Taimako Daga “Allah na Haƙuri da na Ta’aziyya”
SHEKARU 2,000 da suka shige, marubucin Littafi Mai Tsarki Bulus ya kira Jehobah “Allah na haƙuri da na ta’aziyya.” (Romawa 15:5) Tun da yake Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbacin cewa Jehobah ba ya canjawa, muna da tabbaci cewa Allah yana ba da ta’aziyya ga waɗanda suke bauta masa. (Yaƙub 1:17) Babu shakka, Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Jehobah yana ba da ta’aziyya a hanyoyi masu yawa ga waɗanda suke bukata. Waɗanne ne wasu cikin hanyoyin? Allah yana ƙarfafa waɗanda suka yi addu’a don ya taimake su. Kuma yana motsa Kiristoci na gaskiya su ba da ta’aziyya ga ’yan’uwa masu bi. Kuma Jehobah ya yi tanadin labarai masu daɗaɗa zuciya a cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, musamman da suke ƙarfafa waɗanda suke makoki domin sun yi rashin ɗa ko ’yar su. Bari mu tattauna waɗannan hanyoyi uku na ta’aziyya, ɗaya bayan ɗaya.
“Ubangiji Kuma Ya Ji Shi”
Sarki Dauda ya rubuta game da Mahaliccinmu, Jehobah: “Ku al’ummai, ku dogara gareshi kowane loto, ku zazzage zuciyarku a gabansa: Allah mafaka ne a garemu.” (Zabura 62:8) Me ya sa Dauda ke da irin wannan tabbacin a Jehobah? Sa’ad da yake magana game da kansa, Dauda ya rubuta: “Wannan talaka ya yi kuka, Ubangiji kuma ya ji shi, Ya cece shi daga dukan wahalansa.” (Zabura 34:6) A cikin dukan yanayi na baƙin ciki da ya fuskanta, Dauda ya yi addu’a ga Allah don ya taimake shi a kowane lokaci, kuma Jehobah ya taimaka masa. Daga abubuwan da ya fuskanta, Dauda ya sani cewa Allah zai taimaka masa ya jimre.
Iyaye da suke makoki suna bukatar su sani cewa Jehobah zai taimaka masu, kamar yadda ya taimaka wa Dauda. Suna iya yin addu’a ga “Mai-jin addu’a,” da tabbacin cewa zai taimaka masu. (Zabura 65:2) “A yawancin lokaci, na ji kamar ba zan rayu ba ba tare da ɗa na ba, kuma na roƙi Jehobah ya ƙarfafa ni. A kowane lokaci yana ƙarfafa ni na ci gaba da rayuwa,” in ji William. Idan kai ma ka yi addu’a ga Jehobah cikin bangaskiya, Allah na samaniya mai girma zai ƙarfafa ka. Jehobah Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙoƙarin su bauta masa: “Ni Ubangiji Allahnka zan riƙe hannun damanka, in ce maka, Kada ka ji tsoro, ni taimake ka.”—Ishaya 41:13.
Taimako Daga Abokan Kirki
Waɗanda suka yi rashin ɗa ko ’ya suna bukatar lokaci don su yi kuka kuma su daidaita yadda suke ji. Amma, guje wa mutane na dogon lokaci ba shi da kyau. Misalai 18:1 ta ce “wanda ya ware kansa” na iya yi wa kansa lahani. Saboda haka, waɗanda suke baƙin ciki su mai da hankali kada su ware kansu daga mutane.
Abokai masu tsoron Allah suna iya ba da taimako mai muhimmanci ga waɗanda suke baƙin ciki. Misalai 17:17 ta ce: “Aboki kullayaumi ƙauna ya ke yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.” Lucy ta sami ta’aziyya daga abokai na kirki bayan ta yi rashin ɗanta. Sa’ad da take magana game da ’yan’uwa masu bi da ke cikin ikilisiya, ta ce: “Ziyararsu ta taimaka sosai, duk da cewa a wasu lokatai ba sa magana mai yawa. Wata ƙawata ta ziyarce ni a ranakun da nike gida ni kaɗai. Ta san cewa ina gida ina kuka, kuma ta kan biya ta taya ni kuka. Wata kuma tana yi mini waya kullum don ta ƙarfafa ni. Ƙari ga haka, wasu suna gayyatarmu zuwa gidansu don mu ci abinci tare, kuma sun ci gaba da yin haka.”
Ko da yake baƙin cikin da iyaye suke yi sa’ad da suka yi rashin ɗansu ko ’yarsu ba ya wucewa da wuri, yin addu’a ga Allah da kuma tarayya da Kiristoci na gaskiya zai kawo ta’aziyya ga waɗanda suke baƙin ciki. Iyaye Kiristoci masu yawa da suka yi rashin ɗansu ko ’yarsu sun shaida cewa Jehobah yana tare da su. Hakika, Jehobah “yana warkadda masu-karyayyar zuciya, Yana ɗaure miyakunsu.”—Zabura 147:3.
Labaran Littafi Mai Tsarki da ke Ba da Ta’aziyya
Ƙari ga addu’a da kuma tarayya mai ƙarfafawa, rubutacciyar Kalmar Allah tana ba da ta’aziyya ga waɗanda suke kuka. Labaran da suke cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Yesu yana da cikakken muradi da kuma ikon kawar da baƙin cikin iyaye ta wajen ta da mamacin. Irin waɗannan labaran suna ba da ta’aziyya ga waɗanda suke baƙin ciki. Bari mu tattauna irin waɗannan labaran biyu.
Luka sura 7 ta kwatanta abin da ya faru sa’ad da Yesu ya haɗu da wasu a birnin Nayin da za su jana’ida. Mutanen suna kan hanyarsu ta binne wani ɗa tilo na wata gwauruwa. Aya ta 13 ta ce: “Sa’anda Ubangiji ya gan ta, ya yi juyayi bisa gareta, ya ce mata, Kada ki yi kuka.”
Mutane kalilan ne za su iya gaya wa uwar da ake gab da binne ɗanta ta daina kuka. Me ya sa Yesu ya faɗi haka? Domin ya san cewa baƙin cikin uwar yana gab da ƙarewa. Labarin ya ci gaba da cewa: “[Yesu] ya kusato ya taɓa ana’ashi: masu-ɗauka suka tsaya. Ya ce, Saurayi, ina ce maka, Ka tashi. Matacen ya tashi zaune, ya soma yin magana. Ya bada shi ga uwatasa.” (Luka 7:14, 15) A wannan lokacin, wataƙila uwar ta sake fashewa da kuka, amma na farin ciki.
A wani lokacin kuma, wani mutum mai suna Yayirus ya je wurin Yesu don ya taimaka wa ɗiyarsa ’yar shekara sha biyu da take mugun rashin lafiya. Ba da daɗewa ba, aka zo aka sanar da shi cewa ɗiyarsa ta mutu. Wannan labarin ya sa Yayirus baƙin ciki sosai, amma Yesu ya ce masa: “Kada ka ji tsoro, sai dai ka bada gaskiya.” A gidan Yayirus, Yesu ya je inda gawar yarinyar take. Ya kama hannun yarinyar, ya ce: “Yarinya, ina ce maki, Ki tashi.” Me ya faru? “Nan da nan yarinya ta tashi, ta soma tafiya.” Menene iyayenta suka yi? Sun cika da “mamaki nan da nan da mamaki mai-girma.” Sa’ad da Yayirus da matarsa suka rungumi ɗiyarsu, sun cika da farin ciki. Abin kamar dai mafarki suke yi.—Markus 5:22-24, 35-43.
Irin waɗannan labaran Littafi Mai Tsarki game da tashin yara daga matattu, suna nuna wa iyayen da suke baƙin ciki a yau abin da zai faru a nan gaba. Yesu ya ce: “Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito.” (Yohanna 5:28, 29) Jehobah ya yi alkawari cewa Ɗansa zai ba da rai ga waɗanda suka mutu. Miliyoyin yaran da suka rasu “za su ji muryatasa” sa’ad da ya ce masu: ‘Ina ce maku, ku tashi.’ Waɗannan yaran za su soma magana da kuma tafiya. Kuma kamar Yayirus da matarsa, iyayen waɗannan yaran za su tsaya kusa da juna cike da “mamaki nan da nan da mamaki mai-girma.”
Idan ka yi rashin ɗa ko ɗiya, ka san cewa Jehobah zai iya canja baƙin cikinka zuwa farin ciki ta wajen tashin matattu. Domin ka amfana daga wannan bege mai girma, ka yi biyayya ga gargaɗin mai zabura: “Ku biɗi Ubangiji da ikonsa; Ku biɗi fuskatasa tuttur. Ku tuna da al’ajibansa da ya yi; Da alamominsa.” (Zabura 105:4, 5) Hakika, ka bauta wa Jehobah Allah na gaskiya, kuma ka bauta ma shi a hanyar da ta dace.
Wane sakamako ne za ka samu yanzu idan ka “biɗi Ubangiji”? Za ka sami ƙarfafa ta wajen yin addu’a ga Allah, za ka sami ta’aziyya daga abokai Kiristoci na gaskiya da suka damu da kai, kuma za ka sami ƙarfafa ta wajen yin nazarin Kalmar Allah. Bugu da ƙari, a nan gaba, za ka shaida ayyuka masu ban ‘al’ajabi da alamomi’ da Jehobah zai yi don kai da yaro ko yarinyar ka da ya ko ta rasu ku amfana har abada.
[Akwati a shafi na 4]
“Ki Kawo Matar da ta yi Rashin ’Ya’yanta Biyu”
Kehinde da matarsa Bintu, waɗanda Shaidun Jehobah ne ’yan Nijeriya, sun yi rashin ’ya’yansu biyu a haɗarin mota. Tun daga wannan lokacin, suna ta baƙin ciki domin wannan mugun rashi da suka yi. Duk da haka, dogarar da suka yi ga Jehobah ta ci gaba da ƙarfafa su, kuma sun ci gaba da sanar da saƙon bege da ke cikin Littafi Mai Tsarki ga maƙwabtansu.
Wasu sun ga kwanciyar rai da kuma ƙarfafa da Kehinde da matarsa Bintu suka nuna. Wata rana wata matar Ukoli ta ce wa ɗaya daga cikin ƙawayen Bintu: “Ki kawo matar da ta yi rashin ’ya’yanta biyu a lokaci guda, wadda kuma har yanzu tana wa’azin saƙon Littafi Mai Tsarki. Ina son in san abin da ya ba ta ƙarfin jimrewa.” Sa’ad da Bintu ta isa gidan matar, matar Ukoli ta ce mata: “Ina son in san dalilin da ya sa kike wa’azi game da Allahn da ya kashe ’ya’yan ki. Allah ya kashe ɗiyata tilo ta. Kuma tun daga lokacin ba na sha’awar bauta wa Allah.” Bintu ta yi amfani da Littafi Mai Tsarki ta bayyana mata dalilin da ya sa mutane suke mutuwa da kuma dalilin da ya sa za mu iya kasancewa da tabbataccen bege cewa waɗanda muke ƙauna da suka mutu za su tashi daga matattu.—Ayukan Manzanni 24:15; Romawa 5:12.
Bayan haka, matar Ukoli ta ce: “A dā ina tunanin cewa Allah ne ke kashe mutane. Amma, yanzu na san gaskiya.” Ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah don ta ƙara koyon alkawuran Allah.
[Akwati a shafi na 5]
‘Ina Son in Taimaka, Amma Ban San Abin da Zan Yi Ba’
Sa’ad da iyaye da ’yan’uwan yaro ko yarinyar da ya ko ta rasu suke baƙin ciki, abokansu na iya rasa abin da za su yi. Suna son su taimaka wa iyalin, amma suna tsoron cewa faɗi da kuma yin abin da bai dace ba zai iya ƙara musu baƙin cikinsu. Ga wasu shawarwari ga waɗanda suke iya tunanin cewa, ‘Ina son in taimaka, amma ban san abin da zan yi ba.’
❖ Kada ka guji waɗanda suka yi rashi domin ba ka san abin da za ka ce ko yi ba. Zuwanka wurin zai ƙarfafa su. Yana yi maka wuya ka yi tunanin abin da za ka faɗa? Runguma da kuma cewa “yaya aka ji da haƙuri” zai sa su san cewa ka damu da su. Kana tsoron cewa idan ka soma kuka, hakan zai daɗa baƙin cikinsu? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi kuka tare da masu-kuka.” (Romawa 12:15) Kukanka ya nuna cewa kai ma kana baƙin ciki, kuma hakan zai ƙarfafa su.
❖ Ka ɗauki mataki. Za ka iya shirya wa iyalin abincin da za su ci? Za ka iya wanke masu kwanonin da suka yi datti? Za ka iya je masu aike-aike? Kada ka ce, “Ku sanar da ni idan kuna bukatar wani abu.” Ko da da gaske kake, ga yawancin iyayen da suke baƙin ciki waɗannan kalaman suna nufin cewa ba za ka iya taimaka masu ba. Maimakon haka, ka tambaye su “Menene zan yi maku don in taimaka?” bayan haka, sai ka yi abin da suka ce ka yi. Amma ka guje wa shiga wuraren da bai kamata ka shiga a cikin gidansu ko kuwa sanin asirinsu.
❖ Kada ka ce, “Na san yadda kuke ji.” Yadda kowane mutum ke ji sa’ad da wanda yake ƙauna ya mutu ya bambanta. Ko da kai ma ka taɓa rashin ɗa ko ’ya, ba ka san ainihin yadda wasu suke ji a wannan lokacin ba.
❖ Lokaci mai tsawo zai wuce kafin iyalin ta soma murmurewa. Ka ci gaba da taimaka musu iya ƙoƙarinka. Sa’ad da iyali ta yi rashi, mutane suna mai da masu hankali sosai a wannan lokacin, amma suna bukatar taimakon da ya wuce hakan. Ku ci gaba da kula da bukatunsu a makonni da watanni masu zuwa.a
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani a kan yadda za a taimaka wa waɗanda suka yi rashin ɗa ko ’ya, ka duba babin nan “Ina Yadda Wasu Zasu Taimaka?” shafuffuka 20-24 na mujallar nan Yayinda Wani Wanda Ka Ke Ƙauna ya Mutu, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.