Duniyar Nan Za ta Tsira Kuwa?
Babu wata tsara da ta ji magana da yawa game da ƙarshen duniya kamar wannan. Mutane da yawa suna jin tsoro cewa duniya za ta zo ƙarshenta a yaƙin nukiliya. Wasu suna jin cewa gurɓata mahalli za ta halaka duniya. Har ila wasu suna damuwa cewa rikitaccen tattalin arziki zai kawo tarzoma tsakanin mutane.
Wannan Duniyar za ta zo ƙarshenta da gaske? Idan haka ne, me yake nufi? Duniya ta taɓa zuwan ƙarshenta ne a dā?
Duniya ta Ƙare—Wata Kuma ta Sake Ta
Hakika duniya ta taɓa ƙarewa. Yi la’akari da duniya wadda ta cika da mugunta a kwanakin Nuhu. Littafi Mai-Tsarki ya yi bayani: “Duniya wadda ta ke a sa’an nan, yayinda ruwa ya sha kanta, ta halaka.” Littafi Mai-Tsarki ya daɗa cewa: “[Allah] ba ya kuwa keɓe duniya ta dā ba, amma ya ceci Nuhu mai-shelan adalci, tare da waɗansu bakwai, sa’anda ya kawo rigyawa bisa duniya ta masu-fajirci.”—2 Bitrus 2:5; 3:6.
Ka lura da abin da ƙarshen wancan duniya take nufi da abin da ba ta nufa ba. Ba ta nufin ƙarshen ’yan Adam ba. Nuhu da iyalinsa sun tsira wa Rigyawa da ta ci dukan duniyar lokacin. Hakanan ma Duniya da sararin sama kyakkyawa su ma sun tsira. “Duniya ta masu-fajirci” ce ta shuɗe, mugun tsarin abubuwa.
A ƙarshe, da ’ya’yan Nuhu suka ƙaru, aka sake samun wata duniya. Wannan duniya ta biyu, ko kuma shirin abubuwa, ta wanzu har zuwa kwanakinmu. Tarihinta ya cika da yaƙi, yin laifi, da nuna ƙarfi. Me zai sami wannan duniyar? Za ta tsira kuwa?
Abin da Zai Sami Wannan Duniyar a Nan Gaba
Bayan ya faɗi cewa duniyar kwanakin Nuhu ta halaka, Littafi Mai-Tsarki ya ci gaba da ba da labari: “Amma sammai da su ke yanzu, da duniya kuma, bisa ga wannan magana kanta an tanaje su domin wuta.” (2 Bitrus 3:7) Hakika, yadda wani marubucin Littafi Mai-Tsarki ya yi bayani: “Duniya [wadda ke wanzuwa a yau] ma tana wucewa.”—1 Yohanna 2:17.
Littafi Mai-Tsarki ba ya nufin cewa duniya ta zahiri ko sararin sama za su wuce yadda waɗannan ba su wuce ba a kwanakin Nuhu. (Zabura 104:5) Maimakon haka, wannan duniyar, da ‘sammanta,’ ko kuma masu mulki a gwamnati a ƙarƙashin tasirin Shaiɗan, da ‘duniyarta’ ko kuma jam’iyyar ’yan Adam, za ta halaka kamar da wuta. (Yohanna 14:30; 2 Korinthiyawa 4:4) Wannan duniyar, ko kuwa tsarin abubuwa, za ta shuɗe kwata-kwata yadda waccan duniya kafin Rigyawa ta shuɗe. Yesu Kristi ma ya yi magana game da yanayi cikin “kwanakin Nuhu” da yake ba da misalin abubuwa da za su faru kafin ƙarshen wannan duniyar.—Matta 24:37-39.
A muhimmin hali, yayin da Yesu ya yi maganar kwanakin Nuhu, amsa ce ga tambayar manzanninsa: “Me ne kuma alamar zuwanka, da cikar zamani?” (Matta 24:3) Mabiyan Yesu sun san cewa wannan duniyar za ta ƙare. Wannan zato ya firgita su ne?
Akasarin haka, lokacin da Yesu ya kwatanta al’amura da za su auku kafin ƙarshen duniya, ya ƙarfafa su su yi murna ‘domin fansarsu ta kusa.’ (Luka 21:28) Hakika, fansa daga Shaiɗan da mugun tsarin abubuwansa zuwa sabuwar duniya ta salama!—2 Bitrus 3:13.
Amma yaushe ne wannan duniyar za ta ƙare? Wace “alama” Yesu ya bayar game da ‘zuwansa, da kuma ƙarshen duniya’?
“Alama”
Kalmar Hellenanci da aka juya ‘zuwa’ a nan ita ce pa·rou·siʹa kuma tana nufin “bayyanuwa,” wato, kasancewa a zahiri. Saboda haka idan an ga “alamar” ba ta nufin cewa Kristi zai zo jim kaɗan, amma tana nufin ya riga ya komo kuma yana bayyane. Tana nufin ya soma sarauta da ba a gani a sama kuma jim kaɗan zai kawo ƙarshen magabtansa.—Ru’ya ta Yohanna 12:7-12; Zabura 110:1, 2.
Yesu bai ba da aba guda kawai ta zama “alamar” ba. Ya kwatanta aukuwa da yanayin duniya da yawa. Duk waɗannan za su faru lokacin da marubutan Littafi Mai-Tsarki suka kira “kwanaki na ƙarshe.” (2 Timothawus 3:1-5; 2 Bitrus 3:3, 4) Yi la’akari da wasu abubuwa da Yesu ya annabta za su ba da alamar “kwanaki na ƙarshe.”
“Al’umma za ta tasa ma al’umma, mulki kuma za ya tasa ma mulki.” (Matta 24:7) Yaƙi a lokuttan zamani ya fi na dā yawa. Wani ɗan tarihi ya lura: “Yaƙin Duniya na Farko [kamawa daga shekara ta 1914] shi ne yaƙin da ‘dukan duniya ta yi’ na farko.” Amma dai, yaƙin duniya na biyu ya fi ɓarna. Yaƙi ya ci gaba da lalata duniya. Hakika, kalmomin Yesu sun sami cika a hanya ta ban mamaki!
“Za a yi yunwa.” (Matta 24:7) Bayan Yaƙin Duniya na I sai aka yi yunwa wadda wataƙila ba a taɓa irinta ba a duk tarihi. Ƙarancin abinci mai tsanani ya biyo bayan Yaƙin Duniya na II. Annoba ta rashin abinci mai-gina jiki ta shafi wajen kashi biyar bisa ɗari na jama’ar duniya, tana kashe yara miliyan 14 kowace shekara. Babu shakka, ana “yunwa”!
“Za a yi manyan raye-rayen duniya” (Luka 21:11) Matsakancin mutane da suke mutuwa a duk shekara tun daga 1914 daga raye-rayen ƙasa sun fi sau goman na ƙarnuka da suka shige. Ka ga wasu manya cikinsu: a shekara ta 1923, a Japan, kusan mutane 140,000 suka rasa rayukansu ko kuma suka ɓace; a 1920, a Sin, mutane 200,000 suka mutu; a 1939, a Turkiya, mutane 32,700 suka rasu; a 1970, a Peru mutane 66,800 suka mutu; da kuma a 1976, kusan mutane 240,000 (ko, in ji wasu majiya suka ce, 800,000) ne suka rasa rayukansu a Sin. Babu shakka, “manyan raye-rayen ƙasa” ne kuwa!
“Wuri dabam dabam kuma annoba.” (Luka 21:11) Nan da nan bayan Yaƙin Duniya na I, misalin mutane miliyan 21 suka mutu daga cutar da ake kira da Turanci Spanish flu. Science Digest ya ba da rahoto: “Cikin dukan tarihi ba a taɓa mutuwa mai tsanani na nan da nan haka ba.” Tun lokacin, ciwon zuciya, ciwon daji, ƙanjamau, da wasu annoba sun kashe ɗarurrukan miliyoyin mutane.
“Yawaita da Mugunta.” (Matta 24:12) Tun daga shekara ta 1914 an san duniyarmu da yin laifi da nuna ƙarfi. A wurare da yawa ba mai kwanciyar rai a tituna ko da rana ma. Da dare mutane sukan kulle kansu cikin daƙunansu da ƙofofin ƙarfe, suna tsoro su fita waje.
An ambata wasu abubuwa da yawa da za su faru cikin kwanaki na ƙarshe, kuma dukan waɗannan suna faruwa. Wannan yana nufi cewa ƙarshen duniya ta yi kusa. Amma, abin farin ciki ne cewa za a samu waɗanda za su tsira. Bayan ya faɗa cewa “duniya ma tana wucewa,” Littafi Mai-Tsarki ya yi alkawari: “Wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”—1 Yohanna 2:17.
Saboda haka, muna bukatar mu koyi nufin Allah kuma mu yi shi. Sa’annan za mu iya tsira wa ƙarshen wannan duniyar don mu more albarka cikin sabuwar duniya ta Allah har abada. Littafi Mai-Tsarki ya yi alkawarin cewa a lokacin: “Allah . . . za ya share dukan hawaye kuma daga idanun [mutane], mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.