Za Mu Bi Jehobah Allahnmu
“Mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.”—Mika 4:5.
1. In ya zo ga ɗabi’a, yaya yanayin yake a zamanin Nuhu, ta yaya Nuhu ya bambanta?
ANUHU ne mutum na farko da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki cewa ya yi tafiya da Allah. Nuhu ne na biyu. Labarin ya gaya mana cewa: “Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah.” (Farawa 6:9) A zamanin Nuhu, mutane galibi sun daina bauta ta gaskiya. Yanayin ya ƙara munanta da mala’iku marasa aminci suka yi jima’i da bai dace ba da mata kuma suka haifi ’ya’ya da ake kira Ƙattai, “manya manyan mutane,” ko kuma “shahararru” na wancan zamani. Shi ya sa duniya ta cika da mugunta! (Farawa 6:2, 4, 11) Duk da haka, Nuhu ya kasance mai aminci da kuma “mai wa’azin adalci.” (2 Bitrus 2:5) Sa’ad da Allah ya umurce shi ya sassaƙa jirgi don ceton rai, Nuhu ya yi biyayya “ya yi dukan abin da Allah ya umarce shi.” (Farawa 6:22) Hakika, Nuhu ya yi tafiya da Allah.
2, 3. Wane misali mai kyau ne Nuhu ya kafa mana a yau?
2 Bulus ya saka Nuhu a jerinsa na shaidu masu aminci sa’ad da ya rubuta: “Ta bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al’amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magajin adalcin Allah, wanda ke samuwa ta bangaskiya.” (Ibraniyawa 11:7) Wannan misali ne mafi kyau! Da yake ya tabbata cewa kalmomin Jehobah za su cika, Nuhu ya ba da lokaci, kuzari, da dukiya domin ya cika umurnin Allah. Hakanan ma, mutane da yawa a yau suna ƙin zarafin wannan duniya kuma suna ba da lokacinsu, kuzari da dukiya a yin biyayya da umurnin Jehobah. Yana da kyau a yabi bangaskiyarsu kuma zai sa su ceci kansu da kuma wasu.—Luka 16:9; 1 Timoti 4:16.
3 Babu shakka, ya yi wa Nuhu da iyalinsa da kuma Anuhu kakan Nuhu da aka tattauna a talifi da ya shige wuya, su ba da gaskiya. A zamanin Nuhu kamar na Anuhu, masu bauta ta gaskiya kaɗan ne—mutane takwas ne kawai suka kasance da aminci kuma suka tsira wa Tsufana. Nuhu ya yi wa’azin adalci a duniya ta mugunta da lalata. Ƙari ga haka, shi da iyalinsa suna gina babban jirgi don rigyawa na dukan duniya, ko da yake ba wanda ya taɓa ganin irin wannan Tsufana. Wannan abin mamaki ne ga waɗanda suke kallon su.
4. Wane laifi na mutanen zamanin Nuhu Yesu ya nuna?
4 Abin mamaki shi ne cewa sa’ad da Yesu ya yi maganar zamanin Nuhu, bai yi maganar mugunta, addinin ƙarya ko kuma lalata, ko da waɗannan abubuwa zunubai ne masu tsanani. Yesu ya yi maganar yadda mutanen suka ƙi yin biyayya da gargaɗin da aka bayar. Ya ce ana “ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi.” Laifi ne a ci, a sha, a yi aure kuma a aurar? Suna rayuwa ne kawai “irinta yau da kullum”! Amma ruwan tsufana na zuwa, kuma Nuhu na wa’azin adalci. Kalmominsa da halinsa ya kamata ya zama gargaɗi a gare su. Duk da haka “ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su.”—Matiyu 24:38, 39.
5. Waɗanne halaye ne Nuhu da iyalinsa suke bukata?
5 Idan mun yi tunanin lokacin can, za mu ga hikimar Nuhu a tafarkin rayuwa da ya bi. Amma, a kwanaki kafin Rigyawa, mutum yana bukatar gaba gaɗi don ya bambanta da sauran mutanen. Nuhu da iyalinsa suna da tabbaci sosai da ya sa suka gina wannan babban jirgi kuma suka cika shi da dabbobi dabam dabam. Shin wasu cikin amintattun wani lokaci suna jin kamar kada a gansu kuma su yi rayuwa irinta “yau da kullum”? Ko idan sun yi irin wannan tunani, ba su kasala ba a amincinsu. Bayan shekaru da yawa fiye da yadda kowannenmu zai jimre a wannan zamanin, bangaskiyar Nuhu ta kai ga cetonsa daga rigyawa. Amma, Jehobah ya zartar da hukunci a kan dukan waɗanda suke rayuwa irinta “yau da kullum” kuma ba su lura da ma’anar yanayin da suke ciki lokacin ba.
Mugunta ta Sake Damun ’Yan Adam
6. Wane yanayi har ila ya kasance bayan Rigyawan?
6 Bayan da ruwan Rigyawan ya bushe, mutane suka soma sabuwar rayuwa. Amma, mutane har ila ajizai ne kuma “zace-zacen zuciyar mutum” ya ci gaba da kasance “mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa.” (Farawa 8:21) Ban da haka, ko da aljanu ba sa iya canja jikinsu zuwa na ’yan adam, sun ci gaba da aiki sosai. Duniyar mutane marasa ibada ta nuna cewa “tana hannun Mugun,” kuma kamar yadda yake a yau masu bauta ta gaskiya suna yaƙi da “kissoshin Iblis.”—1 Yahaya 5:19; Afisawa 6:11, 12.
7. Ta yaya mugunta ta yaɗu a duniya bayan Rigyawa?
7 Bayan Rigyawa, daga lokacin Nimrod duniya kuma ta sake cika da mugunta ta ’yan adam. Domin ƙaruwar mutane da kuma cin gaba na fasaha, wannan mugunta ta yaɗu da shigewar lokaci. Da farko ana amfani da takobi da māshi, baka da kibiya, da kuma karusa. A baya baya nan, aka soma amfani da alkadariyya da kuma igwa, a farkon ƙarni na 20 kuma bindiga da wasu manyan makaman yaƙi. A Yaƙin Duniya na I aka fito da makamai masu ban tsoro, kamarsu jirgin sama, tanki, igwa mai ruwa, da kuma hayaƙi mai guba. A wannan yaƙi, waɗannan makamai sun kashe miliyoyin mutane. Ba su sani ba ne zai kasance haka? A’a.
8. Ta yaya Wahayin Yahaya 6:1-4 suke cikawa?
8 A shekara ta 1914 aka naɗa Yesu Sarkin Mulkin Allah a samaniya, kuma “ranar Ubangiji” ta soma. (Wahayin Yahaya 1:10) A wahayin da ke littafin Wahayin Yahaya, an ga Yesu Sarki yana kan farin doki ya yi nasara. Wasu mahayan doki suka biyo shi, kowanne na wakiltan annoba dabam a kan ’yan adam. Ɗaya cikinsu mahayin jan doki ne, kuma aka ba shi izini “ya ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma bashi babban takobi.” (Wahayin Yahaya 6:1-4) Wannan doki da mahayinsa alamar yaƙe-yaƙe ne, kuma babban takobi na nuna halakar yaƙe-yaƙe na zamani da makamansu masu ƙarfi. Waɗannan makaman a yau sun haɗa da makaman nukiliya, kowanne na iya kashe dubban mutane; rokoki na iya kai waɗannan makaman dubban miloli; da kuma makamai masu yaɗa cututtuka masu ƙarfi da za su iya kashe mutane da yawa.
Mun Mai da Hankali ga Kashedin Jehobah
9. Ta yaya duniyar yau take idan aka gwada ta da wadda ta kasance kafin Rigyawa?
9 A zamanin Nuhu, Jehobah ya halaka mutane domin yawan muguntan miyagu da ke tallafa wa Ƙattai. Yau kuma fa? Duniya ta kai zamanin Nuhu mugunta ne? Hakika. Ƙari ga haka, yadda yake a zamanin Nuhu mutane a yau suna rayuwarsu ta kullum, suna ƙoƙari su yi rayuwa “irinta yau da kullum” suna ƙin yin biyayya ga kashedi da ake shelarsa. (Luka 17:26, 27) Akwai dalilin shakka cewa Jehobah zai sake halaka ’yan adam kuma? A’a.
10. (a) Wane kashedi ake bayarwa a kai a kai cikin annabcin Littafi Mai Tsarki? (b) Wane tafarki ne mai kyau a yau?
10 Shekaru da yawa kafin Tsufana, Anuhu ya yi annabci cewa za a yi halaka a zamaninmu. (Yahuza 14, 15) Yesu ma ya yi maganar “matsananciyar wahala” mai zuwa. (Matiyu 24:21) Wasu annabawa sun yi kashedi game da lokacin. (Ezekiyel 38:18-23; Daniyel 12:1; Yowel 2:31, 32) A littafin Wahayin Yahaya, mun ga kwatanci na wannan halaka na ƙarshe. (Wahayin Yahaya 19:11-21) Ya kamata ɗaɗɗaya mu yi koyi da Nuhu kuma mu zama masu wa’azin adalci da ƙwazo. Muna lura da kashedin Jehobah kuma mu taimaki maƙwabtanmu su yi hakan. Shi ya sa kamar Nuhu muke bin Allah. Hakika, wajibi ne wanda yake son rai ya ci gaba da bin Allah. Ta yaya za mu yi hakan domin matsi da muke fuskanta kowace rana? Muna bukatar mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi a cikar ƙudurin Allah.—Ibraniyawa 11:6.
Ka Ci Gaba da Bin Allah a Lokacin Wahala
11. A wace hanya ce muke yin koyi da Kiristoci na ƙarni na farko?
11 A ƙarni na farko, an kira shafaffu Kiristoci masu bin “wannan hanya.” (Ayyukan Manzanni 9:2) Rayuwarsu ta dangana a kan bangaskiya ga Jehobah da Yesu Kristi. Sun bi hanyar da Shugabansu ya bi. A yau, Kiristoci masu aminci suna hakan.
12. Menene ya faru bayan da Yesu ya ciyar da jama’a ta mu’ujiza?
12 An ga muhimmancin bangaskiya a wani abin da ya faru lokacin hidimar Yesu. A wani lokaci, Yesu ta mu’ujiza ya ciyar da mutane 5,000. Mutanen sun yi mamaki da kuma farin ciki. Amma ka lura da abin da ya faru kuma. “Da jama’a suka ga mu’ujizar da ya yi, suka ce, ‘Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya!’ Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen, shi kaɗai.” (Yahaya 6:10-15) Cikin daren nan ya koma wani waje. Abin da Yesu ya yi mai yiwuwa ya sa mutane da yawa sun yi sanyin gwiwa. Ballantana ma ya nuna cewa ya isa zama sarki kuma yana da ikon ya biya bukatun mutane. Amma lokacin da Jehobah zai naɗa shi Sarki bai yi ba tukuna. Ban da haka ma, Mulkin Yesu zai zama na samaniya ba na duniya ba.
13, 14. Wane ra’ayi mutane da yawa suka nuna, kuma yaya aka gwada bangaskiyarsu?
13 Duk da haka, taron sun bi Yesu suka same shi a “hayin tekun” yadda Yahaya ya faɗa. Me ya sa suka bi shi bayan ya kauce don kada su naɗa shi sarki? Da yawa cikinsu sun nuna suna da ra’ayin ’yan adam, sun yi nanaci a kan abubuwa na biyan bukata da Jehobah ya yi tanadinsa a jeji a zamanin Musa. Abin da suke nufi shi ne cewa Yesu ya ci gaba da yi musu tanadi. Da yake Yesu ya gane muradinsu da bai dace ba, ya soma koya musu gaskiya ta ruhaniya da za ta gyara tunaninsu. (Yahaya 6:17, 24, 25, 30, 31, 35-40) Wasu suka yi gunaguni game da shi, musamman lokacin da ya ba da wannan misalin: “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku. Duk wanda ke cin naman jikina, ya ke kuma shan jinina, yana da rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar ƙarshe.”—Yahaya 6:53, 54.
14 Sau da yawa kwatancin Yesu na motsa mutane su nuna ko da gaske suna son su bi Allah. Abin da wannan kwatanci ya yi ke nan. Ya sa su nuna ra’ayinsu. Labarin ya ce: “Da yawa daga cikin almajiransa suka ce, ‘Wannan magana mai wuya ce, wa zai iya jinta?’ ” Yesu ya yi bayani cewa ya kamata su fahimci cewa kalmominsa suna da ma’ana ta ruhaniya. Ya ce: “Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai.” Har ila mutane da yawa ba su saurara ba, kuma labarin ya ce: “Kan wannan da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba.”—Yahaya 6:60, 63, 66.
15. Wane ra’ayi da ya dace wasu cikin mabiyan Yesu suke da shi?
15 Amma ba dukan almajiran Yesu suka aikata hakan ba. Hakika, almajiran masu aminci ba su fahimci abin da Yesu ya ce ba. Duk da haka sun kasance da aminci a gare shi. Bitrus ɗaya cikin waɗannan almajirai masu aminci, ya furta yadda duka da suka rage suke ji sa’ad da ya ce: “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai ke da maganar rai madawwami.” (Yahaya 6:68) Wannan halin misali ne mai kyau sosai!
16. Ta yaya za a iya gwada mu, wane ra’ayi da ya dace ya kamata mu nuna?
16 A yau za a iya gwada mu yadda aka gwada waɗannan almajirai na farko. Muna iya sanyin gwiwa domin alkawuran Jehobah ba sa cika da sauri yadda muka so ba. Muna iya jin cewa bayani na Nassosi cikin littattafanmu na Littafi Mai Tsarki suna da wuyan fahimta. Halin ’yan’uwa Kirista masu bi suna iya sa mu sanyin gwiwa. Zai dace ne mu daina bin Allah don irin waɗannan dalilai da kuma wasu? Sam! Almajirai da suka daina bin Yesu sun nuna suna da ra’ayi na ’yan adam. Dole ne mu kauce wa yin hakan.
Ba Ma “Cikin Waɗanda Ke Ja da Baya”
17. Ta yaya za a taimake mu mu ci gaba da bin Allah?
17 Manzo Bulus ya rubuta: “Kowane Nassi hurarre na Allah ne.” (2 Timoti 3:16) A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya gaya mana sarai: “Ga hanyan nan, ku bi ta.” (Ishaya 30:21) Yin biyayya da Kalmar Allah na taimaka mana mu ‘mai da hankali ƙwarai ga zamanmu.’ (Afisawa 5:15) Nazarin Littafi Mai Tsarki da bimbini a kan abin da muka koya na taimakonmu mu ci gaba da “bin gaskiya.” (3 Yahaya 3) Hakika, yadda Yesu ya ce, “ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome.” Matabbaciyar ja-gora da za mu bi ita ce ja-gora ta ruhaniya, wadda za a samu ta Kalmar Jehobah, ruhunsa, da kuma ƙungiyarsa.
18. (a) Wane abu marar kyau ne wasu suka yi? (b) Wane irin bangaskiya ne za mu koya?
18 A yau, marasa wadatar zuci sau da yawa suna komawa ga neman abin duniya domin ra’ayi na ’yan adam ko kuma tsammani da ba su cika ba. Da yake sun manta da yanayin gaggawa da muke ciki, ba sa ganin bukatar “su zauna a faɗake,” sukan zaɓi su biɗi makasudi na kansu maimakon sa abubuwa na Mulki a gaba. (Matiyu 24:42) Bin irin wannan hanyan ba hikima ba ce. Ka lura da kalmomin Bulus: “Mu ba cikin waɗanda ke ja da baya su halaka muke ba, mu a cikin masu bangaskiya muke, mai kai mu ga ceton rayukanmu.” (Ibraniyawa 10:39) Kamar Anuhu da Nuhu muna zama a lokacin wahala, amma kamar su, muna da gatar bin Allah. Idan muka yi hakan, muna da tabbaci cewa za mu ga cikan alkawuran Jehobah, za a kawar da mugunta, za a yi sabuwar duniya ta adalci. Lallai wannan bege ne mai girma!
19. Ta yaya ne Mika ya kwatanta tafarkin masu bauta ta gaskiya?
19 Annabi Mika da aka hura ya ce game da al’ummai na duniya cewa za su ‘bi gumakansu.’ Sai ya yi magana game da kansa da kuma wasu amintattu masu bauta, ya ce: “Mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.” (Mika 4:5) Idan ƙudurinka irin na Mika ne, ka kusaci Jehobah ko yaya ne wahalar lokacin da muke ciki zai zama. (Yakubu 4:8) Bari fatar kowannenmu ya zama na bin Jehobah Allahnmu yanzu da kuma har abada abadin!
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya zamanin Nuhu da yau suka yi kama?
• Wane tafarki ne Nuhu da iyalinsa suka bi, kuma yaya za mu yi koyi da bangaskiyarsu?
• Wane ra’ayi da bai dace ba wasu cikin mabiyan Yesu suka nuna?
• Menene Kiristoci na gaskiya suka ƙuduri aniyar yi?
[Hotuna a shafi na 28]
Kamar yadda yake a zamanin Nuhu, mutane a yau sun shagala da ayyukansu na kullum
[Hoto a shafi na 29]
Mu masu shelar Mulki, ba ma “cikin waɗanda ke ja da baya”