DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 22-23
Ku Riƙa Bin Umurnin Dokoki Biyu Mafi Girma
Ka yi amfani da littafin Matta 22:36-39, sai ka jera dalilai da ke gaba da suke sa muke halartar taro bisa ga muhimmancinsu:
- Don ka sami ƙarfafa 
- Don ka ƙarfafa ’yan’uwa 
- Don mu bauta wa Jehobah kuma mu nuna masa ƙaunarmu 
Me ya sa ya kamata mu je taro ko da mun gaji sosai ko kuma muna ganin ba za mu amfana a taron ba?
A waɗanne hanyoyi ne kuma za mu iya nuna cewa muna bin umurnin da ke dokoki biyu mafi girma?