Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • my labari na 61
  • Dauda Ya Zama Sarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dauda Ya Zama Sarki
  • Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Dauda da Saul
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Dalilin Da Ya Sa Dole Dauda Ya Gudu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • ‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Isra’ilawa Sun Ce a Naɗa Musu Sarki
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
Dubi Ƙari
Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
my labari na 61

LABARI NA 61

Dauda Ya Zama Sarki

SAUL ya sake ƙoƙarin ya kama Dauda. Ya kwashi ƙwararrun sojojinsa 3,000 ya fita neman Dauda. Da Dauda ya fahimci haka, ya aiki ’yan leƙen asiri su je su nemi inda Saul da sojojinsa suka yi zango. Sai Dauda ya tambayi biyu daga cikin mutanensa: ‘Wanene daga cikinku zai bi ni zuwa sansanin Saul?’

‘Zan bi ka,’ in ji Abishai. Abishai ɗan Zeruiah ne yar Dauda. Sa’ad da Saul da mutanensa suna barci, Dauda da Abishai suka yi sanɗa suka shiga cikin sansanin. Suka ɗauki mashin Saul da gorar ruwansa, da aka ajiye a kusa da kan Saul. Babu wanda ya gan su ko ya ji wani abu domin dukansu suna barci mai zurfi.

Ka ga Dauda da Abishai yanzu. Sun fita sun hau dutse. Dauda ya yi wa shugaban sojojin Isra’ila ihu: ‘Abner, me ya sa ba ka tsare shugabanmu sarki ba? Duba! Ga mashinsa da kuma gorar ruwansa?’

Saul ya farka. Ya gane muryar Dauda, ya yi tambaya: ‘Kai nake ji, Dauda?’ Ka ga Saul da Abner a nan?

‘Ni ne, ubangiji na sarki,’ Dauda ya amsa wa Saul. Sai kuma Dauda ya yi tambaya: ‘Me ya sa kake so ka kama ni? Wane mugun abu ne na yi? Gamashin ka, Ya sarki. Bari ɗaya daga cikin sojojin ka ya zo ya karɓa.’

‘Na yi kuskure,’ in ji Saul. ‘Na yi wauta.’ Sai Dauda ya tafi abinsa, Saul kuma ya koma gida. Amma sai Dauda ya ce wa kansa: ‘Wata rana Saul zai kashe ni. Zan gudu zuwa ƙasar Filistiyawa.’ Kuma abin da ya yi ke nan. Dauda ya ruɗi Filistiyawa ya sa suka gaskata cewa yanzu shi yana tare da su.

Daga baya sai Filistiyawa suka je su yaƙi Isra’ila. A yaƙin aka kashe Saul da kuma Jonathan. Wannan ya sa Dauda ya yi baƙin ciki ƙwarai, ya kuma rubuta waƙa mai daɗi, in da ya rera yana cewa: ‘Na yi baƙin ciki ƙwarai saboda kai, ɗan’uwana Jonathan. Ina ƙaunarka ƙwarai!’

Bayan haka, Dauda ya koma Isra’ila zuwa birnin Hebron. Yaƙi ta ɓarke tsakanin mutanen da suka zaɓi ɗan Saul Ishbosheth ya zama sarki da waɗanda suka zaɓi Dauda ya zama sarki. Amma a ƙarshe mutanen Dauda suka yi nasara. Dauda yana ɗan shekara 30 ya zama sarki. Ya yi sarauta a Hebron na shekara bakwai da rabi. Wasu ’ya’ya da aka haifa masa a nan ya sa masu suna Amnon, Absalom da Adonijah.

Lokaci ya yi da Dauda da mutanensa suka je su kama kyakkyawan birni da ake kira Urushalima. Jo’ab, wani ɗan yar Dauda Zeruiah, ya yi ja-gora wajen yaƙi. Dauda ya ba shi lada wajen mai da shi shugaban mayaƙansa. Yanzu Dauda ya fara sarauta a birnin Urushalima.

1 Samuila 26:1-25; 27:1-7; 31:1-6; 2 Samuila 1:26; 3:1-21; 5:1-10; 1 Labarbaru 11:1-9.

Tambayoyi don Nazari

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba