waɗannan kwanaki na ƙarshe. (Rom. 1:28-31; 2 Tim. 3:1-5) Waɗannan koyarwa ba bishara ba ce. Maimakon haka, kamar yadda manzo Bulus ya faɗa, sun sa mutane su kasance cikin “duhun hankali, bāre daga ran Allah.” (Afis. 4:17-19) Ƙari ga haka, koyarwar ra’ayin bayyanau da kuma na ƙarya sun hana mutane saurarar bisharar da Allah yake sanarwa.—Karanta Afisawa 2:11-13.
7, 8. Mene ne kaɗai zai taimaka wa mutane su fahimci bishara da kyau?
7 Idan mutane suna son su sulhunta da Jehobah, wajibi ne su gaskata cewa ya wanzu kuma su kusace shi. Za mu iya taimaka musu ta wajen gaya musu su yi nazari a kan abubuwan da Allah ya halitta. Idan mutane suka yi nazarin halitta ba tare da wata da’awa ba, za su koya hikima da kuma ikon Allah. (Rom. 1:19, 20) Ta yaya za mu taimaka wa mutane su fahimci cewa kome da Allah ya halitta suna da ban al’ajabi? Muna iya yin amfani da littafin nan Ka Kusaci Jehovah. Duk da haka, waɗanda suka yi nazarin halitta ba za su samu amsoshin tambayoyi masu muhimmanci a rayuwa ba. Alal misali, Me ya sa Allah ya ƙyale wahala ta ci gaba? Mene ne nufin Allah ga duniya? Allah yana kula da ni kuwa?
8 Yin nazarin Littafi Mai Tsarki ne kaɗai zai sa mutane su san Allah da kuma nufinsa. Gata ne sosai mu sa mutane su samu amsoshin tambayoyinsu! Idan muna son masu sauraronmu su fahimce mu, muna bukatar mu gaya musu gaskiya. Kuma yana da muhimmanci mu huɗubantar da su. (2 Tim. 3:14) Misalin Yesu zai taimaka mana mu ƙware wajen yin hakan. Me ya sa Yesu ya yi nasara? Wani abin da ya sa shi ne, don ya yi amfani da tambayoyi masu kyau. Ta yaya za mu yi koyi da shi?
ƘWARARRUN MASU BISHARA SUNA BUKATAR YIN TAMBAYA MAI KYAU
9. Mene ne muke bukatar mu yi don mu iya taimaka wa mutane?
9 Yadda Yesu ya yi, me ya sa za mu yi amfani da tambayoyi a hidimarmu? Ka yi la’akari da wannan yanayin. A ce likitanka ya ce maka yana da wani albishir, wato za ka warke idan ya yi maka fiɗa. Za ka amince da shi? Wataƙila. Amma, shin za ka yarda da shi kuwa idan ya yi maka wannan alkawarin kafin ma ya yi maka tambayoyi game da lafiyar jikinka? Da kyar. Ko da likitan ya ƙware sosai, yana bukatar ya yi maka tambayoyi don ya san abin da ke damunka, kafin ya taimaka maka. Haka nan ma, wajibi ne mu iya yin tambayoyi masu kyau don mu taimaka wa mutane su karɓi bisharar Mulkin. Ba za mu iya taimaka musu, ba idan ba mu san imaninsu ba.
Wajibi ne mu huɗubantar da masu sauraronmu don mu ratsa zuciyarsu
10, 11. Mene ne za mu cim ma idan muka yi koyi da yadda Yesu yake koyarwa?
10 Yesu ya san cewa yin tambayoyi zai taimaka wa malami ya san yanayin ɗalibinsa, kuma zai sa wanda ake tattaunawa da shi ya saurara da kyau. Alal misali, Yesu ya yi wa almajiransa wata tambaya mai sa mutum ya yi tunani, sa’ad da yake son su koya darasi game da kasancewa da tawali’u. (Mar. 9:33) Sa’ad da yake son ya sa Bitrus ya fahimci ƙa’idodi, ya yi masa jerin tambayoyi. (Mat. 17:24-26) A wani lokaci kuma, Yesu ya yi amfani da tambayoyin da ke sa mutum ya faɗi ra’ayinsa don ya san abin da suke tunani. (Karanta Matta 16:13-17.) Ta wajen yin tambayoyi da kuma kalamai, Yesu bai cika wa mutane da ilimi kawai ba, amma ya motsa su su ɗauki mataki.
11 Idan muka yi koyi da yadda Yesu yake yin amfani da tambayoyi, za mu cim ma abubuwa uku. Za mu san yadda za mu iya taimaka wa mutane, za mu iya rinjayar waɗanda suke ba da hujjoji don kada su saurare mu, kuma za mu iya koyar da masu tawali’u don su amfana. Ga yanayi uku da suka nuna yadda za mu yi amfani da tambayoyi da kyau.
12-14. Ta yaya za ka taimaki ɗanka ya yaɗa bishara da gaba gaɗi? Ka ba da misali.
12 Yanayi na ɗaya: A matsayin iyaye, mene ne za ka yi idan ɗanka ya gaya maka cewa yana son ya san yadda zai kāre imaninsa game da halitta a makaranta? Babu shakka cewa za ka so ka taimaka masa ya yaɗa bishara da gaba gaɗi. Maimakon ka kushe shi ko kuma ka shawarce shi nan take, zai fi kyau ka yi koyi da misalin Yesu ta wurin yi masa tambaya don ka ji ra’ayinsa. Ta yaya za ka yi hakan?
13 Bayan ka karanta wasu shafuffuka na littafin nan Ka Kusaci Jehovah da ɗanka, sai ka tambaye shi ko wanne cikin bayanan ne zai fi sa mutane tunani. Ka ƙarfafa shi ya yi tunanin wasu dalilan da suka sa ya yi imani da Mahalicci da kuma abin da ya sa yake son ya yi nufinsa. (Rom. 12:2) Ka sa ya san cewa ba sai dalilansa na yin imani da Mahalicci sun yi daidai da naka ba.
14 Ka gaya masa cewa zai iya tattaunawa da ɗan ajinsa kamar yadda ka tattauna da shi. Wato, bayan ya ɗan tattauna wasu batutuwa da ɗan ajinsa, sai ya yi masa tambayoyi da za su sa ya faɗi ra’ayinsa. Alal misali, yana iya gaya wa ɗan ajinsa ya karanta shafi na 172 da kuma sakin layi na 12 na littafin nan Ka Kusaci Jehovah. Sai ya tambaye shi, ‘Shin da gaske ne cewa ƙwaƙwalwar ɗan Adam tana iya ɗaukan bayanan da ke cikin dukan laburare na duniya kuma ba za ta cika ba?’ Wataƙila amsar ɗan ajin za ta zama E. Sa’annan ɗanka zai iya tambayarsa, ‘Amma, kana ganin wannan ya wanzu haka kawai?’ Ku gwada yin hakan tare a kai a kai don ka sa ya kasance da gaba gaɗin bayyana wa mutane imaninsa. Za ka taimaka wa ɗanka ya yi aikinsa na mai-bishara da kyau idan ka koya masa yin amfani da tambayoyi masu kyau.
15. Ta yaya za mu yi amfani da tambayoyi wajen taimaka wa wanda bai amince da wanzuwar Allah ba?
15 Yanayi na biyu: Sa’ad da muke wa’azi, muna iya haɗuwa da waɗanda ba su yarda cewa akwai Allah ba. Alal misali, idan wani ya gaya mana cewa bai gaskata da wanzuwar Allah ba, mene ne ya kamata mu yi? Maimakon mu ƙyale shi kurum, za mu iya tambayarsa ko ya daɗe da yin imani da hakan da kuma dalilansa na yin hakan. Mu saurare shi, kuma mu yaba masa don ya yi tunani sosai game da batun. Sai mu tambaye shi ko zai so ya karanta bayanin da ya nuna cewa an halicci abubuwa. Mutumin zai so ya karanta bayanin idan shi ba mai son nace wa nasa ra’ayi ba ne. Sai mu ba shi littafin nan Ka Kusaci Jehovah. Yin tambayoyi cikin basira da kuma sauƙin kai zai sa mu san abin da ke cikin zuciyar mutane, kuma mu taimake su su saurari bishara.
16. Me ya sa yake da kyau mu tabbata cewa ɗalibinmu ba ya karanta amsoshi daga littafin da muke nazarinsa?
16 Yanayi na uku: Idan muna nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibi, wataƙila za mu sa ɗalibin ya riƙa karanta amsar daga littafin da muke amfani da shi. Amma, hakan ba zai taimaka masa ya samu ci gaba ba. Me ya sa? Domin ɗalibin da ba ya yin bimbini kafin ya ba da amsa ba zai kasance da imani mai ƙarfi ba. Idan ya fuskanci tsanani, zai yi yaushi kamar furen da ya sha rana. (Mat. 13:20, 21) Idan ba ma son hakan ya faru da ɗalibinmu, ya kamata mu riƙa jin ra’ayinsa game da abin da yake koya. Ka tambaye shi ka ji ko ya yarda da abin da kuka tattauna. Mafi muhimmanci ma, ka sa ya faɗi dalilinsa na yin hakan. Ka taimaka masa ya yi tunani a kan Nassosi. Hakan zai sa imaninsa ya kasance bisa ga koyarwar Littafi Mai Tsarki. (Ibran. 5:14) Idan muka yi amfani da tambayoyi da kyau, za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su riƙe gaskiya gam, kuma su kasance da aminci sa’ad da ake tsananta musu ko kuma ake son a rinjaye su. (Kol. 2:6-8) Mene ne kuma zai taimaka mana mu yi aikinmu na bishara da kyau?
ƘWARARRUN MASU BISHARA SUNA TAIMAKA WA JUNA
17, 18. Ta yaya za ka iya taimaka wa wanda kuke wa’azi tare?
17 Yesu ya tuna almajiransa bibbiyu yin wa’azi. (Mar. 6:7; Luk 10:1) Daga baya, manzo Bulus ya yi magana game da ‘abokan aikinsa’ da ‘suka yi aiki tare da shi cikin bishara.’ (Filib. 4:3) A shekara ta 1953, ƙungiyar Jehobah ta soma bin wannan gurbin, ta wajen sa masu shela su koyar da juna.
18 Sa’ad da wanda aka haɗa ka da shi yake wa’azi, ta yaya za ka taimaka masa? (Karanta 1 Korintiyawa 3:6-9.) Ka buɗe kuma ka bi sa’ad da yake karanta Littafi Mai Tsarki. Ka saurara sosai sa’ad da shi ko kuma maigidan yake magana. Hakan zai sa ka iya taimaka masa idan yana bukata. (M. Wa. 4:12) Amma, ka yi hankali don kada ka katse masa magana sa’ad da yake ƙoƙarin ba da bayani da ya dace. Idan ka katse masa magana, za ka iya sa ɗan’uwanka sanyin gwiwa ko kuma ka rikitar da maigidan. Ba laifi ba ne ka ɗan yi magana, amma bayan haka, ka ƙyale shi ya ci gaba.
19. Mene ne ya kamata mu tuna, kuma me ya sa?
19 Ta yaya za ku iya taimaka wa juna sa’ad da kuke wa’azi gida-gida? Ku yi amfani da wannan zarafin wajen tattauna yadda za ku kyautata wa’azinku. Amma, kada ku tattauna abubuwa game da mutanen yankin da za su sa ku sanyin gwiwa. Kuma kada ku tattauna kurakuran ’yan’uwanku da ke ikilisiya. (Mis. 18:24) Ya kamata mu tuna cewa dukanmu ajizai ne. Amma, Jehobah ya nuna mana alheri ta wajen danƙa mana gatan yin wa’azi. (Karanta 2 Korintiyawa 4:1, 7.) Saboda haka, ya kamata dukanmu mu nuna godiya don wannan gatan ta wajen ƙoƙartawa mu yi aikinmu na masu-bishara da kyau.