Kasancewarmu A Faɗake Ya Fi Gaggawa Yanzu Da Dā
“Ku yi tsaro fa: gama ba ku sani ba cikin ko wace rana Ubangijinku ke zuwa.”—MATTA 24:42.
1, 2. Me ya nuna muna ƙarshen wannan zamani?
“FIYE da kome, yaƙi ne ya cika ƙarni na ashirin,” in ji mawallafi Bill Emmott. Ya yarda da cewa dukan tarihin ’yan Adam sun cika da wahalar yaƙi da kuma mugunta, sai ya daɗa haka: “Ƙarni na farko ba dabam yake ba, bambancin batun yawan wahalar ce kawai. Ƙarni ne wanda ya fara shaida faɗace-faɗace na dukan duniya . . . Ƙari ga haka ma, ya jawo faɗā ba ɗaya ba, amma ya jawo yaƙi biyu na dukan duniya.”
2 Yesu Kristi ne ya annabta yaƙe-yaƙe na ‘al’umma da take tayar wa al’umma, mulki kuma da take tayar wa mulki.’ Amma wannan fanni ɗaya ne kawai na ‘alamar bayyanuwar Kristi da kuma kammalawar zamani.’ A cikin wannan babban annabci, Yesu ya sake ambata yunwa, cuta, da kuma girgizar ƙasa. (Matta 24:3, 7, 8; Luka 21:6, 7, 10, 11) Waɗannan bala’i sun ƙaru sosai kuma sun yi tsanani. Muguntar mutum ta yi yawa, idan aka duba halinsa wurin Allah da kuma ’yan’uwansa ’yan Adam. Suƙuƙucewar ɗabi’a da kuma ƙaruwar yin laifi da mugunta suna ko’ina. Mutane sun zama masu son kuɗi maimakon Allah, yin annashuwa ta sha kansu. Dukan wannan na tabbatar da cewa muna zama cikin “miyagun zamanu.”—2 Timothawus 3:1-5.
3. Yaya ya kamata “alamun zamanu” su shafe mu?
3 Yaya kake ji game da yadda abubuwa suke ƙara muni a harkokin ’yan Adam? Mutane da yawa ba sa damuwa, har ma sun taurara game da wahalar aukuwa na wannan zamani. Mutanen duniya masu iko masu haziƙanci ba sa fahimtar ma’anar “alamun zamanu”; kuma shugabannin addini ba su yi ja-gora a wannan batun da kyau ba. (Matta 16:1-3) Amma Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi: “Ku yi tsaro fa: gama ba ku sani ba cikin ko wace rana Ubangijinku ke zuwa.” (Matta 24:42) A nan Yesu yana ƙarfafa mu ba kawai mu yi tsaro ba amma ‘mu ci gaba da tsaro.’ Dole mu kasance a faɗake kuma da ƙwazo idan za mu yi tsaro. Wannan ya bukaci fiye da fahimtawa kawai cewa muna zama cikin kwanaki na ƙarshe, kuma fiye da fahimta kawai cewa lokatai sun yi wuya. Dole ne mu kasance da tabbaci ƙwarai cewa “matuƙar dukan abu ta kusa.” (1 Bitrus 4:7) Ta hakan ne kawai yin tsaronmu zai kasance da gaggawa. Shi ya sa, tambayar da za mu yi tunani a kanta ita ce: ‘Menene zai taimake mu mu ƙarfafa tabbacinmu cewa ƙarshe ya kusa?’
4, 5. (a) Menene zai ƙarfafa tabbacinmu cewa ƙarshen wannan zamani ya kusa, kuma me ya sa? (b) Wane kamani guda ke tsakanin zamanin Nuhu da bayyanuwar Ɗan mutum?
4 Ka yi la’akari da yanayin da ke ruwan dare a dā cikin tarihin ’yan Adam—Rigyawa mai girma na zamanin Nuhu. Mutane mugaye ne sosai da har “abin ya ɓata ma [Jehovah] zuciya.” Ya ce: “Mutum wanda na halitta zan shafe shi daga fuskar ƙasa.” (Farawa 6:6, 7) Kuma ya yi haka nan. Da yake kwatanta lokacin da yanzu, Yesu ya ce: “Kamar yadda kwanakin Nuhu su ke, hakanan kuma bayyanuwar Ɗan mutum za ta zama.”—Matta 24:37.
5 Daidai ne a yi tsammanin cewa haka ne ma Jehovah yake ji game da duniya ta yanzu yadda ya ji game da duniyar can kafin Rigyawa. Tun da yake ya kawo ƙarshen duniya marasa ibada na zamanin Nuhu, lallai zai halaka muguwar duniya ta yau. Ya kamata yadda muka fahimci kwatanci sarai na lokacin da kuma zamaninmu ya ƙarfafa mu mu tabbata ƙarshen duniyar nan ta kusa. To, menene kamaninsu? Aƙalla muna da guda biyar. Na farko shi ne, an yi gargaɗi sarai game da halaka da take zuwa.
An Yi Gargaɗin “Al’amuran da ba a Gani ba Tukuna”
6. Menene Jehovah ya ƙuduri ya yi a zamanin Nuhu?
6 A zamanin Nuhu Jehovah ya faɗa haka: “Ruhuna ba za ya riƙa ja da mutum har abada ba, gama shi kuma nama ne: amma kwanakin ransa shekara ɗari da ashirin za su zama.” (Farawa 6:3) Wannan shelar Allah a shekara ta 2490 K.Z. ce, masomin ƙarshen duniya marar ibada. Ka yi tunanin abin da wannan yake nufi ga waɗanda suka rayu a lokacin! Shekara 120 ne kawai kuma Jehovah zai kawo “ruwan tufana a bisa duniya, domin a halaka dukan mai-rai, wanda ke da lumfashin rai a cikinsa, daga ƙarƙashin sama.”—Farawa 6:17.
7. (a) Menene Nuhu ya yi da ya ji gargaɗi game da Rigyawan? (b) Yaya ya kamata mu aika game da gargaɗin ƙarshen wannan zamani?
7 Da daɗewa aka yi wa Nuhu gargaɗin wannan bala’in, kuma cikin hikima ya yi amfani da lokacin ya yi shirin tsira. “Da aka faɗakarda shi a kan al’amuran da ba a gani ba tukuna,” manzo Bulus ya ce, “domin tsoro mai-ibada, sai [Nuhu] ya shirya jirgi domin ceton gidansa.” (Ibraniyawa 11:7) Mu kuma fa? Shekaru 90 sun wuce da ƙarshen wannan zamani ya soma a 1914. Hakika muna cikin “kwanaki na ƙarshe.” (Daniel 12:4) Ta yaya ya kamata mu aika ga gargaɗi da aka bayar? “Wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yohanna 2:17) To, yanzu ne lokaci na yin nufin Jehovah da azancin gaggawa.
8, 9. Wane gargaɗi ne Jehovah yake bayarwa a zamaninmu, kuma yaya ake shelarsa?
8 A zamanin yau, ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun koya daga huraren Nassosi cewa wannan zamani ya kai a halaka. Mun yarda da haka? Ka lura da abin da Yesu Kristi ya faɗa sarai: “Za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba daɗai.” (Matta 24:21) Yesu kuma ya ce zai zo shi Alƙali wanda Allah ya naɗa kuma za ya ware mutane yadda makiyayi yake ware tumaki daga awaki. Waɗanda aka ga ba su cancanta ba za su “tafi cikin hukunci na har abada: amma masu-adalci cikin rai na har abada.”—Matta 25:31-33, 46.
9 Jehovah yana jawo hankalin mutanensa ga waɗannan gargaɗi ta wurin tunasarwa ta abinci na ruhaniya daga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Matta 24:45-47) Ban da haka ma, ana ariritar kowacce al’umma, ƙabila, harshe, da kuma mutane su “ji tsoron Allah, [su] ba shi daraja; gama sa’ar hukuncinsa ta zo.” (Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7) Muhimmin abu cikin saƙon Mulkin da Shaidun Jehovah suke wa’azinsa shi ne gargaɗin cewa Mulkin Allah zai kawar da sarautar mutane. (Daniel 2:44) Bai kamata a yi wasa da wannan ba. Kullum Allah Mai Iko Duka yana cika maganarsa. (Ishaya 55:10, 11) Ya cika ta a zamanin Nuhu kuma zai yi haka a zamaninmu.—2 Bitrus 3:3-7.
Lalatar Jima’i ta Zama Ruwan Dare Gama Gari
10. Me za a iya cewa game da lalatar jima’i a zamanin Nuhu?
10 Zamaninmu ya yi daidai da wani fanni a zamanin Nuhu. Jehovah ya gargaɗe namiji da tamace na farko su “mamaye duniya” da irinsu, ta jima’i da Allah ya sa cikin tsarin aure. (Farawa 1:28) A zamanin Nuhu, mala’iku da suka yi rashin biyayya sun ɓata ’yan Adam da lalatar jima’i. Suka sauko duniya, suka canja siffarsu suka kwana da kyawawan mata, suka haifi ’ya’ya rabin mutum rabin aljani—Nephilim. (Farawa 6:2, 4) An kwatanta zunubin waɗannan lalatattun mala’ikun da lalatar Saduma da Gwamrata. (Yahuda 6, 7) Sakamakonsa shi ne, lalata ta cika ko’ina a zamanin.
11. Wane irin yanayi na ɗabi’a ya sa zamaninmu ya yi daidai da na Nuhu?
11 Yanayin ɗabi’a a yau kuma fa? A cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe, rayuwan mutane ta cika da tunanin jima’i. Ga yadda Bulus ya kwatanta irin waɗannan sarai cewa “sun wuce gaban su ji”; mutane da yawa sun ba da kansu ga “aika dukan ƙazanta tare da kwaɗayi.” (Afisawa 4:19) Hotunan tsirarun mutane, jima’i ba tare da aure ba, zalunci na jima’i a kan yara, da kuma ’yan daudu suna ko’ina. Wasu sun soma “karɓan sakamakon” ta wurin cuta da ake samu ta jima’i, ragargajewar rayuwar iyali, da kuma wasu matsaloli.—Romawa 1:26, 27.
12. Me ya sa ya kamata mu ƙi abin da bai da kyau?
12 A zamanin Nuhu, Jehovah ya sa Rigyawa mai yawa ta kawo ƙarshen duniya da ta cika da lalata. Kada mu manta cewa waɗannan kwanaki hakika sun yi daidai da na zamanin Nuhu. “Ƙunci mai-girma” da ke zuwa zai kawar da ‘fasikai, mazinata, masu luwaɗi, masu kwana da maza’ za a kawar da su daga duniya. (Matta 24:21; 1 Korinthiyawa 6:9, 10; Ru’ya ta Yohanna 21:8) Lallai abin gaggawa ne mu ƙi abin da bai da kyau mu guji yanayin da zai iya tura mu cikin lalata!—Zabura 97:10; 1 Korinthiyawa 6:18.
Duniya ta “Cika da Zalunci”
13. A zamanin Nuhu, me ya sa duniya ta “cika da zalunci”?
13 Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna wani hali na zamanin Nuhu, ya ce: “Duniya kuwa ta ɓāci a gaban Allah, duniya kuma ta cika da zalunci.” (Farawa 6:11) Mugunta ba sabuwar abu ba ce. Kayinu ɗan Adamu ya kashe ɗan’uwansa adali. (Farawa 4:8) Da yake nuna halin mugunta na zamaninsa, Lamech ya shirya waƙa na fahariyar yadda ya kashe wani matashi, cewa yana tsare kansa ne. (Farawa 4:23, 24) Abin da ya bambanta da na zamanin Nuhu shi ne yawan mugunta. Yayin da ’ya’yan Allah mala’iku suka auri mata a duniya kuma suka haifi ’ya’ya—Nephilim—mugunta ta ƙaru fiye da yadda aka sani. Littafi Mai Tsarki na New World Translation ya nuna cewa asalin kalmar Ibrananci da take nuni ga waɗannan ƙarfafan su ne ‘mafaɗā’—‘waɗanda suke sa wasu su fāɗi.’ (Farawa 6:4) Domin haka, duniya ta cika da “zalunci.” (Farawa 6:13) Ka yi tsammanin irin matsaloli da Nuhu ya fuskanta sa’ad da yake kula da iyalinsa cikin irin yanayin nan! Duk da haka, Nuhu ne ya kasance ‘mai adalci a gaban Jehovah cikin tsarar nan.’—Farawa 7:1.
14. Ta yaya duniya a yau ta “cika da zalunci”?
14 Zalunci ya kasance duk cikin tarihin ’yan Adam. Kamar yadda yake a zamanin Nuhu, lokacinmu ma ya shaida zalunci da girma ƙwarai. Sau da yawa muna ji game da zalunci cikin gida, ayyukan ta’addanci, kamfen na ƙarar da dangi, da kuma mutane da ake kashe su babu gaira. Ban da haka, sai kuma jini da ake zubawar a yaƙe-yaƙe. Duniya ta sake cika da zalunci. Me ya sa? Me ya jawo ƙaruwar zalunci? Amsar ta bayyana wani kamani na zamanin Nuhu.
15. (a) Menene ya daɗa ga ƙaruwar nuna ƙarfi a kwanakin ƙarshe? (b) Me za mu tabbata zai zama sakamakon?
15 Lokacin da aka kafa Mulkin Allah na Almasihu a sama a 1914, Sarki da aka naɗa, Yesu Kristi ya soma aiki na musamman. An fitar da Shaiɗan Iblis da kuma aljannunsa daga sama zuwa ƙasa. (Ru’ya ta Yohanna 12:9-12) Kafin Rigyawan, mala’iku masu rashin biyayya suka bar wajen zamansu a sama da son ransu; amma a zamanin yau, an tilasta musu su fita. Ban da haka ma, ba su da ikon su iya canja jikunansu su zo duniya don su yi lalata kuma ba. Saboda baƙin cikinsu, fushi, da kuma tsoron hukunci da ke zuwa kansu, suna shafan mutane da ƙungiyoyi don su aikata laifi a nuna rashin tausayi da mugunta mafi yawa da na zamanin Nuhu. Jehovah ya kawar da duniya da take kafin Rigyawan, bayan da mala’iku da suka yi rashin biyayya da ’ya’yansu sun cika ta da mugunta. Babu shakka, zai yi haka nan a zamaninmu! (Zabura 37:10) Amma, waɗanda suke a faɗake a yau sun sani cewa cetonsu ya kusa.
An Yi Shelar Saƙon
16, 17. Wane kamani na huɗu ne ke tsakanin zamanin Nuhu da namu?
16 Ana iya ganin darasi na huɗu da ya yi kama da zamanin yau da kuma duniya ta kafin Rigyawa cikin aikin da aka ba Nuhu ya yi. Nuhu ya gina babban jirgi. Shi ma ‘mai-shela’ ne. (2 Bitrus 2:5) Wane saƙo ya yi wa’azinsa? Lallai wa’azin da Nuhu ya yi zai haɗa da bukatar a tuba kuma faɗakar game da halaka mai zuwa. Yesu ya ce mutanen zamanin Nuhu “ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka.”—Matta 24:38, 39.
17 Haka nan ma, Shaidun Jehovah suna ci gaba da aikinsu na wa’azi da ƙwazo, saƙon Mulkin Allah da ake yi a dukan duniya. A kusan kowanne gefen duniya, mutane suna iya ji kuma karanta saƙon Mulkin a nasu yare. Jaridar Hasumiyar Tsaro, mai shelar Mulkin Jehovah ta kai sama da 25,000,000 da ake rarrabawa kuma ake bugawa cikin harsuna 140. Hakika, ana shelar Mulkin Allah a “cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai.” Sa’ad da aka gama aikin yadda Allah yake so, ƙarshen zai zo.—Matta 24:14.
18. Yaya za a kwatanta yadda mutane suke aikata ga aikin wa’azinmu da na yawancin mutane a zamanin Nuhu?
18 Domin rashin ruhaniya da kuma suƙuƙucewar ɗabi’a da ke kafin Rigyawa, ya kasance da sauƙi maƙwabta marasa bi su yi wa Nuhu da iyalinsa dariya, kuma su yi musu zargi da ba’a. Ƙarshen kuwa ya zo. Haka kuma, ‘masu-ba’a da ba’arsu’ za su yi yawa a kwanakin ƙarshe. Duk da haka, “ranar Ubangiji kamar ɓarawo za ta zo,” in ji Littafi Mai Tsarki. (2 Bitrus 3:3, 4, 10) Za ta zo a lokacin da aka ayana. Ba za ta makara ba. (Habakkuk 2:3) Abar hikima ce mu kasance a faɗake!
Kalilan ne Suka Tsira
19, 20. Wane kamani za mu iya samu tsakanin Rigyawa da kuma halakar wannan zamani?
19 Kamani da ke tsakanin zamanin Nuhu da zamaninmu ba kawar da muguntar mutane da kuma halaka su ne kawai ba. Tun da an sami waɗanda suka tsira wa Rigyawar, haka kuma za a sami waɗanda za su tsira wa ƙarshen wannan zamani. Waɗanda suka tsira wa Rigyawan masu tawali’u ne da ba su yi rayuwa irin na sauran mutane ba. Sun bi gargaɗin Allah kuma ware kansu daga muguwar duniya ta lokacin. “Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji,” in ji Littafi Mai Tsarki. “[Nuhu] marar-aibi ne cikin tsararakinsa.” (Farawa 6:8, 9) A cikin dukan mutane, iyali ɗaya, “mutane kima, watau masu-rai takwas, suka tsira ta wurin ruwa.” (1 Bitrus 3:20) Kuma Jehovah Allah ya ba su umurni yana cewa: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓanɓanya, kuma mamaye duniya.”—Farawa 9:1.
20 Kalmar Allah ta tabbatar da mu cewa “taro mai-girma” za su “fito daga cikin babban tsananin.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14) Mutane nawa ne cikin taro mai girman? Yesu kansa ma ya ce: “Ƙofa ƙunƙunta ce, hanya kuwa matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu samunta fa kaɗan ne.” (Matta 7:13, 14) Idan an gwada da biliyoyi da suke duniya a yau, waɗanda za su tsira daga babban tsananin kalilan ne. Amma za su iya samun irin gatar da aka ba wa waɗanda suka tsira wa Rigyawa. Ƙila waɗanda suka tsira za su iya haihuwa na ɗan lokaci cikin sabuwar jam’iyya ta duniya.—Ishaya 65:23.
“Ku Yi Tsaro Fa”
21, 22. (a) Ta yaya bincika labarin Rigyawan nan ta amfane ka? (b) Menene jigon shekarar 2004, kuma me ya sa ya kamata mu bi shawarar da ya bayar?
21 Ko da yake Rigyawan ta daɗe kafin zamaninmu, tana ba mu gargaɗi sosai da ba za mu ƙyale ba. (Romawa 15:4) Kamani da ke tsakanin zamanin Nuhu da namu ya kamata su sa mu daɗa ganin muhimmancin abin da ke faruwa kuma sa mu kasance a faɗake game da zuwan Yesu zuwan ɓarawo don ya hukunta duniya.
22 A yau, Yesu Kristi yana ja-gorar aikin gini mai girma na ruhaniya. Domin kwanciyar rai da kuma ceto da zai yi wa masu bauta ta gaskiya, da akwai aljanna ta ruhaniya. (2 Korinthiyawa 12:3, 4) Domin mu tsira daga babban tsananin, dole ne mu kasance cikin wannan aljanna. Duniyar Shaiɗan tana kewaye da aljannar nan ta ruhaniya, a shirye suke su kama wani da yake gyangyaɗi a ruhaniya. Ya kamata mu “yi tsaro” kuma mu kasance a shirye domin ranar Jehovah.—Matta 24:42, 44.
Ka Tuna?
• Wane gargaɗi Yesu ya bayar game da zuwansa?
• Da menene Yesu ya gwada lokacin zuwansa?
• A waɗanne hanyoyi ne zamaninmu ya yi kama da na Nuhu?
• Yaya ya kamata yin tunani a kan kamani da ke zamanin Nuhu ya shafi azancinmu?
[Bayanin da ke shafi na 10]
Jigon shekarar 2004 shi ne: “Ku yi tsaro fa . . . Ku zama da shiri.”—Matta 24:42, 44.
[Hoto a shafi na 7]
Nuhu ya yi biyayya da gargaɗin Allah. Haka muke yi mu ma?
[Hotuna a shafuffuka na 8, 9]
“Kamar yadda kwanakin Nuhu su ke, hakanan kuma bayyanuwar Ɗan mutum za ta zama”