Sashe na 9—Yadda Muka Sani Muna Cikin “Kwanaki Na Ƙarshe”
1, 2. Ina yadda zamu iya sani ko muna cikin kwanaki na ƙarshe?
INA yadda zamu iya tabbata cewa muna rayuwa cikin lokacinda Mulkin Allah zai soma tasam ma shirin sarautar yan-Adam na yanzu? Ina yadda zamu iya sani cewa mun yi kusa ko sosai da lokacinda Allah zai kawo ƙarshe ga dukan mugunta da shan wahala?
2 Almajiran Yesu Kristi sun so su san waɗannan abubuwa. Sun tambaye shi “alamar” zuwansa cikin ikon Mulki da kuma na “ƙarshen wannan shirin abubuwa.” (Matta 24:3, New World Translation) Yesu ya amsa ta wurin ambata al’amura masu jijjiga duniya da yanayoyi waɗanda a haɗe zasu nuna cewa mutane sun shiga “lokaci na ƙarshe,” “kwanaki na ƙarshe” na wannan shirin abubuwa. (Daniel 11:40; 2 Timothawus 3:1) Ashe mun ga haɗaɗɗen alamar nan ko cikin wannan ƙarnin? I fa, mun gani ko, sosai ma!
Yaƙoƙin Duniya
3, 4. Ina yadda yaƙoƙin wannan ƙarnin sun yi daidai da annabcin Yesu?
3 Yesu ya annabta cewa “al’umma zata tasa ma al’umma, mulki kuma zata tasa ma mulki.” (Matta 24:7) A 1914 duniya ta shaƙu cikin wata yaƙi wadda ta shaidar shaƙuwar al’ummai da mulkoki a hanyar da ta bambanta ƙwarai da wata yaƙi da aka taɓa yi kafin wannan. Cikin shaida al’amarin nan fa, yan tarihi na lokacin sun ƙira shi Babbar Yaƙi. Ita ce na fari a dukan yaƙoƙi na tarihin, yaƙin duniya na fari. Misalin sojoji da yan-farin hula 20,000,000 suka yi hasarar rayukansu, fiye da wata yaƙi da ta rigaye wannan.
4 Yaƙin Duniya na I ya alamta somawar kwanaki na ƙarshe. Yesu ya ce wai wannan da wasu al’amura zasu zama “mafarin wahala” ne. (Matta 24:8) Hakan ya zama gaskiya, da shike Yaƙin Duniya na II ya kasance mafi muni, sojoji da yan-farin hula wajen 50,000,000 suka yi hasarar rayukansu. A cikin wannan ƙarni na 20, an kashe mutane ko sama da 100,000,000 a cikin yaƙoƙi, wannan ya ninke waɗanda aka kashe cikin shekaru 400 sau hudu da suka shige can duka! Dubi tabbacin laifin sarautar yan-Adam mai-girma fa!
Wasu Alamu
5-7. Ina wasu alamu da suke nuna cewa muna cikin kwanaki na ƙarshe?
5 Yesu ya daɗa wasu al’amura da zasu zo tare da kwanaki na ƙarshen: “Za a yi manyan raye-rayen duniya, wuri dabam dabam kuma yunwa da aloba [yaɗuwar aloba].” (Luka 21:11) Hakan ya jitu sarai da al’amura na 1914, kamar yadda an yi ta shaida wahaloli ko daga irin matsifun nan.
6 Manyan raye-rayen duniya aukuwa na kullum ne, wanda ke cin rayuka dayawa. Cutar Spanish influenza kaɗai ta kashe mutane wajen 20,000,000 bayan Yaƙin Duniya na I—wasu sun kimanta 30,000,000 ne ko kuwa fiye da haka ma. AIDS ta ci dubban ɗarurrukan rayuka ko kuma yana iya cin miliyoyi fiye da haka a nan gaba kurkusa. Kowace shekara miliyoyin mutane suna mutuwa daga ciwon zuciya, cancer, da kuma wasu cututtuka. Miliyoyin wasu kuma suna mutuwa irinta sannu sannu don yunwa. Babu shakka fa ‘mahayan Wahayi’ da yaƙoƙinsu, rashin abinci, da aloban cututtuka nasu sun yi ta kashe jimillar mai-girma na iyalin yan-Adam ko tun 1914.—Ru’ya ta Yohanna 6:3-8.
7 Yesu ma ya annabta yawaitawar aika laifi da ake shaida a cikin dukan ƙasashe ayau. Ya ce: “Saboda yawaita da mugunta zata yi kuma, ƙaunar yawancin mutane zata yi sanyi.”—Matta 24:12.
8. Ina yadda annabcin 2 Timothawus sura 3 ya yi daidai da lokacinmu?
8 Bugu kan ƙari, annabcin Littafi Mai-tsarki ya annabta rugugujjewar ɗabi’a da ke ko’ina a duniya yau: “Cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu zasu zo. Gama mutane zasu zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu girman kai, masu zagi, marasa bin iyaye, marasa godiya, marasa tsarki, marasa ƙauna irin ta tabi’a, masu baƙar zuciya, masu tsegumi, marasa kamewa, masu zafin hali, marasa son nagarta, masu cin amana, masu taurin kai, masu kumbura, ma-fiya son annishuwa da Allah; suna riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta . . . Miyagun mutane da masu-hila zasu daɗa mugunta gaba gaba.” (2 Timothawus 3:1-13) Dukan waɗannan sun zama gaskiya a idanunmu.
Wani Al’amari
9. Minene ya faru a sama da ya zama a lokaci ɗaya da somawar kwanaki na ƙarshe a nan duniya?
9 Da akwai wani al’amari kuma da ya auku wanda ke jawo yawaitawar shan wahala a cikin wannan ƙarni. A lokaci ɗaya da somawar kwanaki na ƙarshe a 1914 fa, wani abu ya faru da ya jefa mutane cikin haɗari mai-girma. Kamar yadda aka annabta cikin littafi na ƙarshe na Littafi Mai-tsarki, wai a lokacin: “Aka yi yaƙi cikin sama; Mikailu [Kristi cikin ikonsa na samaniya] da nasa mala’iku suna fita su yi gāba da dragon [Shaitan]; dragon kuma ya yi gāba tare da nasa mala’iku [aljannu]; basu rinjaya ba, ba a kuwa ƙara tarasda matsayinsu cikin sama ba. Aka jefas da babban dragon, tsofon macijin, shi wanda ana ce da shi Ibelis da Shaitan, mai-ruɗin dukan duniya; aka jefas da shi a duniya, aka jefas da mala’ikunsa kuma tare da shi.”—Ru’ya ta Yohanna 12:7-9.
10, 11. Ina yadda yan-Adam suka taɓu yayinda aka jefas da Shaitan da aljannunsa zuwa duniya?
10 Minene ya zama sakamakon haka ga iyalin yan-Adam? Annabcin ya ci gaba haka: “Kaiton duniya da teku, domin Shaitan ya sauƙo wajenku, hasala mai-girma kuma gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.” I fa, Shaitan ya sani cewa shirinsa yana kusance ƙarshenta, saboda haka yana yin iyakar abinda zai iya yi don ya juya yan-Adam cikin gāba da Allah kafin a hallakas da shi da duniyarsa. (Ru’ya ta Yohanna 12:12; 20:1-3) Ga fa yadda waɗannan halittun ruhun suke ƙyamamu domin ɓata amfanin son zuciya nasu! Dubi yadda yanayoyi sun zama na kaito fa a duniya ƙalƙashin tasirinsu, musamman tun 1914!
11 Ba abin mamaki ba ke nan cewa Yesu ya annabta haka game da lokacinmu: “Akan duniya al’ummai suna ciwon rai, sun ruɗe . . . mutane suna suma don tsoro, domin tsammanin al’amuran da ke auko ma duniya kuma.”—Luka 21:25, 26.
Ƙarshen Sarautar Yan-Adam da Aljannu ya Kusa
12. Wannene ɗaya daga cikin annabce-annabce na ƙarshe da zai cika kafin ƙarshen wannan shirin?
12 Ina yawan annabce-annabcen Littafi Mai-tsarki da suke akwai waɗanda zasu cika kafin Allah zai hallakas da wannan zamani? Kaɗan ne kawai! Ɗaya daga cikin na ƙarshen yana 1 Tassalonikawa 5:3 ne, wanda ya ce: “Yayinda suke zancen salama da kwanciyar rai, sai farat ɗaya bala’i tana bisansu.” (The New English Bible) Wannan ya nuna cewa ƙarshen wannan shirin zai soma “yayinda suke zancen ne.” Mara ganuwa ga duniya kuwa, hallakar zata faɗa a lokaci da ba za a zace ta ba, yayinda hankalin yan-Adam yana bisa salama da kwanciyar rai nasu da suke begensa.
13, 14. Wane lokaci mai-wuya ne Yesu ya annabta, kuma ina yadda zai ƙare?
13 Lokaci yana ƙarewa ga wannan duniya da ke ƙalƙashin tasirin Shaitan. Bada daɗewa ba zata zo ga ƙarshenta a lokaci mai-wuya wanda Yesu ya ce: “Gama sa’annan za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba daɗai.”—Matta 24:21.
14 Ƙarshen “ƙunci mai-girman” nan zai zama yaƙin Allah na Armageddon ne. Lokacinda annabi Daniel ya annabta ke nan sa’anda Allah zai “farfashe dukan waɗannan mulkokin ya cinye su.” Wannan zai nufa ƙarshen sarautancin yan-Adam na yancin kai daga Allah duka. Sa’annan fa sarautar Mulkinsa daga sama zai sarrafa dukan harƙoƙin yan-Adam. Kamar yadda Daniel ya annabta, ba za a sāke, bada ikon shugabanci ga “wata al’umma kuma.”—Daniel 2:44; Ru’ya ta Yohanna 16:14-16.
15. Minene zai faru ga tasirorin Shaitan da na aljannunsa?
15 A lokacin nan ma, dukan tasirin shaitan da na aljannu zasu yanke. Za a kawas da waɗannan halittun ruhu don kada su sāke “ruɗas da al’ummai kuma.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9; 20:1-3) An hukuntad da su ko ga mutuwa suna dai jiran hallakarsu. Dubi wartsakewa da wannan zai kasance ga mutane su yantu daga ƙyamamiyar tasirinsu!
Wa Zai Tsira? Wa Kuma Ba Zai Tsira Ba?
16-18. Wa zai tsira ma ƙarshen wannan shirin, wa kuma ba zai tsira ba?
16 Sa’anda aka zartas da hukuncin Allah akan wannan duniya, wa zai tsira? Wa kuma ba zai tsira ba? Littafi Mai-tsarki ya nuna cewa za a kāre waɗanda suke son sarautar Allah kuma zasu tsira. Waɗanda basu son sarautar Allah kuwa ba za a kāre su ba amma zasu hallaku tare da duniyar Shaitan.
17 Misalai 2:21, 22 ma ya ce: “Gama masu-adilci [waɗanda suke son sarautar Allah] zasu zauna cikin ƙasan, kamilai kuma zasu wanzu a cikinta. Amma za a datse miyagu [waɗanda basu son sarautar Allah] daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana.”
18 Zabura 37:10, 11 ma ya ce: “Gama in an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi . . . Amma masu-tawali’u zasu gāje ƙasan; zasu faranta zuciyassu kuma cikin yalwar salama.” Aya 29 ya daɗa haka: “Masu-adilci zasu gāje ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”
19. Wane galgaɗi ne ya kamata mu tuna da shi?
19 Ya kamata mu tuna da galgaɗi da ke Zabura 37:34, wanda ya ce: “Ka yi sauraro ga [“Jehovah,” NW ], ka kiyaye tafarkinsa, shi kuma zaya ɗaukaka ka ka gāje ƙasan. Lokacinda an datse miyagu, ka gani.” Ayoyi 37 da 38 sun ce: “Ka lura da kamili, ka duba kuma adili, gama ƙarshen wannan mutum salama ne. Zancen masu-zunubi fa, za a hallaka su gaba ɗaya; za a datse ƙarshen miyagu.”
20. Me yasa zamu ce waɗannan lokutta na motsa rai ne muke rayuwa a cikinsu yanzu?
20 Ga fa yadda yake abin ta’aziya, i fa, abin motsa rai ne a sani cewa Allah yana kulawa da gaske kuma cewa bada jimawa ba zaya kawo ƙarshe ga dukan mugunta da shan wahala! Dubi yadda yake abin motsa rai fa mu gane cewa muna rayuwa a lokaci na kusa da cikawar waɗannan annabce-annabce masu-girman!
[Hoto a shafi na 20]
Littafi Mai-tsarki ya annabta al’amura da zasu zama “alamar” kwanaki na ƙarshe
[Hoto a shafi na 22]
Bada jimawa ba, a Armageddon, za a datse waɗanda basu son sarautar Allah. Waɗanda suke son shi kuma zasu tsira zuwa cikin sabuwar duniya ta adilci