Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
4-10 GA MAYU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 36-37
“An Wulaƙanta Yusuf Saboda Kishi”
(Farawa 37:3, 4) Isra’ila kuwa yana ƙaunar Yusuf fiye da sauran ’ya’yansa maza, gama an haifi Yusuf a tsufarsa. Isra’ila ya yi wa Yusuf riga mai ado. 4 Amma da ’yan’uwansa suka lura cewa babansu ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowannensu, sai suka ƙi ganin Yusuf. Ba sa yi masa maganar alheri.
w14-E 8/1 12-13
“Ku Ji Wannan Mafarkin”
Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar cewa: “Amma da ’yan’uwansa suka lura cewa babansu ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowannensu, sai suka ƙi ganin Yusuf. Ba sa yi masa maganar alheri.” (Farawa 37:4) Mun san cewa idan mahaifi yana ƙaunar ɗaya daga cikin yaransa fiye da sauran, hakan zai iya jawo kishi. Amma sun yi kuskure da suka ji kishin ɗan’uwansu domin kishi yana da lahani sosai. (Karin Magana 14:30; 27:4) Ka taɓa kishin wani don ya samu wani abin da kake zaton za ka samu? Ka tuna cewa kishi ya sa ’yan’uwan Yusuf sun yi abin da ya sa su da-na-sani daga baya. Labarinsu ya nuna ma Kiristoci cewa, ya fi kyau su “yi farin ciki tare da masu farin ciki.”—Romawa 12:15.
Ba shakka, Yusuf ya san cewa ’yan’uwansa suna gāba da shi. Shin hakan ya sa ya ƙi saka riga mai kyau da babansa ya saya masa don kar ’yan’uwansa su gani? Wataƙila zuciyarsa ta gaya masa ya yi hakan. Amma ka tuna cewa babansa ya saya masa rigar ne don ya nuna cewa yana ƙaunarsa kuma ya amince da shi. Yusuf ya saka rigar don ya faranta ran babansa. Za mu iya koyan darasi daga wurinsa. Ko da yake Ubanmu na sama ba ya nuna bambanci, amma a wasu lokuta yakan zaɓi bayinsa masu aminci kuma ya albarkace su. Ban da haka ma, yana so halayensu su yi dabam da na mutanen duniya. Kamar riga mai kyau na Yusuf, halayen Kiristoci na gaskiya ne suke bambanta su da mutanen duniya. A wasu lokuta, halayenmu masu kyau suna sa mutane su yi kishinmu da kuma gāba da mu. (1 Bitrus 4:4) Ya kamata Kirista ya ji tsoro ko kunyar gaya wa mutane cewa shi bawan Allah ne? Babu. Kamar yadda Yusuf bai ƙi saka rigarsa mai kyau ba, mu ma bai kamata mu ji tsoro ko kunyar gaya wa mutane cewa mu bayin Allah ne ba.—Luka 11:33.
(Farawa 37:5-9) Wata rana Yusuf ya yi mafarki, amma sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, sai suka ƙara ƙinsa. 6 Ya ce musu, “Ku ji wannan mafarkin da na yi. 7 Muna ɗaura damman dawa a gona, sai ga shi damina ya tashi ya miƙe a tsaye. Sai ga naku damman sun taru kewaye da nawa, suka rusuna wa damina.” 8 ’Yan’uwansa suka ce, “Kana nufi za ka zama sarki a bisanmu? Ko kuwa za ka yi mulki a kanmu?” Sai suka ƙara ƙinsa saboda mafarkansa da kuma maganganunsa. 9 Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce musu, “Ga shi, na sāke yin wani mafarki. Na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
(Farawa 37:11) ’Yan’uwan Yusuf suka yi kishinsa, amma baban ya ɓoye zancen a zuciyarsa.
w14-E 8/1 13 sakin layi na 2-4
“Ku Ji Wannan Mafarkin”
Jehobah ne ya sa ya yi mafarkin. Mafarkan annabci ne kuma Jehobah yana so Yusuf ya gaya wa mutane saƙon da ke ciki. Ma’ana, Jehobah yana so Yusuf ya yi annabci kamar yadda sauran annabawa suka annabta saƙonnin huƙuncin Jehobah ga mutanensa marasa biyayya.
Cikin basira Yusuf ya ce ma ’yan’uwansa: “Ku ji wannan mafarkin da na yi.” ’Yan’uwansa sun gane ma’anar mafarkin kuma ba su ji daɗin hakan ba ko kaɗan. Sun ce masa: “Kana nufi za ka zama sarki a bisanmu?” Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa: “Sai suka ƙara ƙinsa saboda mafarkansa da kuma maganganunsa.” Da Yusuf ya sake yin mafarki, ya gaya wa mahaifinsa da ’yan’uwansa kuma hakan ya daɗa ba su haushi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babansa ya tsawata masa ya ce, ‘Wane irin mafarki ke nan ka yi? Kana nufin ni da mamarka da ’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka da fuskokinmu har ƙasa?’ ” Amma Yakub ya ci gaba da tunani a kan mafarkin. Mai yiwuwa yana cewa, anya ba Jehobah ne yake magana da yaron ba?—Farawa 37:6, 8, 10, 11.
Ba Yusuf ne bawan Jehobah na farko ko na ƙarshe da aka ce ya idar da saƙo da ya sa mutane fushi kuma ya sa aka tsananta masa ba. Saƙon da Yesu ya idar ne ya fi sa mutane fushi, shi ya sa ya gaya wa mabiyansa: “In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku.” (Yohanna 15:20) Dukan Kiristoci za su iya koyan darussa daga bangaskiya da kuma ƙarfin zuciyar Yusuf.
(Farawa 37:23, 24) Sa’ad da Yusuf ya kai wurin ’yan’uwansa, suka tuɓe rigarsa, wannan riga mai ado wadda ya sa. 24 Sai suka ɗauke shi suka jefa shi a cikin wata rijiya marar ruwa.
(Farawa 37:28) Da Ishma’ilawa daga Midiyan, wato ’yan kasuwa suka zo wucewa, sai ’yan’uwan Yusuf suka fitar da shi daga rijiyar. Suka sayar da shi ga Ishma’ilawan nan a kan kuɗin azurfa ashirin. Aka ɗauke shi zuwa Masar.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Farawa 36:1) Ga tarihin zuriyar Isuwa, wato Edom.
it-1-E 678
Edom
(Edom) [Ja], Edomawa.
Edom wani suna ne da aka ba wa Isuwa ɗan biyun Yakub. (Fa 36:1) An ba shi sunan ne domin ya sayar da matsayinsa na ɗan fari a kan jan fate. (Fa 25:30-34) Kuma fatar Isuwa ja ce sa’ad da aka haife shi (Fa 25:25). Ban da haka ma, ƙasa da duwatsu da suke wasu wuraren da shi da zuriyarsa suka gada daga baya, suna da jar kala.
(Farawa 37:29-32) Lokacin da Ruben ya dawo wurin rijiyar ya ga babu Yusuf, sai ya yayyage rigunansa domin baƙin ciki. 30 Ya koma wurin ’yan’uwansa ya ce musu, “Yaron ba ya nan. Ni kuma, me zan yi?” 31 Sai suka ɗauki rigar Yusuf suka kashe akuya, suka tsoma rigar a cikin jinin. 32 Suka kawo riga mai ado da jinin a kai wurin babansu, suka ce, “Mun sami wannan, duba, ko rigar ɗanka ne ko babu.”
it-1-E 561-562
Mai Riƙo
Idan makiyayi ya amince zai yi riƙon garke, hakan yana nufin cewa zai kula da kuma kiyaye dabbobin. Ban da haka ma, yana tabbatar wa mai garken cewa zai ciyar da su kuma idan aka sace su, zai biya. Amma hakan ba ya nufin cewa a kowane yanayi ne za a ɗora masa laifi, alal misali dokar ta ce idan naman daji ne ya cinye ɗaya daga cikin dabbobin, ba za a kama shi da laifi ba. Don kada a kama shi da laifi, yana bukatar ya kawo matacce ko kuma ƙasusuwan dabbar don ya nuna cewa naman daji ne ya cinye shi. Bayan mai dabbar ya bincika abin da makiyayin ya kawo, sai ya amince cewa makiyayin bai da laifi.
Haka ma yake da kowane abin da aka ba wa mutum riƙo. Alal misali, a iyali ɗan fari ne ake ba wa riƙon ƙannensa. Ba mamaki shi ya sa Ruben ɗan farin Yakub ya ƙi sa’ad da ’yan’uwansa suke so su kashe ƙaninsu Yusuf kamar yadda aka nuna a Farawa 37:18-30. “Ya ce musu, ‘Kada mu kashe shi.’ . . . ‘Kada mu zub da jini. . . . ko kaɗan kada hannunku ya taɓa shi.’ Ya yi haka da nufi ya juya ya fitar da Yusuf, ya mayar da shi wurin babansa.” Amma da Ruben ya dawo don ya cire Yusuf kuma bai gan sa a rijiyar ba, ya yi baƙin ciki sosai kuma “ya yayyage rigunansa” kuma ya ce: “Yaron ba ya nan. Ni kuma, me zan yi?” Ya san cewa shi ne za a kama da alhakin jinin Yusuf. Don ya guje hakan, shi ya sa suka haɗa baƙi da ’yan’uwansa su gaya wa mahaifinsu cewa naman daji ne ya cinye Yusuf. Sai suka shafa wa rigar Yusuf jinin akuya don ya zama shaida. Da suka nuna wa babansu Yakub, sai ya ɗauka cewa naman daji ne ya cinye Yusuf kuma bai ɗora alhakin mutuwar Yusuf a kan Ruben ba.—Fa 37:31-33.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Farawa 36:1-19) Ga tarihin zuriyar Isuwa, wato Edom. 2 Isuwa ya ɗauki matansa daga ’yan matan Kan’aniyawa. Su ne Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana ɗan Zibeyon mutumin Hiwi, 3 da Basemat ’yar Ishma’il, ’yar’uwar Nebaiyot. 4 Ada kuwa ta haifa wa Isuwa Elifaz. Basemat ta haifa masa Reyuwel. 5 Oholibama ita ma ta haifa masa Yewush, da Yalam, da Kora. Waɗannan ne ’ya’ya maza na Isuwa waɗanda an haifa masa a ƙasar Kan’ana. 6 Sa’an nan Isuwa ya ɗauki matansa, da ’ya’yansa maza da mata, tare da dukan mutanen gidansa, da kuma shanunsa da dukan kayansa da ya samu a Kan’ana, sai ya tafi wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yakub. 7 Gama dabbobinsu sun yi yawa yadda ba sa iya zama tare. Ƙasar ba za ta ishe su ba saboda yawan shanunsu da garkunansu. 8 Saboda haka Isuwa ya zauna a yankin tuddai na Seyir. Isuwa ne ake kira Edom. 9 Ga tarihin zuriyar Isuwa kakan Edomawa a yankin tuddai na Seyir. 10 Waɗannan ne sunayen ’ya’ya maza na Isuwa, Elifaz ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa. 11 ’Ya’ya maza na Elifaz su ne Teman, da Omar, da Zefo, da Gatam, da Kenaz. 12 Elifaz ɗan Isuwa yana da wata macen da ya ajiye mai suna Timna wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan ne ’ya’ya maza na Ada matar Isuwa. 13 ’Ya’ya maza na Reyuwel su ne Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza. Waɗannan ne ’ya’ya maza na Basemat matar Isuwa. 14 ’Ya’ya maza na matar Isuwa, wato Oholibama, ’yar Ana ɗan Zibeyon su ne Yewush, da Yalam, da Kora. 15 Waɗannan su ne sarakuna na zuriyar Isuwa, ’ya’ya maza na Elifaz ɗan farin Isuwa su ne Teman, da Omar, da Zefo, da Kenaz, 16 da Kora, da Gatam, da kuma Amalek. Waɗannan ne dangogin Elifaz a ƙasar Edom, zuriyar Ada matar Isuwa. 17 ’Ya’ya maza na dangin Reyuwel ɗan Isuwa su ne Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza. Waɗannan ne dangogin Reyuwel a ƙasar Edom, zuriyar Basemat matar Isuwa. 18 ’Ya’ya maza na Oholibama matar Isuwa su ne Yewush, da Yalam, da Kora. Waɗannan ne dangogin matar Isuwa, wato Oholibama ’yar Ana. 19 Waɗannan ne dangogi da sarakuna na Isuwa, wato Edom.
11-17 GA MAYU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 38-39
“Jehobah Bai Bar Yusuf Ba”
(Farawa 39:1) Aka kuwa gangara da Yusuf zuwa Masar. Sai Fotifar mutumin Masar, shugaban ’yan gadin Sarki Fir’auna, ya saye shi daga hannun Ishma’ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can.
w14-E 11/1 12 sakin layi na 4-5
“Don Me Zan Yi Wannan Babbar Mugunta?”
“Aka kuwa gangara da Yusuf zuwa Masar. Sai Fotifar mutumin Masar, shugaban ’yan gadin Sarki Fir’auna, ya saye shi daga hannun Ishma’ilawa, waɗanda suka gangaro da shi zuwa can.” (Farawa 39:1) Wannan furucin da Littafi Mai Tsarki ya yi ya nuna mana irin wulaƙancin da matashin nan ya sha sa’ad da aka sayar da shi sau biyu kamar kaya. Ka yi tunanin yadda Yusuf yake bin maigidansa, wato shugaban ’yan gadin Sarki Fir’auna na Masar kuma suka bi cikin birnin da ke da manyan shaguna yayin da suke zuwa gidan Fotifar wurin da Yusuf zai yi aiki.
Wurin da Yusuf yake zama yanzu yana da nisa sosai daga garinsu. Shi da iyalinsa makiyaya ne da ke ƙaura wurare dabam-dabam suna kiwon tumaki kuma suna zama a tenti. Amma yanzu yana zama ne a babban gidan Fotifar da aka fenta da kyau. Masu tonon ƙasa sun ce an san Masarawa da gina manyan wuraren hutu mai katanga da ke da lambuna da itatuwa da kuma wurin iyo don jin daɗi. Wasu gidajen suna da lambuna da wurin shan iska da manyan wundo da daƙuna da yawa. Ban da haka ma, suna da babban dakin cin abinci da kuma wurin kwana na bayi.
(Farawa 39:12-14) sai ta kama rigarsa, tana cewa, “Ka kwana da ni.” Sai ya bar mata rigar a hannunta, ya gudu waje. 13 Da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita waje, 14 sai ta yi ta ihu, ta kira mutanen gidan, ta ce musu, “Ku duba ku gani, mijina ya kawo mana ɗan Ibraniyawa, ga shi yana cin mutuncinmu! Ya zo wurina domin ya kwana da ni, sai na yi ihu da ƙarfi.
(Farawa 39:20) Sai maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya jefa shi a kurkuku inda ake kulle ’yan kurkukun sarki. Yusuf ya zauna a kurkukun.
w14-E 11/1 14-15
“Don Me Zan Yi Wannan Babbar Mugunta?”
Ba mu da cikakken bayani game da yadda kurkukun Masarawa na dā suke. Amma masu tonon ƙasa sun gano wasu abubuwa da suka nuna cewa suna da manyan kurkuku da ke da daƙuna da yawa. Daga baya, Yusuf ya kwatanta wurin da rami, wanda yake nuna cewa wurin na da duhu kuma wanda yake wurin bai da begen kome. (Farawa 40:15) Littafin Zabura ya ƙara nuna mana irin wulaƙancin da aka yi ma Yusuf, wurin ya ce: “Ƙafafunsa suka yi rauni saboda an ɗaure su da sarka, Aka kuma sa wa wuyansa ƙuƙumi na baƙin ƙarfe.” (Zabura 105:17, 18, Littafi Mai Tsarki) A wasu lokuta Masarawa sukan ɗaure hannayen fursunoni ta baya, wasu kuma sukan saka musu ƙarafuna a wuyansu. Babu shakka, Yusuf ya sha wahala sosai ko da yake bai yi wani laifi ba.
Yusuf ya jima sosai a fursuna kuma ya sha wahala. Labarin ya nuna cewa “Yusuf ya zauna a kurkukun.” Kuma Yusuf bai san cewa wata rana za a sake shi ba. Bayan Yusuf ya jima a kurkuku, me ya taimaka masa kada ya karaya?
Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar. Ya ce: “Yahweh ya kasance tare da shi. Ya nuna masa ƙaunarsa.” (Farawa 39:21) Hakan ya koya mana cewa babu katangar fursuna ko sarka ko kuma duhu da zai hana Jehobah ƙaunar bayinsa. (Romawa 8:38, 39) Ka yi tunanin irin addu’ar da Yusuf ya yi wa Ubansa na sama kuma ya sami ta’aziya da kwanciyar hankalin da “Allah wanda yake yi mana kowace irin ta’aziyya” yake ba mu. (2 Korintiyawa 1:3, 4; Filibiyawa 4:6, 7) Me kuma Jehobah ya yi ma Yusuf? Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “ya ba shi farin jini a idon shugaban masu gadin ’yan kurkukun.”
(Farawa 39:21-23) Amma Yahweh ya kasance tare da shi. Ya nuna masa ƙaunarsa, ya ba shi farin jini a idon shugaban masu gadin ’yan kurkukun. 22 Sai shugaban masu gadin ’yan kurkukun ya danƙa wa Yusuf sauran ’yan kurkukun a hannu. Duk abin da za a yi a wurin, Yusuf ne yake yi musu jagora. 23 Shugaban masu gadin ’yan kurkukun, bai damu ba a kan abubuwan da suke a ƙarƙashin Yusuf, gama Yahweh yana tare da Yusuf. Kuma dukan abin da ya yi, Yahweh yakan ba shi nasara.
w14-E 11/1 15 sakin layi na 2
“Don Me Zan Yi Wannan Babbar Mugunta?”
Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar. Ya ce: “Yahweh ya kasance tare da shi. Ya nuna masa ƙaunarsa.” (Farawa 39:21) Hakan ya koya mana cewa babu katangar fursuna ko sarka ko kuma duhu da zai hana Jehobah ƙaunar bayinsa. (Romawa 8:38, 39) Ka yi tunanin irin addu’ar da Yusuf ya yi wa Ubansa na sama kuma ya sami ta’aziya da kwanciyar hankalin da “Allah wanda yake yi mana kowace irin ta’aziyya” yake ba mu. (2 Korintiyawa 1:3, 4; Filibiyawa 4:6, 7) Me kuma Jehobah ya yi ma Yusuf? Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “ya ba shi farin jini a idon shugaban masu gadin ’yan kurkukun.”
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Farawa 38:9, 10) Amma fa Onan ya sani cewa ’ya’yan ba za su zama nasa ba. Saboda haka idan ya shiga wurin matar ɗan’uwansa yakan zubar da maniyyinsa a ƙasa, domin kada ya ba ɗan’uwansa zuriya. 10 Amma wannan abin da ya yi mugu ne a idon Yahweh, shi ma Yahweh ya kashe shi.
it-2-E 555
Onan
(Oʹnan) [tushen ma’anarsa “ɗan fari na mazantaka”].
Shi ne ɗan Yahuda na biyu wadda matarsa ’yar Kan’ana mai suna Shuhu ta haifa masa. (Fa 38:2-4; 1Tar 2:3) Bayan da Jehobah ya hallaka yayansa, Er domin wani zunubi da ya yi, babansa Yahuda ya gaya ma Onan ya auri matar Er mai suna Tamar. Idan suka haifi ɗa, yaron ne zai gāji babansa Er kuma za a ba shi dukiyar ɗan fari da ya kamata a ba wa babansa. Amma idan ba su haifi ɗa ba, Onan ne zai karɓi dukiyar ɗan farin. Don haka, idan Onan ya shiga wurin matar ɗan’uwansa, Tamar, yakan “zubar da maniyyinsa a ƙasa.” Ba wai Onan ya tattaɓa al’aurarsa a hanyar da ba ta dace ba, amma labarin ya nuna cewa “idan ya shiga wurin matar ɗan’uwansa yakan zubar da maniyyinsa a ƙasa.” Hakan ya nuna cewa da gangan Onan ya zubar da maniyyinsa a ƙasa don kada Tamar ta sami haifuwa. Saboda haɗamarsa, ya ƙi ya yi biyayya ga babansa da kuma dokar da Jehobah ya tsara, Jehobah ya hallaka shi kuma ya mutu bai da ɗa.—Fa 38:6-10; 46:12; L.Ƙi 26:19.
(Farawa 38:15-18) Sa’ad da Yahuda ya gan ta, ya ɗauka ko karuwa ce, domin ta rufe fuskarta. 16 Sai ya tafi wurinta a bakin hanyar ya ce, “Ki zo zan kwana da ke.” Ya ce haka gama bai san ita matar ɗansa ba ce. Sai ta ce, “To, me za ka ba ni domin ka kwana da ni?” 17 Sai ya amsa, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga garkena.” Sai ta ce, “To, ko akwai wani abin shaida wadda za ka ba ni cewa za ka aiko da ɗan akuya?” 18 Sai ya amsa, “Wace irin shaida ce zan ba ki?” Sai ta ce, “Hatiminka wanda yana a rataye a wuyanka da kuma sandan tafiyarka.” Domin haka ya ba ta su, sai ya shiga ya kwana da ita, ta kuwa ɗauki cikinsa.
w04-E 1/15 30 sakin layi na 4-5
Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Yahuda ya yi kuskure don ya ƙi ya bar yaronsa Shelah ya auri Tamar kamar yadda ya yi alkawari. Ban da haka ma, ya kwana da wata mata da ya ɗauka cewa ita karuwar haikali ce. Allah ya tsani hakan, Littafi Mai Tsarki ya ce ma’aurata ne kaɗai za su kwana da juna. (Farawa 2:24) Amma a gaskiya, Yahuda bai yi zina da karuwa ba. A maimakon haka, ba tare da saninsa ba ya yi abin da ya kamata ɗansa Shelah ya yi, wato, ya auri Tamar, matar ɗan’uwansa.
Abin da Tamar ta yi ba zina ba ne. ’Yan biyun da ta haifa ba shegu ba ne. Sa’ad da Boaz na Bai’talami ya auri Rut, matar ɗan’uwansa, dattawan Bai’talami sun yi magana mai kyau game da yaron Tamar, wato Ferez. Sun gaya wa Boaz cewa: “Yahweh ya ba ka ’ya’ya daga macen nan waɗanda za su zama kamar ’ya’yan kakanmu Ferez ɗan Tamar da Yahuda.” (Rut 4:12) An ambata sunan Ferez a cikin kakannin Yesu.—Matiyu 1:1-3; Luka 3:23-33.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Farawa 38:1-19) Ana nan sai Yahuda ya tashi daga wurin ’yan’uwansa, ya gangara ya kafa tentinsa kusa da wani mutumin ƙauyen Adullam. Sunan mutumin kuwa Hira ne. 2 A wurin Yahuda ya ga wata mace ’yar mutumin Kan’ana, mai suna Shuhu. Yahuda ya aure ta, ya kwana da ita, 3 sai ta yi ciki ta haifi ɗa, ta kira sunansa Er. 4 Ta sāke yin ciki ta haifi ɗa, ta kira sunansa Onan. 5 Ta kuma yi wani ciki ta haifi ɗa, ta kira sunansa Shela. Yahuda yana a Kezib lokacin da ta haifi shela. 6 Sai Yahuda ya samo wa ɗan farinsa Er mata, sunanta Tamar. 7 Amma Er ɗan Yahuda mugu ne a idon Yahweh, sai Yahweh ya kashe shi. 8 Sa’an nan Yahuda ya ce wa Onan, “Ka shiga wurin matar ɗan’uwanka, ka cika hakkinka na ɗan’uwan maigidanta. Ta haka za a samo wa ɗan’uwanka ’ya’ya.” 9 Amma fa Onan ya sani cewa ’ya’yan ba za su zama nasa ba. Saboda haka idan ya shiga wurin matar ɗan’uwansa yakan zubar da maniyyinsa a ƙasa, domin kada ya ba ɗan’uwansa zuriya. 10 Amma wannan abin da ya yi mugu ne a idon Yahweh, shi ma Yahweh ya kashe shi. 11 Sa’an nan Yahuda ya ce wa Tamar matar ɗansa, “Ki koma gidan babanki ki yi zama kamar macen da mijinta ya mutu, sai ɗana Shela ya yi girma.” Ya faɗi haka gama yana jin tsoro kada Shela kuma ya mutu kamar yadda ’yan’uwansa suka yi. Ta haka Tamar ta tafi ta yi zama a gidan babanta. 12 Ana nan, ’yar Shuhu matar Yahuda ta mutu. Bayan da kwanakin kukan mutuwarta suka wuce, sai Yahuda da abokinsa Hira mutumin Adullam suka haura zuwa garin Timna wurin da masu askin gashin tumakinsa suke. 13 Sa’ad da aka faɗa wa Tamar cewa, “Ga shi, baban mijinki yana haurawa zuwa Timna domin ya aske tumakinsa,” 14 sai Tamar ta tuɓe rigar jikinta na matan da mazansu suka mutu. Ta yi lulluɓi da gyale, ta rufe kanta, ta zauna a bakin ƙofar Enayim, wanda yake a hanya zuwa Timna. Gama ta gani cewa Shela ya yi girma amma ba a sa ta zama matarsa ba. 15 Sa’ad da Yahuda ya gan ta, ya ɗauka ko karuwa ce, domin ta rufe fuskarta. 16 Sai ya tafi wurinta a bakin hanyar ya ce, “Ki zo zan kwana da ke.” Ya ce haka gama bai san ita matar ɗansa ba ce. Sai ta ce, “To, me za ka ba ni domin ka kwana da ni?” 17 Sai ya amsa, “Zan aiko miki da ɗan akuya daga garkena.” Sai ta ce, “To, ko akwai wani abin shaida wadda za ka ba ni cewa za ka aiko da ɗan akuya?” 18 Sai ya amsa, “Wace irin shaida ce zan ba ki?” Sai ta ce, “Hatiminka wanda yana a rataye a wuyanka da kuma sandan tafiyarka.” Domin haka ya ba ta su, sai ya shiga ya kwana da ita, ta kuwa ɗauki cikinsa. 19 Tamar ta tashi ta tafi gida, ta cire gyalenta, ta sāke sa rigar da matan da mazansu suka mutu.
18-24 GA MAYU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 40-41
“Jehobah Ya Ceci Yusuf”
(Farawa 41:9-13) Sai wannan shugaban masu miƙa wa sarki abin sha ya ce, “Yau na tuna da laifina. 10 Lokacin da ka yi fushi da bayinka, ka sa ni da shugaban masu gasa wa sarki burodi a cikin kurkuku cikin gidan shugaban ’yan gadin sarki. 11 Mun yi mafarki a dare ɗaya, ni da shi, kowane mutum da nasa mafarkin. 12 Akwai wani saurayi, mutumin Ibraniyawa tare da mu, bawan shugaban ’yan gadin sarki. Lokacin da muka faɗa masa, sai ya yi mana fassarar mafarkanmu duka, kowa bisa ga irin mafarkinsa. 13 Daidai yadda ya fassara mana, haka kuwa ya kasance. Aka mayar da ni a matsayina, ɗayan kuma mai gasa wa sarki burodi, aka rataye shi.”
w15-E 2/1 14 sakin layi na 4-5
“Ba A Wurin Allah Ne Akan Sami Fassarori Ba?”
Shugaban masu ba sarki abin sha ya manta da Yusuf, amma Jehobah bai manta da shi ba. Wata rana da dare, Jehobah ya sa Fir’auna ya yi mafarkai biyu masu ban mamaki. A mafarki na farko, sarkin ya ga shanu bakwai kyawawa masu kiɓa sun fito daga Kogin Nilu da kuma shanu bakwai marasa kiɓa. Shanu marasa kiɓa sun cinye masu kiɓan. Bayan haka, Fir’auna ya sake mafarki kuma ya ga manyan karan dawa bakwai masu kyau da kuma ƙananan karan dawa bakwai marasa kyau. Ƙananan karan dawan sun cinye manyan karan dawan. Da gari ya waye, Fir’auna ya damu sosai game da mafarkan. Don haka, ya kira dukan mutanensa musu hikima da masu dabo don su gaya masa ma’anar mafarkan, amma sun kasa yin hakan. (Farawa 41:1-8) Shin sun ƙasa magana ne ko kuma sun ba da ma’ana dabam-dabam ga mafarkin? Ba mu sani ba. Abin da muka sani shi ne ba su iya gaya wa Fir’auna ma’anar mafarkin ba duk da cewa Fir’auna ya damu ya san ma’anar mafarkin.
A wannan lokacin ne shugaban masu ba wa sarki abin sha ya tuna da Yusuf. Zuciyarsa ta dame shi kuma ya ba wa Fir’auna labarin wani saurayi a kurkuku shekaru biyu da suka shige. Saurayin ya gaya wa shi da shugaban masu gasa wa sarki burodi ma’anar mafarkin da suka yi kuma ya faru daidai yadda ya faɗa. Nan da nan sai Fir’auna ya ba da umurni cewa a kawo masa Yusuf.—Farawa 41:9-13.
(Farawa 41:16) Sai Yusuf ya amsa wa Fir’auna ya ce, “Ranka ya daɗe! Ba ni ne da iyawar ba, amma Allah zai ba Fir’auna cikakken fassara.”
(Farawa 41:29-32) Ga shi, za a yi shekara bakwai ana samun abinci a yalwace a dukan ƙasar Masar. 30 Amma bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa. Tsananin yunwa za ta sa a manta da dukan abincin nan da aka samu a yalwace na ƙasar Masar. Yunwa kuwa za ta cinye ƙasar. 31 Zai kuwa zama kamar ba a taɓa samun abinci a yalwace ba, gama za ta yi tsanani sosai. 32 Maimaitawar mafarkin nan na Fir’auna kuwa, ya nuna cewa Allah ya riga ya tabbatar da zancen, kuma Allah zai sa ya faru ba da jimawa ba.
w15-E 2/1 14-15
“Ba A Wurin Allah Ne Akan Sami Fassarori Ba?”
Jehobah yana ƙaunar mutane masu aminci da kuma sauƙin kai, shi ya sa ya taimaka wa Yusuf ya san ma’anar mafarkan da masafan Fir’auna suka kasa sani. Yusuf ya gaya wa Fir’auna cewa mafarkai guda biyun suna nufin abu ɗaya. Jehobah ya maimaita saƙon ne don ya “tabbatar da zancen,” wato zai sa hakan ya faru ba fasawa. Shanu masu kiɓa da karan dawa masu kyau suna nufin za a yi shekara bakwai ana samun abinci a yawalce a Masar. Shanu marasa kiɓa da kuma karan dawa marasa kyau suna nufin cewa bayan an samu abinci a yawalce, za a yi yunwa na shekara bakwai. Yunwar za ta yi tsanani sosai da har abincin ƙasar zai kare gabaki ɗaya.—Farawa 41:25-32.
(Farawa 41:38-40) Sai Fir’auna ya ce wa dattawansa, “Za mu iya samun mutum irin wannan wanda Ruhun Allah yake a cikinsa haka?” 39 Sai Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Da yake Allah ya nuna maka dukan wannan, ai, babu wani mai ganewa da kuma mai hikima kamarka. 40 Kai, za ka zama shugaban gidana, kuma dukan mutanena za su karɓi umarni daga gare ka. Game da kujerar mulki kaɗai zan fi ka.”
w15-E 2/1 15 sakin layi na 3
“Ba A Wurin Allah Ne Akan Sami Fassarori Ba?”
Fir’auna bai ɓata lokaci wajen cika abin da ya faɗa ba. An saka wa Yusuf riga mai kyau. Fir’auna ya ba wa Yusuf abin wuya na zinariya da zobe mai hatimi da keken doki, kuma ya ba shi ikon zuwa ko’ina a ƙasar don ya soma aikinsa. (Farawa 41:42-44) A cikin rana ɗaya, Yusuf ya bar kurkuku kuma ya zama shugaba. Ya tashi da safe a matsayin bawa, amma ya yi barci a ranar a matsayin mai iko bayan Fir’auna. Babu shakka, Jehobah ya albarkaci Yusuf don bangaskiyarsa. Jehobah ya ga dukan rashin adalcin da bawansa ya fuskanta. Ya magance abubuwan nan a lokaci da kuma yadda ya dace. Nufin Jehobah shi ne ya albarkaci Yusuf kuma ya ceci al’ummar Isra’ila daga bala’i a nan gaba. Za mu ga yadda ya yi hakan a talifi na gaba.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Farawa 41:14) Sai Fir’auna ya aika a kawo Yusuf, sai aka fitar da shi da gaggawa daga kurkuku. Bayan da ya yi aski ya canja rigunansa, sai ya zo gaban Fir’auna.
(Farawa 41:33) “Yanzu bari Fir’auna ya nemi mutum mai ganewa da hikima, ya sa shi bisa ƙasar Masar.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Farawa 40:1-23) Wani lokaci bayan da abubuwan nan suka faru, sai shugaban masu miƙa wa sarki abin sha da shugaban masu gasa wa sarki burodi suka yi wa maigidansu sarkin Masar laifi. 2 Sai Sarki Fir’auna ya yi fushi da masu aikin nan biyu sosai. 3 Ya kulle su a gidan shugaban ’yan gadin sarki, a kurkukun da aka kulle Yusuf. 4 Suka kasance a kurkuku na ɗan tsawon lokaci, shugaban ’yan gadin kuwa ya sa su a ƙarƙashin Yusuf. 5 A dare ɗaya, sai mai miƙa wa sarki abin sha da mai gasa wa sarki burodi, dukansu biyu suka yi mafarki lokacin da suke cikin kurkuku. Kowannensu kuwa da mafarkinsa dabam da kuma fassararsa. 6 Sa’ad da Yusuf ya zo wurinsu da safe, ya gan su sun damu sosai. 7 Sai ya tambayi masu aikin nan biyu na Fir’auna, waɗanda suke tare da shi a kurkukun maigidansa, ya ce, “Don me kuka ɓata fuskokinku yau haka?” 8 Suka ce masa, “Mun yi mafarkai ne, kuma babu wanda zai yi mana fassararsu.” Sai Yusuf ya amsa ya ce, “Shin, ba a wurin Allah ne akan sami fassarori ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.” 9 Saboda haka sai shugaban masu miƙa wa sarki abin sha ya faɗa wa Yusuf mafarkinsa. Ya ce masa, “A mafarkina na ga itacen inabi a gabana. 10 A itacen akwai reshe uku. Da zarar suka fara fitar da ganye, sai fulawa suka bayyana, kuma ba a jima ba sai ga ’ya’yan inabi suka nuna a kai. 11 Ni juwa, ina riƙe da kwaf na Fir’auna a hannuna. Sai na ɗauki ’ya’yan inabin na matse a kwaf ɗin, na sa wa Fir’auna a hannu.” 12 Sa’an nan Yusuf ya ce masa, “To, ga fassarar mafarkinka, reshe ukun nan kwana uku ne. 13 Bayan kwana uku, Fir’auna zai ciro ka daga kurkuku, ya mayar da kai a matsayinka, za ka kuma sa kwaf na Fir’auna a hannunsa kamar yadda dā kake yi masa. 14 Amma ka tuna da ni, sa’ad da abin da na faɗa ya cika a kanka. Ka yi mini alheri ka yi wa Fir’auna magana game da ni, domin a fitar da ni daga wannan wuri. 15 Gama hakika an sace ni ne daga ƙasar Ibraniyawa. A nan ƙasar Masar kuma ban yi wani abin da ya isa a sa ni a kurkuku ba.” 16 Sa’ad da shugaban masu gasa wa sarki burodi ya ga fassarar nan ta yi kyau, sai ya faɗa wa Yusuf nasa ya ce, “Ni ma na yi mafarki. A mafarkina na ga kwanduna uku na waina a kaina. 17 A kwandon da yake bisa duka akwai abinci iri-iri da aka yi domin Fir’auna, amma tsuntsaye suna ta ci daga cikin kwandon da yake a kaina.” 18 Yusuf ya amsa ya ce, “Ga fassarar mafarkin, kwanduna ukun nan kwana uku ne. 19 A cikin kwana uku Fir’auna zai cire kanka daga jikinka, ya rataye jikinka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.” 20 A rana ta uku, wadda ita ce ranar tunawa da haifuwar Fir’auna, Fir’auna ya yi wa dukan dattawansa biki. Sai ya cire shugaban masu miƙa wa sarki abin sha da shugaban masu gasa wa sarki burodi daga kurkuku, ya kawo su gaban dattawansa. 21 Sai ya mayar da shugaban masu miƙa wa sarki abin sha a matsayinsa na dā, ya kuwa ba Fir’auna kwaf a hannunsa. 22 Amma ya rataye shugaban masu gasa wa sarki burodi, daidai yadda Yusuf ya yi musu fassara. 23 Amma shugaban masu miƙa wa sarki abin sha bai ko tuna da Yusuf ba, ya manta da shi.
25-31 GA MAYU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 42-43
“Yusuf Yana da Kamun Kai Sosai”
(Farawa 42:5-7) Ta haka ’ya’yan Yakub suka isa Masar tare da sauran mutanen da suka tafi domin sayen hatsi, gama yunwar ta kai yankin Kan’ana. 6 Yusuf kuwa shi ne gwamnan ƙasar, shi ne kuma mai sayar da hatsi ga dukan mutanen ƙasar. Sai ’yan’uwan Yusuf suka zo gabansa suka rusuna da fuskokinsu har ƙasa. 7 Da Yusuf ya ga ’yan’uwansa sai ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da zafi. Ya ce musu, “Daga ina kuka fito?” Suka ce, “Daga ƙasar Kan’ana domin mu sayi abinci.”
w15-E 5/1 13 sakin layi na 5
“Ni Allah Ne?”
Yusuf fa? Ya gane ’yan’uwansa nan da nan! Ban da haka ma, da ya gan su sun durkusa a gabansa, ya tuna da lokacin da yake ƙarami. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ‘Yusuf ya tuna da mafarkan’ da ya yi sa’ad da yake yaro cewa ’yan’uwansa za su durkusa a gabansa kamar yadda suke yi yanzu! (Farawa 37:2, 5-9; 42:7, 9) Mene ne Yusuf zai yi? Zai rungume su ne ko kuma ya rama abin da suka yi masa?
w15-E 5/1 14 sakin layi na 1
“Ni Allah Ne?”
Mai yiwuwa ba za ka iya samun kanka a irin wannan yanayin ba. Amma akan samu rashin jituwa a cikin iyalai da dama a yau. Idan muka samu kanmu a irin wannan yanayin, yakan mana sauƙi mu bi abin da zuciyarmu ta gaya mana. Zai fi kyau mu yi koyi da Yusuf kuma mu yi tunani a kan abin da Allah yake so mu yi. (Karin Magana 14:12) Mu tuna cewa ko da yake zaman lafiya da ’yan gidanmu yana da muhimmanci, kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma Ɗansa ne ya fi muhimmanci.—Matiyu 10:37.
(Farawa 42:14-17) Amma Yusuf ya ce musu, “Kamar yadda dai na faɗa muku, ku ’yan leƙen asiri ne! 15 Ga yadda zan gwada ku, na rantse da ran Fir’auna, ba za ku fita daga wurin nan ba, sai autanku ya zo nan. 16 Ku aiki ɗaya daga cikinku ya kawo ɗan’uwanku. Amma sauranku, za a kulle ku domin a tabbatar da maganarku, ko akwai gaskiya a cikinku. Idan ba haka ba, na rantse da ran Fir’auna, ku ’yan leƙen asiri ne!” 17 Sai ya kulle su duka cikin kurkuku har kwana uku.
w15-E 5/1 14 sakin layi na 2
“Ni Allah Ne?”
Yusuf ya yi wasu abubuwa don ya san ko ’yan’uwansa sun tuba da gaske. Ya yi amfani da mai fassara kuma ya yi musu magana cikin fushi yana zarginsu cewa su ’yan leƙen asiri ne. Don su kāre kansu, sun ba shi labarin iyalinsu kuma suka gaya masa cewa suna da wani ƙani a gida. Yusuf ya yi farin cikin jin hakan, amma bai nuna musu hakan ba. Don ya san ko da gaske ne ɗan’uwansa yana nan da rai, Yusuf ya ce: “Ga yadda zan gwada ku.” Sai ya gaya musu cewa yana so ya ga ɗan autansu. Daga baya ya amince ya bar su su je gida su kawo ɗan autansu amma zai riƙe ɗaya daga cikinsu.—Farawa 42:9-20.
(Farawa 42:21, 22) Sai suka ce wa junansu a yarensu, “A ainihin gaskiya, alhakin ɗan’uwanmu ne yake binmu, da yake mun ga azabarsa sa’ad da yake roƙonmu mu taimake shi, amma muka ƙi jinsa. Saboda haka ne wannan azaba ta sauko mana.” 22 Sai Ruben ya amsa musu ya ce, “Aha! Ban faɗa muku ba cewa kada ku yi wa yaron nan wani abu ba? Kuka ƙi ku ji ni. To, yau alhakin jininsa ne muke biya.”
it-2-E 108 sakin layi na 4
Yusuf
’Yan’uwan Yusuf sun soma fahimtar cewa suna fuskantar waɗannan matsalolin ne don sun sayar da Yusuf shekarun da suka shige. Sun soma tattauna muguntar da suka yi a gaban Yusuf, wanda ba su gane ba. Da Yusuf ya ji abubuwan da suke faɗa wanda ya nuna cewa sun tuba da gaske, ya tafi wani wajen ya yi kuka. Da ya dawo, ya sa an kama Simeyon har sai sun je sun kawo ɗan autansu.—Fa 42:21-24.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Farawa 42:22) Sai Ruben ya amsa musu ya ce, “Aha! Ban faɗa muku ba cewa kada ku yi wa yaron nan wani abu ba? Kuka ƙi ku ji ni. To, yau alhakin jininsa ne muke biya.”
(Farawa 42:37) Sa’an nan Ruben ya yi magana da babansa ya ce, “Bari ka kashe ’ya’yana maza biyu idan ban dawo tare da yaron wurinka ba. Kai dai ka sa shi a hannuna, zan kuwa dawo maka da shi.”
it-2-E 795
Ruben
Ruben ya nuna halaye masu kyau sa’ad da ya roƙi ’yan’uwansa guda tara su jefa Yusuf cikin rijiya mara ruwa maimakon su kashe shi. Ya faɗi hakan ne da niyyar dawowa ya ceci Yusuf. (Fa 37:18-30) Bayan fiye da shekaru 20, ’yan’uwan Yusuf sun ce alhakin Yusuf ne ya sa ake zarginsu cewa su ’yan leƙen asiri ne a Masar, amma Ruben ya tuna musu cewa alhakin Yusuf ba ya kansa. (Fa 42:9-14, 21, 22) Bayan haka, da Yakub ya ƙi ya amince Benyamin ya bi su Masar, Ruben ya tabbatar wa mahaifinsa cewa zai kula da yaron ta wajen gaya masa cewa: “Bari ka kashe ’ya’yana maza biyu idan ban dawo tare da [Benyamin] wurinka ba.”—Fa 42:37.
(Farawa 43:32) Sai aka sa masa abinci a wurinsa dabam, aka sa wa ’yan’uwansa abinci a wurinsu dabam, aka sa wa Masarawa kuma abinci a wurinsu dabam. Sun yi haka gama Masarawa ba sa cin abinci tare da Ibraniyawa, saboda wannan abin ƙyama ne ga Masarawa.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Farawa 42:1-20) Lokacin da Yakub ya ji cewa akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa ’ya’yansa, “Don me kuke zama kuna kallon juna haka? 2 Ga shi na ji cewa akwai hatsi a Masar. Ku gangara wurin ku sayo mana, domin mu samu mu rayu kada mu mutu.” 3 Sai ’yan’uwan Yusuf goma suka gangara zuwa Masar, domin su sayo hatsi. 4 Amma Yakub bai aiki Benyamin tare da sauran ’yan’uwan Yusuf ba, gama yana tsoro kada wani abu ya faru da shi. 5 Ta haka ’ya’yan Yakub suka isa Masar tare da sauran mutanen da suka tafi domin sayen hatsi, gama yunwar ta kai yankin Kan’ana. 6 Yusuf kuwa shi ne gwamnan ƙasar, shi ne kuma mai sayar da hatsi ga dukan mutanen ƙasar. Sai ’yan’uwan Yusuf suka zo gabansa suka rusuna da fuskokinsu har ƙasa. 7 Da Yusuf ya ga ’yan’uwansa sai ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da zafi. Ya ce musu, “Daga ina kuka fito?” Suka ce, “Daga ƙasar Kan’ana domin mu sayi abinci.” 8 Ko da yake Yusuf ya gane da ’yan’uwansa, su ba su gane shi ba. 9 Sai Yusuf ya gane da mafarkan da dā ya yi a kansu. Ya ce musu, “Ku masu leƙen asiri ne, kun zo ne domin ku ga inda ba mu da ƙarfi a ƙasar.” 10 Suka ce wa Yusuf, “A’a, ranka ya daɗe, mun zo ne domin mu sayi abinci.” 11 Mu duka ’ya’yan mutum guda ne, masu gaskiya, mu kuma ba ’yan leƙen asiri ba ne. 12 Yusuf ya ce, “A’a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu ba ta da karfi ne.” 13 Sai suka ce, “Ranka ya daɗe, mu bayinka ’yan’uwa ne goma sha biyu, kuma ’ya’yan mutum guda a ƙasar Kan’ana. Autanmu yana tare da babanmu, ɗayanmu kuma ba shi da rai.” 14 Amma Yusuf ya ce musu, “Kamar yadda dai na faɗa muku, ku ’yan leƙen asiri ne! 15 Ga yadda zan gwada ku, na rantse da ran Fir’auna, ba za ku fita daga wurin nan ba, sai autanku ya zo nan. 16 Ku aiki ɗaya daga cikinku ya kawo ɗan’uwanku. Amma sauranku, za a kulle ku domin a tabbatar da maganarku, ko akwai gaskiya a cikinku. Idan ba haka ba, na rantse da ran Fir’auna, ku ’yan leƙen asiri ne!” 17 Sai ya kulle su duka cikin kurkuku har kwana uku. 18 A rana ta uku sai Yusuf ya ce musu, “To, ga abin da za ku yi domin ku rayu, gama ni mai tsoron Allah ne. 19 Idan ku masu gaskiya ne, bari ɗaya daga cikinku ya zauna a nan kurkuku, sa’an nan sauran su kai wa iyalanku da suke cikin yunwa hatsi. 20 Sa’an nan sai ku kawo mini autanku. Idan kuka yi haka zan tabbatar da maganarku, ba za a kuwa kashe ku ba.” Haka kuwa suka yarda su yi.