Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • dg kashi 4 pp. 9-10
  • Sashe na 4—Allah Ya Sanas Da Mu Game Da Nufe-Nufensa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sashe na 4—Allah Ya Sanas Da Mu Game Da Nufe-Nufensa
  • Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ina Amsoshin?
  • Ƙyautar Allah
  • Littafi Mai Tsarki Sako Ne Daga Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
dg kashi 4 pp. 9-10

Sashe na 4—Allah Ya Sanas Da Mu Game Da Nufe-Nufensa

1, 2. Ina yadda muka sani cewa Allah yana bada amsoshi ga waɗanda suke biɗansa da gaske?

ALLAH mai-ƙauna lallai yana bayana nufe-nufensa ga waɗanda suke biɗansa da gaske. Yana ba yan-Adam masu bincike amsoshi ga tambayoyi irin su me yasa ya kyale shan wahala.

2 Littafi Mai-tsarki ya ce: “Idan ka biɗe [Allah], ya samu gareka.” “Akwai Allah na sama, wanda yakan Tone asirai.” “Lallai Ubangiji Jehovah ba zaya yi kome ba, sai shi bayana asirinsa ga bayinsa annabawa.”​—⁠1 Labarbaru 28:⁠9; Daniel 2:⁠28; Amos 3:⁠7.

Ina Amsoshin?

3. A ina ne zamu iske dalilin da yasa Allah ya kyale shan wahala?

3 Amsoshi ga tambayoyi irin su me yasa Allah ya kyale shan wahala kuma minene zaya yi game da shi yana cikin labarin da ya hure don amfaninmu. Wannan labarin ita ce Kalmarsa, Littafi Mai-tsarki. “Kowane Nassi hurare ne daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyaswa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adilci; domin mutumen Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.”​—⁠2 Timothawus 3:⁠16, 17.

4, 5. Me ya maida Littafi Mai-tsarki littafi na musamman?

4 Lallai fa Littafi Mai-tsarki littafi ne na musamman. Yana kunshe da labarin tarihin yan-Adam na sosai har kuma yana zuwa can baya wuce da halittar yan-Adam ma. Garau yake ma, gama annabce-annabcensa game da lokacinmu ne da kuma na nan gaba kurkusa.

5 Babu wata littafi da ke da irin ikon tabbacin tarihi haka. Alal misali, kaɗan ne kawai daga cikin rubuce-rubuce na musamman suke akwai. Amma akwai wasu rubuce-rubuce na Littafi Mai-tsarki, wasu sukutum suke: akwai misalin Nassosin Ibrananci 6,000 na (littattafai 39 na “Tsofon Alkawali”) kuma misalin 13,000 na Nassosin Hellenanci na Kirista (littattafai 27 na “Sabon Alkawali”).

6. Me yasa zamu tabbata sarai cewa Littafi Mai-tsarki ayau daidai yake sosai kamar yadda yake lokacinda Allah ya hure shi?

6 Maɗaukakkin Allah, wanda ya hure Littafi Mai-tsarki, ya tabbatar da cewa an tsare gaskiyar waɗannan kofofin littattafan. Saboda haka, Littafi Mai-tsarki namu ayau daidai yake da huraren rubuce-rubuce na asalin. Wani al’amarin da ya taimaka mana mu yarda da wannan shine cewa wasu kofofin littattafan Nassosin Hellenanci na Kirista sun tafi can baya wajen shekaru ɗari daga asalin lokacin rubutunsu. Ƙalila daga cikin kofi-kofi na littattafan marubuta na duniya da suke akwai yau basu kai ko kusa da kwanakin mawallafansu na asali ba.

Ƙyautar Allah

7. Ina iyakar yadda an rarraba Littafi Mai-tsarki ko?

7 Littafi Mai-tsarki shine littafi da aka fi rarrabawa cikin dukan tarihi. An buga kofi-kofin wajen biliyan uku ko. Babu wani littafi da yawan bugunsa yana kusa da wannan. Kuma dukan Littafi Mai-tsarki, ko kuwa sashinsa, an riga an juya shi ko cikin harsuna sama da 2,000. Saboda haka an aza cewa kashi 98 bisa ɗari na jimillar duniya zasu iya kai ga samun Littafi Mai-tsarki.

8-10. Minene wasu dalilai da yasa Littafi Mai-tsarki ya cancanci bincikenmu?

8 Lallai fa littafi da ke da’awar zuwa daga Allah kuma yana da shaida na waje da na ciki game da gaskiyarta ya cancanci bincikewarmu.a Ya bayyana ma’anar rai, ma’anar yanayoyin duniya, da kuma abinda gaba ta ke riƙe da shi. Babu wani littafi da zai iya yin haka.

9 I fa, Littafi Mai-tsarki shine sadarwan Allah da iyalin yan-Adam. Ya jagabance rubutunsa ta wurin ikon aikinsa, ko kuwa ruhu, da yan-Adam 40 kuma da suke rubutun. Da haka Allah yana mana magana ta wurin Kalmarsa, Littafi Mai-tsarki. Manzo Bulus ya rubuto haka: “Sa’anda ku ka karɓi maganar jawabi daga garemu, watau maganar Allah ke nan, ku ka karɓe ta, ba kamar maganar mutane ba, amma, yadda ta ke hakika, maganar Allah.”​—⁠1 Tassalunikawa 2:⁠13.

10 Shugaban United States na 16, Abraham Lincoln, ya kira Littafi Mai-tsarki “ƙyauta mai-girma duka da Allah ya taɓa ba mutum . . . Gama in ban da shi da bamu san abinda ke daidai da kuma mumuna ba.” Saboda haka, minene wannan kyauta mai-girman ya gaya mana game da yadda shan wahala ya soma, kuma dalilin da yasa Allah ya kyale shi, kuma da abinda zaya yi game da shi?

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da gaskiyar Littafi Mai-tsarki fa, ka duba littafin nan The Bible​—⁠God’s Word or Man’s?, wanda Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., suka buga.

[Hoto a shafi na 10]

Littafi Mai-tsarki, hurare daga Allah, shine sadarwarsa da iyalin yan-Adam

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba