Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp21 Na 2 pp. 10-12
  • Abin da Za Ka Iya Yi don Ka Shiga Sabuwar Duniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Za Ka Iya Yi don Ka Shiga Sabuwar Duniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ZA KA TSIRA IDAN KA “SAN” ALLAH
  • KA KARANTA KALMAR ALLAH KULLUM
  • KA ROƘI ALLAH YA TAIMAKA MAKA
  • Abubuwan da Allah Ya Riga Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Sabuwar Duniya Mai Salama Ta Allah—Za Ka Iya Zama Ciki
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Me Ya Sa Yesu Ya Sha Wahala Kuma Ya Mutu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Za Ka Iya Yin Rayuwa Har Abada a Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
wp21 Na 2 pp. 10-12

Abin da Za Ka Iya Yi don Ka Shiga Sabuwar Duniya

Talifofin da suka gabata sun nuna mana cewa nan ba da daɗewa ba, Allah zai kawo ƙarshen wannan muguwar duniya da matsalolinta. Mun tabbata cewa hakan zai faru. Me ya sa? Domin Allah ya yi alkawari a cikin Kalmarsa wato Littafi Mai Tsarki cewa:

“Duniya . . . tana wucewa.”​—1 YOHANNA 2:17.

Muna da tabbaci cewa mutane za su tsira domin ayar da aka ambata a sama ta ƙara da cewa:

“Wanda ya aikata nufin Allah zai rayu har abada.”

Saboda haka, idan muna so mu tsira, muna bukatar mu yi nufin Allah. Amma sai mun san Allah kafin mu san nufinsa.

ZA KA TSIRA IDAN KA “SAN” ALLAH

Hotuna: 1. Wata nas ta zauna a kasa a asibiti ta gaji domin aiki ya yi mata yawa. 2. Ta fita shan iska sai ta ga wata abokiyar aikinta tana karanta wata mujalla da farin ciki. 3. Abokiyar aikinta ta karanta mata wata aya daga Littafi Mai Tsarki kuma ta ba ta katin JW.

Yesu ya ce: “Rai na har abada kuwa shi ne, mutane su san ka, kai da kake Allah makaɗaici na gaskiya.” (Yohanna 17:3) Don mu tsira wa ƙarshen duniya kuma mu rayu har abada, dole ne mu “san” Allah. Hakan ba ya nufin sanin cewa Allah yana wanzuwa ko kuma sanin waɗansu abubuwa game da shi kawai. Muna bukatar mu zama abokansa. Idan muna so abokantakarmu da wani ta yi ƙarfi, dole ne mu riƙa kasancewa da mutumin. Haka ma abokantaka da Allah take. Ka yi la’akari da wasu abubuwa da ke Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu zama aminan Allah.

Wasu Abubuwa da Muka Koya Daga Littafi Mai Tsarki

Nas din a gidanta ta shiga dandalin jw.org.

Mun koyi cewa tun da farko nufin Allah ne ’yan Adam su yi rayuwa a Aljanna.

Allah ya halicci mutane na farko wato Adamu da Hauwa’u kuma ya saka su a wani wuri mai kyau da aka kira shi lambun Adnin. Allah ya halicce su kamilai, kuma ya yi musu tanadin dukan abubuwan da suke bukata don su ji daɗin rayuwa. Da a ce sun ci gaba da zama abokan Allah, da sun rayu har abada. Amma sun zaɓi su ƙi bin umurnin da Allah ya ba su.

Mun san dalilin da ya sa muke shan wahala.

Sa’ad da mutum na farko wato Adamu ya yi wa Allah rashin biyayya, ya rasa damar yin rayuwa har abada, kuma hakan ya shafi duka ’ya’yansa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, zunubin nan kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta bi ta shiga dukan ’yan Adam.” (Romawa 5:12) Kamar yadda mutum zai iya gādan wata cuta daga iyayensa, haka ma duka ’yan Adam suka gāji ajizanci daga wurin Adamu da Hauwa’u. Abin da ya sa muke tsufa kuma su mutu ke nan.

Mun san abin da Allah ya yi don ya taimaka mana.

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Allah ya turo Yesu duniya don ya ba da ransa a madadinmu. Wani mutum mai shekara 86 a ƙasar Indiya mai suna Prabhakar ya yi magana game da wannan ƙaunar kuma ya ce: “Hakan ya nuna mini cewa Jehobaha yana ƙauna ta sosai. Kuma ƙaunar ta sa na kasance da begen yin rayuwa har abada.”

Mun koyi yadda za mu nuna godiya don abin da Allah ya yi mana.

Littafi Mai Tsarki ya ce za mu iya nuna godiya domin abin da Allah ya yi mana ta wajen yin “biyayya da umarnin Allah.” (1 Yohanna 2:3) Jehobah ya nuna mana abin da muke bukatar mu yi don mu ji daɗin rayuwa yanzu. (Ishaya 48:17, 18) Allah ba ya so mu sha wahala. Shi ya sa ya yi alkawari cewa idan mun bi umurnansa, za mu ji daɗin rayuwa yanzu kuma za mu sami damar yin rayuwa har abada.

KA KARANTA KALMAR ALLAH KULLUM

Nas din tana kallon sama bayan ta gama karanta Littafi Mai Tsarki a lokacin da ta fita shan iska.

Za ka iya tsira wa ƙarshen wannan duniyar ta wajen yin addu’a ga Allah ya taimaka maka da kuma yin nufinsa

Muna cin abinci a kullum don mu rayu. Amma Yesu ya ce: “Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga wurin Allah.”​—Matiyu 4:4.

A yau, za mu iya karanta abin da Jehobah ya faɗa a cikin Littafi Mai Tsarki. Idan ka karanta Littafi Mai Tsarki, za ka san abin da Allah ya yi a dā, da abin da yake yi a yanzu, da kuma abin da zai yi a nan gaba.

KA ROƘI ALLAH YA TAIMAKA MAKA

Me za ka yi idan kana so ka bi abin da Allah ya faɗa, amma yana yi maka wuya ka daina yin abin da ya haramta? Sanin Allah sosai zai taimaka maka.

Ka yi la’akari da misalin wata mata da a dā ta yi fasiƙanci sosai da za mu kira ta Sakura. Sa’ad da ta soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ta koyi umurnin Allah cewa mu “guje wa halin lalata!” (1 Korintiyawa 6:18) Sakura ta yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mata, kuma ta daina wannan halin. Amma bai yi mata sauƙi ta daina ba. Ta ce: “Idan na soma tunanin banza, ina addu’a ga Jehobah kuma in gaya masa dukan abin da ke zuciyata, domin na san cewa ba zan iya daina wannan halin da kaina ba. Yin addu’a ya sa na daɗa kusantar Jehobah.” Kamar yadda Sakura ta yi, miliyoyin mutane suna koya game da Jehobah. Jehobah yana ba su ƙarfin da suke bukata don su yi canje-canje a rayuwarsu kuma su soma yin irin rayuwar da yake so.​—2 Korintiyawa 4:7.

Yayin da kake daɗa sanin Allah, shi ma zai “san” da kai a matsayin amininsa. (Galatiyawa 4:9; Zabura 25:14) Hakan zai sa ka cancanci shiga sabuwar duniya. Amma yaya sabuwar duniyar nan za ta zama? Za a bayyana hakan a talifi na gaba.

a Jehobah ko Yahweh shi ne sunan Allah a Littafi Mai Tsarki.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba