12-18 ga Maris
MATTA 22-23
- Waƙa ta 30 da Addu’a 
- Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan) 
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
- “Ku Riƙa Bin Umurnin Dokoki Biyu Mafi Girma”: (minti 10) - Mt 22:36-38—Ta yaya wannan ayar ta bayyana abin da doka ta farko mafi girma ta ƙunsa? (nwtsty na nazarin Mt 22:37) 
- Mt 22:39—Mece ce doka ta biyu mafi girma? (nwtsty na nazari) 
- Mt 22:40—Abubuwan da aka rubuta a duka littattafan Ibrananci game da ƙauna ne (nwtsty na nazari) 
 
- Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8) - Mt 22:21—Mene ne “abin da ke na Kaisar,” da kuma “abin da ke na Allah”? (nwtsty na nazari) 
- Mt 23:24—Mene ne Yesu yake nufi a ayar nan? (nwtsty na nazari) 
- Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah? 
- Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon? 
 
- Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mt 22:1-22 
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
- Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi. 
- Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi. 
- Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) bhs 199 sakin layi na 8-9—Mai shelar ya ƙarfafa ɗalibin ya gayyaci mutanen da ya sani zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu. 
RAYUWAR KIRISTA
- “Ta Yaya Za Ka Ƙaunaci Allah da Kuma Maƙwabtanka?”: (minti 15) Tattaunawa. Don ka nuna muhimmancin yin tunani a kan labaran Littafi Mai Tsarki, ka saka bidiyon nan Jehobah Ne Kaɗai Allah Na Gaskiya—Taƙaitawa. Ka gaya wa ’yan’uwa su bi karatun a littafin 1 Sarakuna 18:17-46. 
- Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 5 sakin layi na 1-6 da akwatin da ke shafi na 52 da 55 
- Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3) 
- Waƙa ta 52 da Addu’a