Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
6-12 GA MARIS
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 1-4
“Ina Tare da Kai Domin In Cece Ka”
jr-E 88 sakin layi na 14-15
KA ƘARFAFA WAƊANDA SUKA KARAYA
14 Ya kamata mu lura da yadda aka ƙarfafa Irmiya da kuma yadda shi ma ya ƙarfafa “waɗanda suka gaji.” (Irm. 31:25) Jehobah ne musamman ya ƙarfafa wannan annabin. Ka yi tunanin yadda za ka ji sa’ad da Jehobah ya ce maka: “Ga shi, yau na maishe ka birni mai-ganuwa, . . . Za su yi yaƙi da kai; amma ba za su yi nasara da kai ba: gama ina tare da kai, in ji Ubangiji, domin in cece ka.” (Irm. 1:18, 19) Don haka, Irmiya yana da dalilai da yawa da suka sa ya ce Jehobah shi ne “ƙarfina, kagarata, mabọyata cikin ranar wahala.”—Irm. 16:19
15 Abin ban ƙarfafa ne da Jehobah ya gaya wa Irmiya cewa: “Ina tare da kai.” Shin ka lura da abin da ya kamata ka yi sa’ad da wani yake bukatar ƙarfafa? Da akwai bambanci tsakanin sanin cewa wani ɗan’uwa ko wata ’yar’uwa tana cikin matsala da kuma taimakawa sa’ad da wani yake cikin matsala. A yawancin lokaci, kasancewa tare da wanda yake fama da baƙin ciki kamar yadda Allah ya yi wa Irmiya ne ya fi dacewa. Bayan haka, kana iya faɗin kalaman da za su ƙarfafa shi amma kada ka cika shi da surutu. Kalmomi kaɗan masu daɗin ji suna ƙarfafa mutum sosai. Ba ka bukatar ka yi dogon jawabi. Ka yi amfani da kalmomi masu sauƙi da za su nuna cewa ka damu da mutumin sosai. Irin waɗannan kalaman suna da kyau sosai.—Karanta Misalai 25:11.
13-19 GA MARIS
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 5-7
w88 11/1 9-10 sakin layi na 7-8
Irmiya—Annabin da Ya Yi Shelar Hukuncin da Allah Zai Yi
7 Jehobah ya gaya wa Irmiya cewa: “Za su yi yaƙi da kai amma ba za su yi nasara da kai ba.” (Irmiya 1:19) Me ya sa Yahudawa da kuma mahukunta suke so su kashe Irmiya? Domin yana wa’azi ne game da irin hali marar kyau da suke da shi da kuma bautar ƙarya da suke yi. Amma Irmiya bai ji tsoro ba, ya ce: “Ga shi kuwa, har maganar Ubangiji ta zama abin zargi a garesu: ba su ji daɗinta ba ko kaɗan. Gama tun daga ƙaraminsu har zuwa babbansu dukansu sun ba da kansu ga sha’awa: tun daga annabi kuma har zuwa firist, kowane ɗayansu yana aikin ƙarya.”—Irmiya 6:10, 13.
8 A gaskiya, suna yin ayyuka ta ibada kamar miƙa haɗayu da dai sauran su, amma ba sa yin hakan da zuciya ɗaya. Sun fi mai da hankali ga miƙa haɗayu maimakon kyautata dangantakarsu da Jehobah. Ƙari ga haka, malaman addinin Yahudawa suna ruɗin al’ummar ta wajen cewa: “Lafiya, Lafiya,” alhali hakan ƙarya ce. (Irmiya 6:14; 8:11) Sun faɗin hakan ne don su sa mutanen su ji cewa suna da dangantaka mai kyau da Allah. Suna ganin cewa su mutanen Allah ne kuma suna zama a birninsa mai tsarki da kuma yin ibada a haikalinsa, don haka ba su da damuwa. Amma, shin haka ne Jehobah yake ɗaukan lamarin?
w88 11/1 10 sakin layi na 9-10
Irmiya—Annabin da Ya Yi Shelar Hukuncin da Allah Zai Yi
9 Jehobah ya gaya wa Irmiya ya je ya saya a baƙin ƙofar hankalin, inda mutanen da suke shiga za su gan shi don ya gaya musu saƙonsa. Yana bukatar ya gaya musu cewa: “Kada ku dogara ga maganar ƙarya, cewa, Haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji ke nan!’ . . . marasa amfani.” Yahudawan suna yin abubuwa don ganin ido ba don bangaskiya ba. Sun manta da kalaman Jehobah cewa: “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce; wane irin gida fa za ku gina mani?” Tabbas, ko da yaya girman haikalin da suka gina yake, Jehobah Mahaliccin sama da ƙasa ba ya cikin hankalin!—Irmiya 7:1-8; Ishaya 66:1.
10 Irmiya ya ci gaba da gaya musu sakonsa: ‘Za ku yi sata, da kisankai, ku yi zina, ku yi rantsuwa da ƙarya, ku ƙona turare ga Baal, ku bi waɗansu allohi waɗanda ba ku san su ba, . . . sa’an nan ku ce, “Za a cece mu,” don kawai ku ci gaba da yin dukan waɗannan abubuwan ban ƙyama?’ A matsayinsu na mutanen Allah, Yahudawan suna ganin cewa Allah ba zai damu da halayensu marasa kyau ba muddin suna miƙa haɗayu a haikali. Amma idan har suna tsamamin Jehobah yana kama da uban da yake goyan bayan ɗansa da ya lalace, to ruɗin kansu suke yi.—Irmiya 7:9, 10, Littafi Mai Tsarki; Fitowa 19:5, 6.
jr-E 21 sakin layi na 12
Bauta wa Jehobah a “Cikin Kwanaki Na Ƙarshe”
12 A farkon shekarar mulkin Jehoiakim, Jehobah ya gaya wa Irmiya ya je haikali kuma ya tsauta wa Yahuwada don ayyukan mugunta da suke yi. Suna ganin cewa haikalin Jehobah ne zai kāre su. Amma idan har ba za su daina ‘yin sata, da kisankai, da zina, da rantsuwa da ƙarya, da ƙona turare ga Baal, da kuma bin waɗansu allohi waɗanda ba su san su ba,’ Jehobah ba zai amince da haɗayar da suke yi a haikalin ba. Hakazalika, zai rabu da mutanen da suke bauta a wajen kamar yadda ya rabu da mazaunin da ke Shiloh a zamanin Eli Babban Firist. Kuma ƙasar Yahuda “za ta zama kango.” (Irm. 7:1-15, 34; 26:1-6) Babu shakka, Irmiya yana bukatar ƙarfin zuciya kafin ya iya gaya wa mutane irin wannan saƙon! Wataƙila ya faɗi wannan saƙon a gaban jama’a da masu kuɗi da kuma mutane masu iko sosai. Ko a yau ma, ba ya yi wa wasu ’yan’uwa sauƙi su yi wa’azi a inda jama’a suke ko ga masu kuɗi ko kuma mutanen da ke da babban matsayi. Amma muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Allah zai taimaka mana kamar yadda ya yi wa Irmiya.—Ibran. 10:39; 13:6.
Neman Abubuwa Masu Tamani
w88 11/1 11 sakin layi na 15
An Hukunta Yahudawa
15 A wajen shekara ta 632 kafin haihuwar Yesu, mutanen Kaldiyawa da kuma Madiya sun ci Assuriya a yaƙi kuma Masar da ke kudancin Yahuda ba ta da iko kamar dā. Ainihin mutanen da za su kai wa Yahudawa hari za su zo daga arewa. Shi ya sa Irmiya ya gaya wa Yahudawa magana marar daɗin ji. Ya ce: “Ga shi, wata al’umma tana zuwa daga ƙasar arewa . . . masu-zafin rai ne. . . . kamar mutum da za ya shiga yaƙi, shi yi yaƙi da ke, ya ɗiyar Sihiyona.” A lokacin, Babila ce take da iko sosai. Wannan ƙasar ce Allah zai yi amfani da ita don ya hukunta Yahudawa.—Irmiya 6:22, 23; 25:8, 9.
20-26 GA MARIS
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 8-11
it-1-E 555
Gurji
Ana saka katanga ko kuma wani abu da aka ƙera kamar mutum a cikin gona don a tsorata dabbobi. Kuma annabi Irmiya ya yi amfani da wannan misali na “umudi a gonar” gurji don ya kwatanta irin bautar gumaka da al’ummar take yi.—Irm. 10:5.
27 GA MARIS–2 GA AFRILU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 12-16
jr-E 51 sakin layi na 17
Kada Ka Bar Zuciyarka Ta Yaudare Ka
17 Irmiya yana bukatar ya bi ja-gorancin Allah a aikin da aka ba shi. Idan kai Irmiya ne, shin za ka bi dukan umurnin da aka ba ka? Akwai lokacin da Jehobah ya gaya wa Irmiya ya tsayi ɗamara ta linen kuma ya ɗaura a jikinsa. Bayan haka, sai Allah ya ce masa ya je kogin Yufiretis. Idan ka duba taswira, za ka ga cewa wannan tafiya za ta kai wajen mil 300 (kilomita 500). Irmiya yana bukatar ya ɓoye wannan ɗamara a cikin dutse sa’an nan ya koma Urushalima. Bayan an jima, sai Allah ya sake gaya masa ya koma ya ɗauko ɗamarar. (Karanta Irmiya 13:1-9.) Tafiyar gabaki ɗaya za ta kai wajen mil 1,200 (kilomita 1,900). Masu sūkar Littafi Mai Tsarki ba su yarda cewa Irmiya zai iya yin wannan tafiyar da ƙafa ba. (Ezra 7:9) Amma duk da haka, abin da Irmiya ya yi shi ne abin da Allah ya umurce shi ya yi.
jr-E 52 sakin layi na 18
Kada Ka Bar Zuciyarka Ta Yaudare Ka
18 Ka ɗauka cewa kana ganin Irmiya yana takawa da ƙafa daga Yahuda har zuwa kogin Yufiretis. Yana wannan tafiyar ne don kawai ya je ya ɓoye ɗamara ta linen! Wataƙila maƙwabtansa za su ta yin mamakin inda ya je. Kuma da Irmiya ya tashi dawowa, bai dawo da ɗamara ta linen ɗin ba. Sai Allah ya gaya masa cewa ya sake yin wannan tafiya don ya ɗauko ɗamarar da wataƙila ta riga ta lalace. Irmiya zai iya yin tunanin cewa: ‘Ya isa haka, babu amfanin yin hakan.’ Amma Irmiya bai yin hakan ba. Ya bi umurnin Allah ba tare da yin gunaguni ba!
jr-E 52 sakin layi na 19-20
Kada Ka Bar Zuciyarka Ta Yaudare Ka
19 Sa’ad da Irmiya ya sake koma wa Yufiretis ne Jehobah ya gaya masa dalilin da ya sa ya ba shi wannan aikin. Halin da Irmiya ya nuna ya sa ya sami damar gaya wa mutanen saƙon Allah cewa: “Wannan muguwar jama’a, wadda ta ƙi jin maganata, wadda ta taurare, ta bi son zuciyarta, ta kuma bi gumaka ta bauta musu, ta yi musu sujada, za ta zama kamar abin ɗamaran nan, wanda ba shi da sauran amfani.” (Jer. 13:10, LMT) Hakika, Jehobah ya yi amfani da kwatanci mai kyau don ya koya wa mutanensa darasi! Irmiya ya yi wa Jehobah biyayya da dukan zuciyarsa duk da cewa hakan ba shi da sauƙi kuma abin da ya yi ya sa ya iya ratsa zuciyar mutanen.—Irm. 13:11.
20 Ko da yake ba a umurci Kiristoci a yau su yi tafiya irin wanda Irmiya ya yi ba. Amma wataƙila zaɓin da kake yi a matsayinka na Kirista zai iya sa mutane ko abokanka su yi mamaki ko kuma su riƙa sūkar ka. Hakan yana iya ƙunshi irin kayan da kake sakawa ko zaɓinka game da ilimi ko aikin da za ka yi ko kuma ra’ayinka game da shan giya. Shin za ka bi umurnan Allah kamar yadda Irmiya ya yi? Bin umurnan Allah zai ba ka damar yi wa mutane wa’azi. Ƙari ga haka, za ka amfana sosai idan kana bin ƙa’idodin da ke Littafi Mai Tsarki da kuma ja-gorancin bawan nan mai aminci. Maimakon ka bar zuciyarka ta yaudare ka, ka bi misalin Irmiya. Ka amince da gyarar Jehobah kuma ka bar shi ya yi amfani da kai wajen aikata nufinsa.
it-1-E 1121 sakin layi na 2
Ƙugu
Jehobah ya kwatanta al’ummar Isra’ila da kuma Yahuda a matsayin ɗamara da ke ƙugunsa. Kuma ya riƙe su sosai a jikinsa don su kawo ɗaukaka ga sunansa. (Irm. 13:11) An annabta cewa Yesu Kristi zai yi sarauta cikin adalci da kuma aminci kamar ɗamara da ke ƙugunsa. Hakan ya nuna cewa Yesu zai yi adalci da aminci a cikin dukan abubuwan da zai yi. Kamar yadda ɗamara take riƙe riga, hakan nan wannan halin zai taimaka masa ya yi shari’a yadda ya kamata a matsayinsa na Alƙalin da Jehobah ya naɗa.—Isha. 11:1, 5.
Neman Abubuwa Masu Tamani
jr-E 118 sakin layi na 11
Shin Kana Tambaya “Ina Jehobah?” a Kullum
11 Sa’ad da Irmiya ya ga mugayen mutane suna samu nasara a rayuwarsu, hakan ya sa shi fushi kuma ya yi wa Jehobah tambayoyi. (Karanta Irmiya 12:1, 3.) Irmiya bai ce Jehobah ba mai adalci ba ne, amma ya yi tambaya ne don ya samu amsa ga “da’awarsa.” Kuma hakan ya nuna cewa yana da dangantaka ta kud da kud da Jehobah kamar yadda ɗa da mahaifinsa suke. Irmiya yana mamakin yadda Yahudawa suke jin daɗin rayuwa duk da muguntar da suke yi. Shin Jehobah ya amsa tambayar Irmiya kuwa? Jehobah ya tabbatar masa da cewa zai halaka mugayen mutane. (Irm. 12:14) Da Irmiya ya ga abin da ya faru a ƙarshe, hakan ya ƙara sa ya tabbata da shari’ar Allah. Kuma hakan ya ƙara ba shi damar gaya wa Ubansa Allah abin da yake damunsa.