Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mrt talifi na 45
  • Rasha ta Kai wa Yukiren Hari

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Rasha ta Kai wa Yukiren Hari
  • Karin Batutuwa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da irin wadannan abubuwan?
  • Me zai sa ka kasance da bege game da nan gaba?
  • Wane ne “Sarkin Arewa” a Yau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Addini da Yakin Yukiren?
    Karin Batutuwa
  • An Shiga Shekara Ta Biyu a Yakin Yukiren​—Wane Bege ne Ke Littafi Mai Tsarki?
    Karin Batutuwa
  • “Sarkin Arewa” a Kwanaki na Karshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Karin Batutuwa
mrt talifi na 45
Taswirar Yukiren da kasashe da ke kusa da ita.

Rasha ta Kai wa Yukiren Hari

Da asuba a ranar 24 ga Fabrairu 2022, Rasha ta kai wa Yukiren hari duk da cewa shugabannin duniya sun yi kokari kada yaki ya barke. Ta yaya wannan yakin zai iya shafan duniya? Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai suna António Guterres ya ce: “Wannan yakin zai sa mutane su sha wahala sosai kuma barna da zai jawo zai shafi tsaron kasashen Turai da kuma dukan duniya.”

Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da irin wadannan abubuwan?

  • Yesu Kristi ya yi annabci cewa “al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki.” (Matiyu 24:7) Ka Karanta talifin nan “Mene ne Ake Nufi da Alamun ‘Kwanaki na Karshe’ ko ‘Karshen Duniya’?” don ka ga yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa yake-yake da ake yi a yau suna cika annabcin da Yesu ya yi.

  • Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya kwatanta yake-yake a matsayin mahayi da ke zaune a kan wani jan “doki” kuma ya “kawar da salama daga duniya.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:4) Ka karanta talifin nan “Su Wane ne Mahaya Hudun?” don ka ga yadda wannan annabcin yake da alaka da yake-yaken da ake yi a yau.

  • Littafin Daniyel ya annabta cewa “sarkin arewa” da “sarkin kudu” za su yi jayayya da juna. (Daniyel 11:​25-45) Ka kalli bidiyon nan Annabcin da Ya Cika​—Daniyel Sura 11 don ka ga dalilin da ya sa Rasha da kawayenta ne suke wakiltar sarkin arewa.a

  • Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya kuma bayyana yakin “babbar Ranar nan ta Allah Mai Iko Duka.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 16:​14, 16) Amma wannan ba yaki ba ne tsakanin al’ummai kamar yadda muke gani a yau. Don samun karin bayani game da abubuwan da za su faru a nan gaba, ka karanta “Mene ne Yakin Armageddon?”

Me zai sa ka kasance da bege game da nan gaba?

  • Littafi Mai Tsarki ya ce Allah zai kawar da “yake-yake a dukan duniya.” (Zabura 46:9) Ka karanta talifin nan “A Real Hope for a Better Tomorrow” don ka kara koya game da alkawuran da Allah ya yi da za su faru nan gaba.

  • Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a don Mulkin Allah ya zo. (Matiyu 6:​9, 10) Wannan Mulkin, gwamnati ce a sama da za ta sa a yi nufin Allah a duniya, kuma hakan ya kunita samun salama a duniya. Don ka koyi yadda za ka amfana daga wannan Mulkin, ka kalli bidiyon nan Mene ne Mulkin Allah?

Shaidun Jehobah fiye da 129,000 ne suke zama a Yukiren. Kamar Shaidun da suke zama a kowace kasa, suna yin koyi da Yesu ta wajen kin saka hannu a yaki da kuma siyasa. (Yohanna 18:36) A fadin duniya, Shaidun Jehobah sun ci gaba da wa’azi game da Mulkin Allah, kuma ita ne zai magance matsalolin ’yan Adam, har da yaki. (Matiyu 24:14) Muna gayyatarka ka tuntube mu don ka kara koya game da begen da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

a Don ka samu cikakken bayani game da wannan annabci, ka duba talifofin nan “‘Sarkin Arewa’ a Kwanaki na Karshe” da kuma “Wane ne ‘Sarkin Arewa’ a Yau?”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba