Muna Bukatar Sabuwar Duniya!
Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres ya ce: “Duniya tana cike da matsaloli.” Ka yarda da hakan?
Labaran duniya suna cike da abubuwa masu tā da hankali, kamar
- Cututtuka da annoba 
- Bala’o’i 
- Talauci da yunwa 
- Gurɓata mahalli da ɗumamar yanayi 
- Aikata laifi da ta’addanci da cin hanci 
- Yaƙe-yaƙe 
Lallai muna bukatar sabuwar duniya, inda za a sami
- Ƙoshin lafiya 
- Zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali 
- Abinci a yalwace 
- Mahalli marar guba 
- Adalci don kowa 
- Salama a duk duniya 
Amma me muke nufi idan muka yi maganar sabuwar duniya?
Me zai faru da duniyar da muke ciki yanzu?
Me za mu yi don mu yi rayuwa a sabuwar duniya?
Wannan fitowar Hasumiyar Tsaro tana ɗauke da amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya bayar ga tambayoyin nan, da ma wasu.