Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Ka Koya wa Ɗalibanka Yin Nazari
Muhimmancinsa: Idan ɗalibanmu suna so su sami ci gaba, ya kamata su yi nazarin koyarwar Littafi Mai Tsarki masu zurfi, ba masu sauƙi kawai ba. (Ibran. 5:12–6:1) Yin nazari yana bukatar ƙoƙari sosai. Ya ƙunshi haɗa sababbin abubuwan da muke koya yanzu da na dā don mu san yadda za mu yi amfani da su. (Mis. 2:1-6) Idan ɗalibai sun koyi yin bincike da kansu, hakan zai taimaka musu su riƙa yin amfani da littattafanmu don ba da amsa ga tambayoyin da aka musu game da Littafi Mai Tsarki. Idan suka yi iya ƙoƙarinsu don su bi abubuwan da suka koya, hakan zai sa su jimre duk wani gwaji da za su fuskanta a matsayinsu na Kirista.—Luk. 6:47, 48.
Ku Bi Shawarar Nan a Wannan Watan:
A ƙarshen kowane kan magana ko babi, ka sa ɗalibinka ya faɗi abin da ya koya. Idan ba ka da ɗalibi, ka taƙaita wasu abubuwan da ka koya daga Littafi Mai Tsarki ko kuma wani sakin layi na Hasumiyar Tsaro don kada ka manta abin da ka karanta.