Jimrewa da Rasuwar Abokiyar Aurenka
LITTAFI MAI TSARKI ya bayyana dalla-dalla cewa: Ya kamata mai gida ya “yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.” Kuma dukansu su cika hakkinsu a matsayin “nama ɗaya.” (Afis. 5:33; Far. 2:23, 24) Da shigewar lokaci, dangantaka da kuma ƙaunar da ke tsakanin ma’aurata sukan yi ƙarfi sosai. Za mu iya kwatanta wannan dangantakar da jijiyoyin itatuwa biyu da suke girma kusa da juna. Da shigewar lokaci, soyayyar da ke tsakanin ma’aurata takan yi ƙarfi sosai.
Amma, idan mijin ko matar ta rasu fa? To, wannan dangantaka mai ƙarfi ta zo ƙarshe ke nan. Gwauruwar ko kuma gwauron yakan yi baƙin ciki ya kuma kaɗaita ko kuma ya yi fushi. Sa’ad da wata mata mai suna Daniella ta kai shekaru 58 da aure, ta san da mutane da yawa waɗanda matansu ko mazajensu suka rasu.a Amma sa’ad da mai gidanta ya rasu, ta ce: “Ban taɓa sanin cewa haka yanayin yake ba. Ba za ka iya sanin yanayin ba sai ka fuskanci hakan.”
BAƘIN CIKIN DA KE DA WUYAR DAINAWA
Wasu masu bincike sun ce babu abin da ke kawo baƙin ciki kamar idan miji ko mata ta rasu. Kuma mutane da yawa da suka fuskanci wannan yanayin sun yarda da hakan. Mijin Millie ya rasu shekaru da yawa da suka shige. Sa’ad da take kwatanta rayuwarta a matsayin gwauruwa, ta ce, “Na ji kamar na gurgunce.” Ta yi wannan furucin ne wajen kwatanta yadda ta ji lokacin da mijinta da suka yi shekaru 25 da aure ya rasu.
Wata mata mai suna Susan takan ji cewa matan da suke baƙin ciki na dogon lokaci don rasuwar mijinsu suna wuce gona da iri. Amma sai mijinta da suka zauna shekaru 38 tare ya rasu. Shekaru ashirin yanzu da rasuwar mijinta, duk da haka ta ce, “Ina kewarsa sosai a kowace rana.” Takan zub da hawaye domin tana kewarsa sosai.
Littafi Mai Tsarki ya ce baƙin cikin rasuwar miji ko mata yana ɗaukan lokaci sosai. Sa’ad da Saratu ta rasu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ibrahim kuma ya zo domin makoki saboda Saratu, ya yi kuka kuma dominta.” (Far. 23:1, 2) Ibrahim ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da matarsa ta rasu ko da yake ya gaskata da begen tashin matattu. (Ibran. 11:17-19) Yaƙubu yana ƙaunar matarsa Rahila sosai, kuma sa’ad da ta rasu, bai mance da ita da wuri ba. Ya gaya wa ’ya’yansa abubuwa masu kyau game da ita.—Far. 44:27; 48:7.
Waɗanne darussa ne za mu koya daga waɗannan misalan da muka karanta a Littafi Mai Tsarki? Idan ɗaya cikin ma’aurata ya rasu, baƙin cikin da ɗayan yake yi yana ɗaukan shekaru da yawa. Bai kamata mu ga cewa suna da kasawa shi ya sa suke kuka da kuma baƙin ciki ba. Maimakon haka, mu ɗauki baƙin cikin a matsayin rashin da suka yi ne. Za su bukaci ta’aziya da kuma taimakonmu na dogon lokaci.
DA SANNU-SANNU ZA KA DAINA
Sa’ad da ɗaya cikin ma’aurata ya rasu, rayuwa ba za ta kasance wa ɗayan kamar yadda take a lokacin da bai yi aure ba. Idan ma’aurata suka daɗe da aure, miji yakan san yadda zai ƙarfafa matarsa kuma ya lallaɓe ta sa’ad da ta kasala. Amma idan ya mutu, ƙaunar da kuma ƙarfafar da yake mata ya ƙare. Hakazalika, mata ma takan san yadda za ta ladabta wa mijinta kuma ta sa shi farin ciki. Yakan ji daɗin lallaɓa da kalmomin ƙarfafa, haɗe da irin kula da take masa. Amma idan ta rasu, ya rasa dukan waɗannan abubuwan ke nan. Saboda haka, waɗanda matansu ko mazansu suka rasu sukan damu ko kuma ji tsoron yadda rayuwa za ta kasance musu a nan gaba. Wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce za ta taimaka musu su kasance da salama da kuma kwanciyar hankali?
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada fa ku yi alhini a kan gobe: gama gobe za ya yi alhini don kansa. Wahalar yini ta ishe shi.” (Mat. 6:34) Ko da yake Yesu ya yi wannan furucin ne don bukatunmu na yau da kullum, amma waɗanda suka rasa mata ko miji ma sun amfana daga waɗannan kalmomin. ’Yan watanni bayan matar wani mutum mai suna Charles ta rasu, ya ce: “Ina kewar matata Monique, har a wani lokaci ina baƙin ciki sosai. Amma, na gane cewa haka al’amarin yake kuma da sannu-sannu baƙin cikin zai ragu.”
Hakika, da “sannu-sannu” Charles ya jimre. Ta yaya ya iya yin hakan? Ya ce: “Da sannu-sannu, Jehobah ya taimaka mini in daina baƙin ciki.” Ko da yake bai daina baƙin ciki farat ɗaya ba, amma bai bar wannan damuwar ta kasance kan gaba a rayuwarsa ba. Idan mijinki ko matarka ta rasu, ka bi da yanayin a hankali. Ba ka san irin amfani ko kuma ƙarfafar da za ka samu gobe ba.
Jehobah bai halicce mu don mu riƙa mutuwa ba. Akasin haka, mutuwa ɗaya ce cikin “ayyukan Shaiɗan.” (1 Yoh. 3:8; Rom. 6:23) Shaiɗan yana amfani da mutuwa da kuma tsoron mutuwa don ya sa mutane su zama kamar bayi kuma kada su kasance da bege. (Ibran. 2:14, 15) Shaiɗan yana murna idan mutane ba su da begen yin farin ciki a rayuwa yanzu da kuma a sabuwar duniya. Saboda haka, irin baƙin cikin da ma’aurata suke yi idan ɗaya cikinsu ya rasu sanadin zunubin Adamu da Hawwa’u da kuma tawayen da Shaiɗan ya yi ne. (Rom. 5:12) Jehobah zai magance dukan ɓarnar da Shaiɗan ya yi, kuma zai kawo ƙarshen mutuwa. Waɗanda za su sami ’yanci daga tsoron mutuwa sun haɗa da mutane da yawa da matansu ko kuma mazansu suka rasu, kamar irin yanayin da wataƙila kake ciki yanzu.
Babu shakka, waɗanda za a ta da su daga mutuwa za su ga yadda aka kyautata dangantaka tsakanin mutane a sabuwar duniya. Alal misali, za a ta da iyaye da kakannin zuwa duniya kuma a hankali za su zama kamilai tare da yaransu da kuma jikokinsu. Mutane ba za su sake tsufa ba. Matasa ba za su ɗauki kakanninsu kamar yadda suke ɗaukansu a yau ba. Kuma babu shakka, hakan zai kyautata dangantakar ’yan Adam.
Wataƙila kana da tambayoyi da yawa game da waɗanda za a tayar daga mutuwa. Alal misali, me zai faru da waɗanda mijinsu ko matarsu ta biyu, ta uku ko fiye da haka suka rasu? Sadukiyawa sun yi wa Yesu tambaya a kan wata mata da mijinta na fari ya rasu, na biyu ma haka, har su bakwai suka rasu. (Luk 20:27-33) Yaya dangantakarsu za ta zama idan aka tayar da su daga mutuwa? Ba mu san abin da zai faru da su ba, don haka, ba zai kasance da muhimmanci mu ƙaga yadda yanayin zai zama ko kuma mu riƙa damuwa a kan waɗannan tambayoyin ba. Za mu dogara ga Allah ne kawai a wannan batun. Za mu kasance da tabbaci cewa duk abin da Jehobah zai yi nan gaba nagari ne, kuma abu ne da za mu yi ɗokin gani ba wanda zai tsoratar da mu ba.
MUNA SAMUN ƘARFAFA DAGA BEGEN TASHIN MATATTU
Ɗaya cikin koyarwar Kalmar Allah mafi sauƙin fahimta shi ne cewa za a tayar da ’yan’uwanmu da suka mutu. Labaran mutanen da aka tayar daga mutuwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa “dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa [Yesu], su fito kuma.” (Yoh. 5:28, 29) Mutane za su yi farin ciki sosai idan suka sake saduwa da ’yan’uwansu da aka tayar daga mutuwa. Hakika, ba za mu taɓa iya kwatanta irin farin cikin da waɗanda aka tayar za su yi ba.
Mutane za su yi farin ciki sosai a duniya fiye da dā, sa’ad da aka tayar biliyoyin matattu. (Mar. 5:39-42; R. Yoh. 20:13) Yin bimbini a kan tashin matattun da za a yi a nan gaba zai ƙarfafa dukan waɗanda ’yan’uwansu suka rasu.
Shin akwai abin da zai sa kowane mutum baƙin ciki bayan an ta da matattu? Littafi Mai Tsarki ya ce babu. Littafin Ishaya 25:8 ya ce Jehobah zai “haɗiye mutuwa har abada.” Hakan ya ƙunshi kawo ƙarshen mutuwa gaba ɗaya da kuma baƙin cikin da ta jawo. Annabcin da ke littafin Ishaya ya ƙara da cewa: “Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki.” Idan kina baƙin ciki domin mijinki ko matarka ta rasu, begen tashin matattu ya kamata ya sa ka farin ciki.
Babu ɗaya cikin ’yan Adam da ya san dukan abubuwan da Allah zai yi a sabuwar duniya. Jehobah ya ce: “Kamar yadda sammai suna da nisa da duniya, haka nan kuma al’amurana sun fi naku tsawo, tunanina kuma sun fi naku.” (Isha. 55:9) Alkawarin da Yesu ya yi mana na tashin matattu ya kamata ya sa mu dogara ga Jehobah kamar yadda Ibrahim ya yi, ko ba haka ba? Abu mafi muhimmanci da ake bukata daga Kirista yanzu shi ne yin biyayya ga Kalmar Allah don mu da waɗanda aka ta da daga mutuwa mu ‘cancanci samun shiga wancan zamanin.’—Luk 20:35, Littafi Mai Tsarki.
DALILIN KASANCEWA DA BEGE
Idan mun ci gaba da kasancewa da bege yanzu, hakan zai taimaka mana mu daina damuwa game da abin da zai faru a nan gaba. Yawancin mutane ba su da bege sosai game da nan gaba. Amma Jehobah ya yi mana wani alkawari mai kyau. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai biya bukatunmu kuma ya tanadar mana da abubuwan da muke so ko da yake ba mu san yadda zai yi hakan ba. Manzo Bulus ya rubuta: “Bege wanda a ke ganinsa ba bege ba ne: gama wa ke kafa bege ga abin da ya ke gani? Amma idan muna kafa bege ga abin da ba mu gani ba, sa’annan da haƙuri mu ke sauraronsa.” (Rom. 8:24, 25) Kasancewa da bege sosai game da alkawuran Allah zai taimaka mana mu jimre da rasuwar matarmu ko mijinmu. Idan ka kasance da jimiri, za ka more lokacin da Jehobah zai “biya maka muradin zuciyarka” a nan gaba. Ƙari ga haka, Jehobah zai “biya wa kowane mai-rai muradinsa.”—Zab. 37:4; 145:16; Luk 21:19.
A lokacin da Yesu ya kusan mutuwa, manzanninsa sun yi baƙin ciki sosai kuma suka ruɗe. Amma Yesu ya ta’azantar da su da wannan furucin: “Kada zuciyarku ta ɓaci; kuna bada gaskiya ga Allah, ku bada gaskiya gareni kuma.” Ya ƙara da cewa: “Ba na barin ku marayu ba, ni Zan zo wurinku.” (Yoh. 14:1-4, 18, 27) Kalmomin Yesu sun ba mabiyansa shafaffu a karnuka da yawa dalilin kasancewa da bege da kuma jimiri. Waɗanda suke ɗokin ganin ’yan’uwansu da suka rasu ba su da wani dalilin ƙin kasancewa da bege. Jehobah da kuma Ɗansa ba za su yashe su ba. Hakika, za a tayar da waɗanda suka mutu. Nan ba da daɗewa ba, za ka sadu da ’yan’uwanka da suka rasu.
a An canja sunayen.