Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
6-12 GA FABRAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 47-51
“Yin Biyayya ga Jehobah Yana Kawo Albarka”
ip-2-E 131 sakin layi na 18
Jehobah Yana Koyar da Mu Don Mu Amfana
“Ka Yi Sauraro ga Dokokina!”
18 Da taimakon ruhu mai tsarki, annabin ya ce: “Ubangiji Yahweh ya aiko ni, duk da ruhunsa. Haka nan Ubangiji Mai fansarka, Mai Tsarki na Isra’ila ya faɗi: ‘ni ne Ubangiji Allahnka, Wanda yake koya maka zuwa amfaninka, Wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi.’” (Ishaya 48:16b, 17) Waɗannan kalamai masu kyau da Jehobah ya yi sun nuna cewa yana ƙaunar Isra’ilawa, kuma hakan ya kamata ya tabbatar masu da cewa Jehobah zai cece su daga hannun Babila. Shi ne mai Fansar su. (Ishaya 54:5) Abin da Jehobah yake so shi ne Isra’ilawan su sake kyautata dangantakarsu da shi kuma su riƙa kiyaye dokokinsa. Bauta ta gaskiya ta dangana ne ga bin umurnin Jehobah. Isra’ilawan ba za su iya yin abin da ya kamata ba, saboda haka ana bukatar ‘a koya musu abin da za su yi.’
ip-2-E 131 sakin layi na 19
Jehobah Yana Koyar da Mu Don Mu Amfana
19 Jehobah ya sake yin kalaman da suka nuna cewa yana son mutanensa su daina munanan ayyukan da suke yi kuma su ji daɗin rayuwa. Ya ce: “Da ma ka yi sauraro ga dokokina! da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi, adalcinka kuma kamar raƙuman teku.” (Ishaya 48:18) Babu shakka, waɗannan kalaman sun nuna cewa Mahaliccinmu mai ƙauna ne! (Kubawar Shari’a 5:29; Zabura 81:13) Maimakon Isra’ilawa su je bauta, za su iya morar salama da zai kasance da kyau kamar ruwan teku. (Zabura 119:165) Ayyukansu na adalci za su yi yawa kamar rakuman teku. (Amos 5:24) Da yake Jehobah yana ƙaunar Isra’ilawa, ya nuna musu hanyoyin da za su bi idan har za su ci gaba da yi masa biyayya!
ip-2-E 132 sakin layi na 20-21
Jehobah Yana Koyar da Mu Don Mu Amfana
20 Waɗanne albarka ne Isra’ilawa za su samu idan sun tuba? Jehobah ya ce: “Zuriyarka ta zama kamar yashi, ’ya’yan tsatsonka kuma kamar rairai: da ba a datse sunansa ba, ba a kuwa hallaka shi daga gabana ba.” (Ishaya 48:19) Jehobah ya tuna wa mutanen alkawarin da ya yi wa Ibrahim cewa zuriyarsa za ta yi yawa “kamar taurarin sama, kamar yashi kuma wanda ke a bakin teku.” (Farawa 22:17; 32:12) Amma abin bakin ciki shi ne, wannan zuriyar ta yi rashin biyayya kuma hakan ya sa ba su cancanci ganin cikawar alkawarin ba. A gaskiya sun yi munanan abubuwa sosai kuma a bisa Dokar Jehobah, sun cancanci halaka. (Kubawar Shari’a 28:45) Amma duk da hakan, Jehobah bai halaka mutanensa ba kuma bai yi watsi da su ba.
21 Ƙa’idodin da ke wannan littafin sun shafi bayin Jehobah a yau. Jehobah ne ya halicce mu, kuma shi ne ya fi sanin yadda ya kamata mu bi da rayuwarmu. (Zabura 36:9) Ya kafa mana dokoki don amfanin kanmu ba don ya hana mu jin daɗi ba. Kiristoci na gaskiya suna bin umurnin Jehobah. (Mikah 4:2) Umurninsa suna kāre mu daga dabarun Shaiɗan da kuma abubuwan da za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Idan muna bin ƙa’idodin Jehobah, za mu ga cewa yana koyar da mu don mu amfana. Za mu fahimci cewa “dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” Kuma hakan zai sa mu tsira.—1 Yohanna 2:17; 5:3.
Neman Abubuwa Masu Tamani
it-1-E 643 sakin layi na 4-5
Sakin Aure
Saki na Alama. A Littafi Mai Tsarki, ana yawan amfani da dangantakar da ke tsakanin ma’aurata don a kwatanta wani abu. (Ish 54:1, 5, 6; 62:1-6) Ƙari ga haka, an yi amfani da saki don a kwatanta wani abu.—Jer 3:8.
An ci Yahudawa a yaƙi kuma aka halaka Urushalima a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu. Don haka, an ɗauki Yahudawan zuwa bauta a Babila. Shekaru da yawa kafin hakan ya faru, Jehobah ya yi annabci game da Yahudawan da za su yi bauta a Babila cewa: ‘Ina takardar kisan auren mahaifiyarki, da na sake ta da ita?’ (Ish 50:1) Jehobah ya saki ‘mahaifiyarsu’ ko kuma al’ummar ba don ta ƙarya alkawarinsa ba ne amma saboda mutanen sun ƙi bin Dokarsa. Amma daga baya, wasu Isra’ilawa sun tuba kuma suka roƙi Jehobah da ya maido da dangantakar da ke tsakaninsu kamar yadda yake a dā. Saboda sunansa, Jehobah ya maido da mutanensa ƙasarsu a shekara ta 537 kafin haihuwar Yesu. Hakan ya faru ne bayan sun yi shekara 70 suna zaman bauta.—Za 137:1-9; ka duba AURE.
13-19 GA FABRAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 52-57
Neman Abubuwa Masu Tamani
w06 3/15-E 11 sakin layi na 2
“Misali” da Ke da Muhimmanci a Gare Mu
Mene ne ’yar “kuyanga,” wato Saratu da ɗanta Ishaƙu suke wakiltar? Bulus ya nuna cewa Saratu, wato “bakariyar mata” tana wakiltar sashen ƙungiyar Allah da ke sama. Wannan matar ba ta da “ɗa” a duniya domin babu shafaffu kafin Yesu ya zo duniya. (Galatiyawa 4:27; Ishaya 54:1-6) A Fentakos shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, ruhu mai tsarki ya sauko a kan wasu maza da mata kuma hakan ya sa sun zama kamar ’ya’yan wannan matar. Allah ya ɗauki waɗannan ’ya’yan a matsayin ’ya’yansa don haka su ne za su yi sarauta tare da Yesu a Mulkin Allah. (Romawa 8:15-17) Bulus wanda yake ɗaya daga cikin ’ya’yan ya ce: “Amma Urushalima da ke sama ɗiya ce, watau uwanmu ke nan.”—Galatiyawa 4:26.
20-26 GA FABRAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 58-62
“‘Ku Yi Shelar Shekara ta Alherin’ Jehobah”
ip-2-E 322 sakin layi na 4
Za a Yi Adalci a Sihiyona
“Shekara ta Alherin”
4 Ishaya ya rubuta cewa: “Ruhun Ubangiji Yahweh yana bisa gareni; gama Ubangiji ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga matalauta; ya aike ni domin in warkar da masu-karyayyen zuciya, in yi ma ɗaurarru shela ta sāki, da buɗewar kurkuku ga waɗanda su ke a sarƙa.” (Ishaya 61:1) Su wane ne aka ce su yi shelar bishara? Da farko, Ishaya ne aka gaya wa hakan kuma Allah ya hure shi ya rubuta albishiri ga waɗanda suke zaman bauta a Babila. Amma Yesu ya nuna cewa shi ne zai cika wannan annabcin da Ishaya ya rubuta. (Luka 4:16-21) Hakika, an aika Yesu don ya gaya wa masu tawali’u game da Mulkin Allah kuma don haka ne aka shafe shi da ruhu mai tsarki sa’ad da ya yi baftisma.—Matta 3:16, 17.
ip-2-E 326-327 sakin layi na 13-15
Adalci Ya Yaɗu a Sihiyona
13 Daga shekara ta Fentakos 33, Allah ya dāsa “itatuwa na adalci,” wato Kiristoci shaffafu a cikin “Isra’ila na Allah.” (Galatiyawa 6:16) Da shigewar lokaci, waɗannan ‘itatuwan’ sun ƙaru zuwa 144,000, kuma suna ba da ’ya’ya masu kyau da suke ɗaukaka Allah. (Ru’ya ta Yohanna 14:3) Waɗanda suka rage daga cikin ‘itatuwan’ sun soma ba da ’ya’yansu daga shekara ta 1919 sa’ad da Jehobah ya taimaka musu su soma bauta ta gaskiya. Jehobah ya tanadar musu da abubuwa da yawa kuma hakan ya sa suna ba da ’ya’ya masu kyau sosai.—Ishaya 27:6.
14 Ishaya ya ambata ayyukan da waɗannan ‘itatuwan’ za su yi sa’ad da ya ce: “Za su gina kufaifai na dā, su rayar da kangaye na risɓewa na kwanakin dā, za su gyargyarta kangayen birane, risɓewa ta zamanu da yawa.” (Ishaya 61:4) Sarkin Fasiya mai suna Sairus ya umurci Yahudawan da suka yi zaman bauta a Babila da su je su sake gina Urushalima da kuma haikalin da aka halaka da daɗewa. Wannan zai kuma cika bayan shekara ta 33 da 1919 bayan haihuwar Yesu.
15 A shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, mabiyansa sun yi baƙin ciki sosai domin an kashe shi. (Matta 26:31) Amma, sun sake farin ciki sa’ad da Yesu ya bayyana musu bayan ya tashi daga mutuwa. Kuma da aka saukar musu da ruhu mai tsarki, sai suka soma wa’azin bishara da ƙwazo a “cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.” (Ayyukan Manzanni 1:8) Da haka, sun soma dawowa da bauta ta gaskiya. Hakazalika, daga shekara ta 1919, Yesu ya sa shafaffu da suka rage a duniya su sake gina wuraren da aka rushe tun “zamanu da yawa.” Limaman Kiristendom sun daɗe suna koya wa mutane al’adun mutane da kuma koyarwar ƙarya maimakon ƙa’idodin Jehobah. Kiristoci shafaffu sun tsabtacce ikilisiyoyi daga koyarwar addinan ƙarya domin a riƙa bauta wa Jehobah. Kuma sun soma wa’azin da ba a taɓa yin irinsa ba a duk duniya.—Markus 13:10.
27 GA FABRAIRU–5 GA MARIS
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 63-66
“Sababbin Sammai da Sabuwar Duniya Za Su Sa Mu Murna Sosai”
ip-2-E 383 sakin layi na 23
“Ku Yi Farin ciki Har Abada da Abin da Nake Halittawa”
23 A cikin littafin Ru’ya ta Yohanna, manzo Yohanna ya bayyana wani wahayin da ya gani game da ranar Jehobah, wato lokacin da za a halaka mugayen mutane. Kuma aka saka Shaiɗan a cikin rami marar matuƙa. (Ru’ya ta Yohanna 19:11–20:3) Bayan Yohanna ya faɗa hakan, sai ya ambata kalaman Ishaya cewa: “Na ga sabuwar sama da sabuwar duniya kuma.” Wannan wahayi ya nuna lokacin da Jehobah Allah zai mai da duniyar nan aljanna. (Ru’ya ta Yohanna 21:1, 3-5) Don haka, annabcin da Ishaya ya yi game da “sababbin sammai da sabuwar duniya” za su cika! A ƙarƙashin Mulkin Allah, mutane za su ji daɗin rayuwa kuma su zauna lafiya a aljanna. Shi ya sa kalaman nan suke da ban ƙarfafa: “Ba za a tuna da al’amura na dā [wato, cuttutuka da wahala da dai sauransu] ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.” Duk abubuwan da za mu riƙa tunawa a lokacin ba abubuwan da za su ɓata mana rai ko kuma sa mu baƙin ciki ba ne.
ip-2-E 384 sakin layi na 25
“Ku Yi Farin ciki Har Abada da Abin da Nake Halittawa”
25 Ko a yau ma, Jehobah yana sa Urushalima “murna.” Ta yaya? Kamar yadda muka sani, an yi sabuwar sammai a shekara ta 1914 kuma wannan samman za su ƙunshi mutane guda 144,000 da za su yi sarauta da Yesu a Mulkin Allah. An kwatanta su da “Sabuwar Urushalima.” (Ru’ya ta Yohanna 21:2) Allah yana magana ne game da wannan Sabuwar Urushalima sa’ad da ya ce: “Na halitta Urushalima abin murna, mutanenta kuma abin farin ciki.” Allah zai yi amfani da wannan Sabuwar Urushalima don ya albarkaci mutane masu aminci. Ba za a ƙara jin kuka ba domin Jehobah zai ‘biya mana muradin zuciyarmu.’—Zabura 37:3, 4.