Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • we pp. 20-25
  • How Can Others Help?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • How Can Others Help?
  • Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abinda Zaka Yi . . .
  • Abinda Kada ka Yi . . .
  • ”Ku Yi Kuka Tare da Masu-Kuka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Yadda Za Ka Sami Ta’aziya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • How Can I Live With My Grief?
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • Taimako Daga “Allah na Haƙuri da na Ta’aziyya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
we pp. 20-25

Ina Yadda Wasu Zasu Taimaka?

“IDAN akwai wani abinda zan yi, ka gaya mani.” Abinda yawancinmu kan faɗa ga wani aboki ko kuwa ɗangi da aka yi masa rasuwa. I fa, da gaskiya ne muke nufin abinda muka faɗa. Zamu yi kome don mu taimaka. Amma ashe wanda aka yi masa rasuwa yakan ƙira mu ya kuma ce: “Da akwai abinda zaka iya taimake ni da shi”? Ba haka ba. Lallai fa, muna bukata mu ɗauki wani mataki idan da gaske muna son mu taimaka da kuma ta’azantar da wani wanda yake baƙinciki.

Wani karin maganar Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Magana a kan kari tana kāma da tuntuwa na zinariya cikin kwanduna na azurfa.” (Misalai 15:23; 25:11) Da akwai hikima cikin sanin abinda zaka faɗa da abinda ba zaka faɗa ba, abinda zaka yi da kuma abinda ba zaka yi ba. Ga fa wasu shawarwarai na Nassi kaɗan da wasu da aka yi masu rasuwa sun iske yana taimakawa.

Abinda Zaka Yi . . .

Saurara: Ka yi “hanzarin ji,” in ji Yaƙub 1:19. Ɗaya cikin abubuwan taimako na musamman da zaka iya yi shine ka yi rabon jin zafin wanda aka yi masa rasuwa ta wurin saurarawa. Wasu da aka yi masu rasuwa su a so su yi magana game da ƙaunatattu nasu da suke rashinsa, game da hatsari ko kuwa rashin lafiyar da ya jawo mutuwar, ko kuwa jiye-jiyensu tun mutuwar. Saboda haka ka tambaya: “Zaka so yin magana game da shi?” Bari su zaɓa. Da yake tuna da lokacinda ubansa ya mutu fa, wani saurayi ya ce: “Ya taimake ni ƙwarai yayinda wasu suna tambaya minene ya faru sa’annan kuma suna saurarawa da gaske.” Ka saurara da hanƙuri da kuma jin tausayi ba tare da jin cewa zaka tanadar da amsa ko kuwa maganinsa ba. Ka kyalle su su furta dukan abinda suke son yin rabonsa.

Ka tanadar da tabbaci: Ka tabbatar da su cewa sun yi dukan abinda ya yiwu (ko kuwa kome da ka san gaskiya ne da kuma mai-kyau). Ka tabbatar da su cewa abinda suke ji—baƙinciki, fushi, jin laifi, ko kuwa wani jiye-jiye dai—ba bakon abu ba ne sam. Ka yi masu magana game da wasu da sun shaida makamancin abu kuma kayadda shi ko. Irin “zantattuka masu-daɗi” kamar “lafiya ne ga ƙasussuwa,” in ji Misalai 16:24.—1 Tassalunikawa 5:11, 14.

Ka kasance a yalwace: Ka kasance a yalwace, ba kawai a kwanaki na farko sa’anda abokai da ɗangogi dayawa suke a kewaye ba, amma har ma watanni bayan haka yayinda wasu sun komo yanayin harƙoƙinsu ko. A ta haka fa zaka tabbatas da kanka ‘aboki na ƙwarai,’ irin wanda ke tsayawa a gefen aboki a lokacin ‘wahala.’ (Misalai 17:17) “Abokanmu sun tabbatar da cewa mun cika yininmu da ayuka domin kada mu badda lokaci ainun a gida mu kaɗai,” yadda Teresea ta bayyana, wadda ɗanta ya mutu a hatsarin mota. “Hakan ya taimake mu jurewa da jin wofinci da muke da shi.” Shekaru bayan haka, ranakun tunawa na kowace shekara, kamar tunawa da ran ɗaurin aure ko kuwa na mutuwar, zai iya zama lokacin baƙinciki ne ga waɗanda suke da rai. Me yasa ba zaka sa alama bisa ran nan cikin kalanda ba domin yayinda ran nan ya kai, ka iya bada kanka a yalwace, idan ya yiwu, domin goyon baya mai-juyayi?

Ka ɗauki matakai da suka dace: Ashe da akwai aika da ake bukatar yi? Ashe ana bukatar wani ya lura da yaran? Ashe abokai da kuma ɗangogi da sun ziyarta suna bukatar wurin kwanciya? A kwanan nan waɗanda aka yi masu rasuwa sau dayawa sukan damu ƙwarai har da ba zasu ko san abinda suke bukatar yi da gaske ba, balle kuma su gaya ma wasu yadda zasu taimaka. Saboda haka idan ka raɓe bukata na gaske, kada ka jira a ce ka yi; ka ɗauki mataki. (1 Korinthiyawa 10:24; gwada da 1 Yohanna 3:17, 18.) Wata mace wadda mijinta ya mutu ko ta gaya haka: “Mutane dayawa sun ce, ‘Idan da akwai wani abinda zan yi, gaya mani.’ Amma wata abokiya ba ta tambaya ba. Ta dai shiga cikin daƙin kwanciya, kuma naɗe zanēn gadon, kuma ta wanke zannuwan da ya mutu bisansu sarai. Wata kuma ta ɗauki bokiti, ruwa, da kayan shara kuma share mashimfiɗi da mijina ya yi amāi a kai. Makoni kaɗan nan gaba, ɗaya cikin dattiɓai na ikklisiyar ya zo da kayakin aikinsa kuma ya ce, ‘Na sani cewa da akwai wani abinda ke bukatar gyara. Minene?’ Dubi yadda na ji daɗin mutumen nan da ya gyara ƙofana da ke lilo bisa ƙusa ɗaya da kuma kafa wani na’urar lantarki!”—Gwada da Yaƙub 1:27.

Ka nuna karamci: “Kada a manta a nuna [karamci, NW],” Littafi Mai-Tsarki ya tunas da mu. (Ibraniyawa 13:2) Musamman ma ya kamata mu tuna nuna karamci ga waɗanda suke baƙinciki. Maimakon irin gayyatowa “ganin dama” fa, ka bada rana da kuma lokaci. Idan suka ƙi da shi fa, kada ka fidda rai nan da nan. Mai-yiwuwa suna bukatar wani ƙarfafa na hankali. Watakila sun ƙi da gayyatowarka domin suna tsoron kasa sarrafa jiye-jiyensu a gaban wasu ne. Ko kuwa su a kasance da jin laifi yayinda suke jin daɗin abinci da kuma cuɗanya a irin lokuttan nan. Ka tuna da mace mai-karamcin nan Lidiya da aka ambata cikin Littafi Mai-Tsarki. Bayan an gayyace shi zuwa gidanta, Luka ya ce, “Har ta i mamu.”—Ayukan Manzanni 16:15.

Ka zama da hanƙuri da ganewa: Kada ka kasance da mamaki ainun ga abinda waɗanda aka yi masu rasuwa su a faɗa a farko. Ka tuna, mai-yiwuwa suna jin fushi da kuma jin laifi. Idan aka furta fushin jiye-jiye gareka, zai bukaci fahimi da hanƙuri a gefenka don kada ka rama. “Ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa,” haka Littafi Mai-Tsarki ya yaba.—Kolossiyawa 3:12, 13.

Ka rubuta wasiƙa: Abinda ana yawan manta da shi fa shine rubutawar wasiƙar ta’azantarwa ko kuwa katin mai-rubutun nuna tausayi. Minene amfaninsa? Cindy ta amsa haka, wadda ta yi rashin uwatta daga ciwon cancer: “Wata abokiya ta rubuto mani wata kyawawar wasiƙa. Wadda ya taimake ni ƙwarai domin na iya karanta shi sau da sau.” Irin wasiƙar nan ko kuwa katin ƙarfafawar zai iya kasance da “kalmomi kaɗan kawai,” amma ya kamata ya nuna abinda ke cikin zuciyarka. (Ibraniyawa 13:22, NW) Zai iya karanta haka cewa ka damu kuma kana tunani na musamman game da wanda ya mutun, ko kuwa zai iya nuna yadda wanda ya mutun ya taɓe rayuwanka.

Ka yi addu’a tare da su: Kada ka ƙasƙantar da darajar addu’o’inka tare da kuma ga waɗanda aka yi masu rasuwa. Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Addu’ar mai-adilci tana da iko dayawa.” (Yaƙub 5:16) Alal misali, su ji kana addu’a a maimakonsu zai iya taimaka wajen kawas da munanan jiye-jiye na jin laifi.—Gwada da Yaƙub 5:13-15.

Abinda Kada ka Yi . . .

Kada ka gudu domin ba ka san abinda zaka faɗi ko yi ba: ‘Na tabbata suna bukatar kasance kaɗai yanzu,’ zamu iya gaya ma kanmu haka. Amma watakila gaskiyar al’amari shine cewa muna gudu domin muna tsoron gaya ko kuwa yin wani abinda bai dace ba. Amma dai, idan abokai, ɗangogi, ko kuwa yan’uwa masu-bi suka gudu daga wanda aka yi masa rasuwa zai sa shi zama da jin kaɗaici, wanda zai daɗa ga jin zafinsa. Ka tuna, kalmomi da ayuka na alheri sau dayawa sune masu sauƙi. (Afisawa 4:32) Kasancewarka kawai ma zai iya zama ƙarfafawa ne. (Gwada da Ayukan Manzanni 28:15.) Tunawa da ranar da ɗiyarta ta rasu fa, Teresea ta ce: “Cikin sa’a guda kawai, fagen asibitin ta ciku da abokanmu; dukan dattiɓai da matayensu sun hallarta. Wasu cikin matan ba a gama kitsonsu ko ba, wasu kuma cikin tufafin aikinsu. Sun yas da kome kuma taho nan da nan. Yawancinsu sun gaya mana cewa basu san abinda zasu faɗa ba, amma kasancewarsu a wurin shine muhimmin abu.”

Kada ka tsananta masu su denna yin baƙinciki: ‘Ke kuwa, ke kuwa, kada ki yi kuka,’ zamu so faɗin haka. Amma zai iya fi kyau a kyalle hawayen ta zuba. “Ina jin muhimmin abu ne a kyalle waɗanda aka yi masu rasuwa su nuna jiye-jiyensu sarai kuma don su hushe,” in ji Katherine, wadda take tunawa da mutuwar mijinta. Ka ƙi da halin gaya ma wasu yadda ya kamata su ji. Kuma kada ka zace cewa sai ka ɓoye jiye-jiyenka don ka tsare su. Maimakon haka, “yi kuka tare da masu-kuka,” in ji Littafi Mai-Tsarki.—Romawa 12:15.

Kada ka yi hanzarin basu shawarar rabuwa da riguna ko kuwa wasu kayan wanda ya mutu kafin su kansu su yi shirin haka: Zamu iya jin cewa zai fi kyau su kawas da abubuwa masu tadda tunani domin kila zasu tsawonta baƙinciki. Amma furcin cewa “Abinda ba a gani, ba a tuna da shi” baya aikawa a nan. Wanda aka yi masa rasuwa zai bukaci mantawa da mataccen da sannu sannu. Tuna da yadda Littafi Mai-Tsarki ya kwatanta martanin uban iyali Yakubu yayinda an sa shi gaskata da cewa wata bisa ta kashe ɗansa ƙarami Yusufu. Bayan an nuna ma Yakubu doguwar taguwar Yusufu mai-jike da jini fa, ya “yi makokin ɗansa kwanaki dayawa. Dukan ’ya’yansa maza da mata suka tashi garin su yi masa ta’aziya; amma ya ƙi ta’azantuwa.”—Farawa 37:31-35.

Kada ka ce wai, ‘Zaki haife wata jariri’: “Na ji fushin mutane da suke gaya mani zan haife wata jariri,” in ji wata uwa da ta yi rashin jaririnta a mutuwa. Mai-yiwuwa ne cewa suna da nufi mai-kyau, amma ga iyaye masu baƙinciki, kalmomi da ke furta cewa za a iya sāke yaro da ya mutun yakan yi ‘tsoki kamar takobi.’ (Misalai 12:18) Yaro ɗaya ba zai iya sāke wani ba. Don me? Domin kowanne dabam ne.

Kada ka guje ambaci wanda ya mutun babu kāri: “Mutane dayawa basu son ambaci sunan ɗana Jimmy ko kuwa yi magana game da shi,” in ji wata uwa. “Lallai ne cewa na fusata kaɗan yayinda wasu sun yi haka.” Saboda haka kada ka canza taɗin yayinda aka ambace sunan wanda ya mutun. Ka tambaye mutumen ko yana son yin magana game da ƙaunatacce nasa. (Gwada da Ayuba 1:18, 19 da 10:1.) Wasu da aka yi masu rasuwa suna jin daɗin jin abokai suna magana game da ingantai na musamman da ya jawo wanda ya mutun garesu.—Gwada da Ayukan Manzanni 9:36-39.

Kada ka yi hanzarin faɗan cewa, ‘Shi ya fi kyau’: Yin ƙoƙarin iske wani abu mai-kyau game da wanda ya mutu ba kullum ne ‘yake ta’azantar da masu makoki’ waɗanda suke baƙinciki ba. (1 Tassalunikawa 5:14) Yayinda take tuna da lokacinda uwarta ta mutu, wata matashiya ta ce: “Wasu zasu ce, ‘Bata shan wahala’ ko kuwa, ‘Haba yanzu ta huta.’ Amma bana son in ji haka.” Irin furcin nan zai iya nufa ga waɗanda suke da rai ɗin cewa bai kamata su yi baƙinciki ko kuwa cewa rashin ba wani abu mai-girma ba ne. Amma dai, suna jin baƙinciki ainun domin sun yi rashin ƙaunatacce nasu ainun.

Zai iya zama da kyau kada ka ce, ‘Na san yadda ka ke ji’: Ka sani da gaske? Alal misali, yana yiwuwa kuwa ka san yadda mahaifi yakan ji yayinda yaronsa ya mutu idan kai kanka ba ka shaida rashin nan kanka ba? Kuma ko idan ka shaida haka ko, ka gane cewa wasu ba zasu ji daidai kamar yadda ka ji ba. (Gwada da Makoki 1:12.) A wata sassa kuma, idan ya dace, zai iya zama da kyau ka furta yadda ka kayad da jiye-jiyenka a mutuwar ƙaunataccenka. Wata mace wadda aka kashe ɗiyarta ta iske shi abin bege ne yayinda uwar wata yarinya da ta mutu ta gaya yadda ta dawo cikin zama kamar yadda take. Ta ce: “Uwar yarinya da ta mutun ba ta soma labarin da ‘Na san yadda ki ke ji’ ba. Ita dai ta gaya yadda abubuwa suke mata kuma ta bari in yi nuni garesu.”

Taimaka ma wanda aka yi masa rasuwa yana bukatar juyayi, ganewa, da kuma ƙauna mai-girma a gefenka. Kada ka jira wanda aka yi masa rasuwar ya zo wurin ka. Kada ka dai ce, “Idan da akwai wani abu zan . . .” Ka nemi “wani abin” nan kai kanka, sai kuma ka ɗauki mataki da ya dace.

Da akwai tambayoyi kaɗan da sun rage: Me kuma za a ce game da begen Littafi Mai-Tsarki na tashin matattu? Minene zai nufa gareka da ƙaunattatu naka da sun mutu ko? Ina yadda zamu tabbata sarai cewa bege ne da za a dogara da shi?

Tambayoyin Yin Bimbini

  • Me yasa abin taimako ne ka yi rabon zafin wanda aka yi masa rasuwa ta wurin saurarawa?

  • Ina wasu abubuwa da zamu iya yi don mu ta’azantar da wani wanda ke baƙinciki?

  • Minene ya kamata mu guje faɗi ko kuwa yi ga wani wanda ke makoki?

Taimaka ma Yara su Jure da Mutuwa

Yayinda mutuwa ta buge iyali, iyaye da kuma wasu ɗangogi da abokai sau dayawa basu sanin abinda zasu faɗa ko kuwa yi don taimaka ma yara su jure da abinda ya faru. Duk da haka, yara suna bukatar manya su taimake su jure da mutuwa. Ka yi la’akari da wasu tambayoyi da ake yawan yi game da taimake yara su gane abinda mutuwa yake.

Ina yadda fa zaka bayyana mutuwa ga yara? Muhimmin abu ne ka bayyana al’amura a furci mai-sauƙi. Ka bayyana shi da gaskiya kuma. Kada ka jinkirta ka yi amfani da kalmomi na gaske, kamar “matacce” da “mutuwa.” Alal misali, zaka iya zauna da yaron, ka sa shi cikin dantsenka, kuma ka ce: “Wani mumunan abu ya auku ko. Baba ya kamu da cuta mai-tsanani da ba mutane dayawa ne suke shaidawa ba [ko kuwa wani abinda ka sani gaskiya ne], kuma ya mutu. Ba laifin wani ba ne da ya mutu. Zamu rasa shi sosai domin muna ƙaunarsa, kuma ya ƙaunacemu.” Amma dai, zai iya zama abin taimako ka bayyana cewa yaron ko kuwa mahaifinsa da ke da rai wanda ke ciwo ba zai mutu kawai domin haka ba.

Ka ƙarfafa yin tambayoyinsu: ‘Minene mutuwa?’ su a iya tambaya. Zaka iya amsa shi haka: “‘Matacce’ yana nufin cewa jikin ya denna rayuwa kuma ba zai iya yin wasu abubuwa kuma kamar yadda ya saɓa yi ba—ba zai iya magana, gani, ko kuwa ji, kuma ba zai zama da jin wani abu ba.” Mahaifi wanda ya gaskata da alkawalin Littafi Mai-Tsarki na tashin matattu zai yi amfani da wannan zarafi don ya bayyana cewa Jehovah Allah yana tuna da wanda ya mutun kuma zai iya komo da shi zuwa rai nan gaba cikin Aljanna ta duniya. (Luka 23:43; Yohanna 5:28, 29)—Duba sashe na “Tabbataccen Bege Ga Matattu.”

Ashe da akwai wani abinda bai kamata ka faɗi ba? Baya taimakawa a ce wai wanda ya mutun ya yi wata doguwar tafiya. Jin yashed wa abin damuwa ne na ƙwarai ga yaro, musamman ma lokacinda mahaifi ne ya mutu. Faɗin wai wanda ya mutun ya yi tafiya ne zai iya ƙarfafa jin yashed wa na yaron kuma zai iya tunani haka: ‘Kaka mace ta tafi, kuma ko ban kwana ma bata yi ba!’ Ka maida hankali, kai ma, da ƙananan yara, game da faɗin cewa wanda ya mutun ya je barci. Yara suna ɗauka abubuwa a zahiri ne. Idan fa yaro ya daidaita barci da mutuwa, to tsoron hawan gado da dare zai auku.

Ya kamata yara su hallarci hidimomin jana’iza? Ya kamata iyaye su yi lura da jiye-jiyen yaran. Idan ba su a son su tafi, kada ku tsananta masu ko kuwa sa su zama da jin laifin ƙin tafiya. Idan suna son su tafi, ku ba su daki dakin abinda za a yi a wurin, haɗe da zancen akwati da kuma ko za a buɗe shi ko kuwa rufe shi. Ku bayyana, ma, cewa zasu iya ganin mutane dayawa da suna kuka domin suna baƙinciki. Kuma, bari su yi tambayoyi. Kuma ka tabbatar da su cewa zasu iya bar wurin idan sun bukaci haka.

Ina yadda yara suke mayas da martani ga mutuwa? Sau dayawa dai yara suna jin cewa sune dalilin mutuwar wani ƙaunatacce. Domin yaro mai-yiwuwa ya taɓa jin fushin wanda ya mutun, yaron zai iya gaskata cewa tunani mai-zafi da kalmomi su a iya jawo mutuwan. Zaku so ku bada ta’aziya: ‘Tunaninka da kalmominka ba sune suke sa mutane ciwo ba, kuma basu sa mutane mutuwa.’ Matashi yana bukatar irin tabbataswan nan sau da sau.

Ya kamata ka ɓoye baƙincikinka daga yara? Yin kuka a gaban yara daidai ne da kuma lafiyayyen abu ne. Balle ma, kusan baya yiwuwa ka ɓoye jiye-jiyenka daga yara sarai sarai; kamar dai suna raɓewa ƙwarai kuma sau dayawa sukan gano cewa wani abu ya ƙuskura. Kasance da gaskiya game da baƙincikinka zai sanas da su cewa daidai ne yin baƙinciki da kuma nuna jiye-jiyenka a wasu lokutta.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba