Gabatarwa
Shin za ka so ka yi rayuwa a duniyar da babu yaƙi da tashin hankali? Yawancin mutane za su so hakan, amma suna ganin kamar ba zai taɓa yiwu ba. Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da ya sa ꞌyanꞌadam ba za su iya hana yaƙe-yaƙe ba. Ya kuma bayyana abin da ya sa za ka iya kasance da tabbaci cewa zai yiwu a sami salama a faɗin duniya, kuma hakan zai faru nan ba da daɗewa ba.
A mujallar nan, “yaƙi” da kuma “tashin hankali” suna nufin ƙungiyoyin siyasa ko ƙasashe da suke amfani da makamai ko kuma sojojinsu don su yaƙi juna. An canja sunayen wasu mutanen da aka ambata a mujallar nan.