Aljannu Masu Kisa Ne!
Shaitan da aljannu dai masu cin zali ne da kuma haɗari kowane lokaci. A lokutta na farko Shaitan ya kashe garke da kuma bayin Ayuba mai-aminci. Ya kuma kashe yaran Ayuba guda goma ta wurin “guguwa mai-girma” ya rushe gidan da suke cikin. Bayan wannan Shaitan ya buge Ayuba da “gyambuna masu-ciwo, tun daga tafin tsawunsa har kan kansa.”—Ayuba 1:7-19; 2:7.
A kwanakin Yesu, aljannu sun sa wasu mutane su kāsa yin magana da kuma makantar da su. (Matta 9:32, 33; 12:22) Sun zalunta mutum har da ya tsage jikinsa da duwatsu. (Markus 5:5) Sun kuma sa wani yaro ya yi ta kuka, su yar da shi a ƙasa kuma “ya murmurɗe shi da zafi ƙwarai.”—Luka 9:42.
Ayau fa, Shaitan da aljannu suna kan kisa kamar yadda suke a dā. Hakika, miyagun ayukansu sun yawaita ko tun aka jefasda su daga sama. Rahotanni daga kewayen duniya sun shaidar da cin zalinsu. Suna ɗaure wasu mutane da ciwo. Sukan razanadda wasu kuma da dare, har ma suna hana su barci ko kuwa sa su yin mafalkai masu ban-tsoro. Sukan fyaɗe wasu kuma. Har ila sukan sa wasu hauka, yin kisa, ko kuwa kisan kansa.
Lintina, wata wadda ta ke da zama a Suriname, ta faɗi cewa wani aljan ko kuwa mugun ruhu ya kashe mambobin iyalinta 16 kuma ya azabanta a jiki da azancinta na shekaru 18. Daga abinda ya faru mata fa, ta faɗi cewa aljannun “suna jin daɗin azabanta mutane da basu son su zama abincinsu har zuwa mutuwa.”
Amma Jehovah yana iya tsare bayinsa daga faɗawar Shaitan.—Misalai 18:10.
[Hotuna a shafi na 11]
A dā, aljannu sun sa wasu mutane ciwo kuma murmurɗe wasu
[Hotuna a shafi na 12]
Ayau aljannu suna sa wasu mutane su nuna karfi; suna razanadda wasu da dare, suna basu mafalkai masu ban-tsoro