Ka Yi Wa Masu Makoki Ta’aziyya
“Ubangiji ya shafe ni . . . in yi ma dukan masu-makoki ta’aziyya.”—ISHAYA 61:1, 2.
1, 2. Waye ya kamata mu yi wa ta’aziyya, kuma me ya sa?
JEHOVAH, Allah na dukan ta’aziyya, ya koya mana mu nuna damuwa sa’ad da wasu suke fuskantar bala’i. Ya koya mana mu “ƙarfafa masu-raunanan zukata” kuma mu yi wa dukan masu makoki ta’aziyya. (1 Tassalunikawa 5:14) Sa’ad da ake bukatar irin wannan taimako, muna yi wa ’yan’uwa masu bi. Muna nuna ƙauna kuma ga waɗanda ba sa cikin ikilisiya, har da waɗanda ba sa ƙaunarmu ma a dā.—Matta 5:43-48; Galatiyawa 6:10.
2 Yesu Kristi ya karanta kuma ya yi amfani da aikin da aka ba shi cikin annabci: “Ruhun Ubangiji Yahweh yana bisa gareni; gama Ubangiji ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga matalauta; ya aike ni domin in warkadda masu-karyayyen zuciya, . . . in yi ma dukan masu-makoki ta’aziyya.” (Ishaya 61:1, 2; Luka 4:16-19) Kiristoci shafaffu na zamani da daɗewa sun fahimci cewa su ma za su yi wannan aikin, kuma “waɗansu tumaki” da farin ciki sun haɗu da su a wajen yin wannan aikin.—Yohanna 10:16.
3. Sa’ad da mutane suke tambaya, “Me ya sa Allah ya ƙyale bala’i?,” ta yaya za mu taimake su?
3 Sa’ad da bala’i ya auku kuma mutane suka karaya a zuciya, sau da yawa suna tambaya, “Me ya sa Allah ya ƙyale bala’i?” Littafi Mai Tsarki ya amsa wannan tambayar da kyau. Amma, zai ɗauki lokaci daga wanda ba ɗalibin Littafi Mai Tsarki ba ya fahimci amsar da kyau. Za a iya samun taimako a littattafan Shaidun Jehovah.a Da farko, ya kasance ta’aziyya ga wasu mutane su gani cikin Littafi Mai Tsarki ayoyi kamar waɗanda suke Ishaya 61:1, 2, domin ta ambata cewa Allah yana son ’yan Adam su sami ta’aziyya.
4. Yaya wata Mashaidiya a Poland ta taimaki wata ’yar makaranta da ta raunana a zuciya, kuma ta yaya wannan labari zai taimake ka ka taimaki wasu?
4 Matasa, da tsofaffi, duka suna bukatar ta’aziyya. Wata yarinya wadda ta raunana a zuciya a Poland ta nemi shawara wurin wata idon sani. Ta ci gaba da tambaya a hankali, abuyarta da Mashaidiyar Jehovah ce ta fahimci cewa yarinyar tana da tambayoyi da yawa da kuma shakka: “Me ya sa mugunta ta yi yawa? Me ya sa mutane suke wahala? Me ya sa ƙanwata da take da shan inna take wahala? Me ya sa nake ciwon zuciya? Coci ya ce haka Allah yake so. Amma idan haka ne, zan daina imani da shi!” Mashaidiyar ta yi wa Jehovah addu’a kuma ta ce: “Ina mai farin ciki da ki ka yi mini tambaya game da wannan. Zan yi ƙoƙari in taimake ki.” Ta gaya mata cewa ita ma ta yi shakka da take yarinya kuma Shaidun Jehovah ne suka taimake ta. Ta yi bayani: “Na koyi cewa Allah ba ya wahalar da mutane. Yana ƙaunarsu, yana son abin da zai fi musu kyau, kuma ba da daɗewa ba zai yi gyare-gyare ƙwarai a duniya. Ciwo, matsaloli da ke tattare da tsufa, da mutuwa za su ƙare, mutane masu biyayya za su rayu har abada—a nan duniya.” Ta nuna wa yarinyar Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4; Ayuba 33:25; Ishaya 35:5-7 da kuma 65:21-25. Bayan tattaunawa na dogon lokaci, yarinyar ta ce: “Yanzu na san ma’anar rayuwata. In sake zuwa in same ki?” Ana nazarin Littafi Mai Tsarki sau biyu a mako da ita.
Ka Yi wa Wasu Ta’aziyya da Ta’aziyyar da Allah ke Bayarwa
5. Sa’ad da muke nuna tausayi, menene zai ba da ta’aziyya ta gaske?
5 Idan muna nema mu yi wa wasu ta’aziyya, lallai kalmomin tausayi za su dace. Mu yi ƙoƙari mu yi magana da murya mai taushi ga wanda yake makoki a nuna damuwarmu ƙwarai game da yanayinsa. Ba a cim ma wannan ta yin amfani da kalamin da ba su da ma’ana. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “ta wurin haƙuri da ta’aziyyar littattafai mu zama da bege.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Romawa 15:4.) Yin la’akari da wannan, za mu iya bayani a lokacin da ya dace abin da Mulkin Allah yake, kuma za mu iya nuna daga Littafi Mai Tsarki yadda zai cire matsaloli na yanzu. Sa’an nan sai mu yi magana a kan abin da ya sa bege ne da za mu dogara. A wannan hanyar, za mu yi ta’aziyya.
6. Me ya kamata mu taimake mutane su fahimta domin su amfana ƙwarai daga ta’aziyya ta Nassosi?
6 Domin a amfana ƙwarai daga ta’aziyya da aka bayar, mutum yana bukatar ya san Allah na gaskiya, irin Mutumin da yake, da tabbacin alkawuransa. Sa’ad da muke nema mu taimaki mutum da ba ya bauta wa Jehovah a yanzu, ya dace mu bayyana abubuwa na gaba. (1) Ta’aziyya da ke cikin Littafi Mai Tsarki daga Jehovah ne, Allah na gaskiya. (2) Jehovah ne Mai Iko Duka, Mahaliccin sama da ƙasa. Allah ne mai ƙauna kuma mai yalwar alheri da gaskiya. (3) Za mu ƙarfafa mu jimre da yanayi idan mun matsa kusa da Allah ta samun cikakken sani daga Kalmarsa. (4) Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da nassosi da ya yi magana a kan gwaji na ainihi da mutane dabam dabam suka fuskanta.
7. (a) Menene za a cim ma ta nanata cewa ta’aziyya da Allah yake bayarwa “tana yawaita ta wurin Kristi”? (b) Ta yaya za ka yi ta’aziyya wa wanda ya fahimta cewa halinsa dā ba shi da kyau?
7 Wasu sun ba da ƙarfafa ta ruhaniya ga masu makoki da suka sarƙu da Littafi Mai Tsarki ta karanta 2 Korinthiyawa 1:3-7. Sa’ad da suke haka, sun nanata furcin nan “ta’aziyyarmu tana yawaita ta wurin Kristi.” Wannan nassin zai taimaki mutum ya fahimta cewa Littafi Mai Tsarki ne tushen ta’aziyya da ya kamata ya yi la’akari da ita. Zai iya zama tushen ƙara tattaunawa, wataƙila wani lokaci. Idan mutum yana jin cewa matsalolinsa domin miyagun abubuwan da ya yi ne, sa’an nan za mu iya gaya masa, ba tare da kushe masa ba, cewa abar ta’aziyya ce mu san abin da aka rubuta a 1 Yohanna 2:1, 2 da Zabura 103:11-14. A waɗannan hanyoyi muna yi wa wasu ta’aziyya da ta’aziyyar da Allah ya bayar.
Ka Yi wa Waɗanda Mugunta ko Tattalin Arziki Ya Shafi Rayuwarsu Ta’aziyya
8, 9. Ta yaya ya dace a yi wa mutane da suka sha wahalar mugunta ta’aziyya?
8 Mugunta ta shafi rayuwar mutane da yawa—mugunta a yanki ko kuma a yaƙi. Ta yaya za mu yi musu ta’aziyya?
9 Kiristoci na gaskiya suna mai da hankali kada su goyi bayan rukuni ko kuma wani a yaƙe-yaƙe na duniya ta kalma ko kuma ta ayyukansu. (Yohanna 17:16) Amma suna amfani da Littafi Mai Tsarki su nuna cewa yanayi mai wuya na yanzu ba zai ci gaba ba har abada. Suna iya karanta Zabura 11:5 su nuna yadda Jehovah yake ji game da waɗanda suke ƙaunar mugunta ko kuma Zabura 37:1-4 su nuna cewa Allah ya ƙarfafa mu kada mu rama wa kanmu amma mu dogara ga Allah. Kalmomin Zabura 72:12-14 sun nuna yadda Sulemanu Mai Girma, Yesu Kristi, da yake Sarauta a sama yanzu, yake ji game da mutane marasa laifi da suke shan wahalar mugunta.
10. Idan ka yi rayuwa cikin shekaru na yaƙe-yaƙe, ta yaya nassosi da aka rubuta za su yi maka ta’aziyya?
10 Wasu mutane sun jimre yaƙe-yaƙe da yawa yayin da rukuni da suke fāɗa da su suna fama su ci nasara. Suna da ra’ayin cewa yaƙi da sakamakonsa sashen rayuwa ce. Suna da begen cewa abubuwa za su fi kyau idan za su iya gudu zuwa wata ƙasa. Amma yawancinsu ba su yi nasarar yin haka ba, mutanen da suka gwada yin haka sun yi hasarar rayukansu a ƙoƙarin yin haka. Waɗanda suka samu shiga wata ƙasa sau da yawa suna iske cewa sun fita daga wata matsala zuwa wata. Za a iya amfani da Zabura 146:3-6 a taimaki irin waɗannan mutane su sa begensu cikin abu mafi tabbaci maimakon ƙaura. Annabcin nan a Matta 24:3, 7, 14 ko kuma 2 Timothawus 3:1-5 zai iya taimake su su fahimta yanayin sosai da ma’anar yanayi da suke jimrewa, musamman, cewa muna zama a ƙarshen tsohon zamani. Ayoyi kamar su Zabura 46:1-3, 8, 9 da Ishaya 2:2-4 za su taimake su su fahimta cewa da gaske da akwai begen salama a nan gaba.
11. Waɗanne ayoyi ne suka ta’azantar da wata mata a Afirka ta Yamma, kuma me ya sa?
11 A lokacin yaƙi a Afirka ta Yamma, wata mata da iyalinta suka gudu daga gidanta sa’ad da ake harbin harsashi. Ta cika da tsoron rayuwa, baƙin ciki, da fid da zuciya. Bayan haka, sa’ad da iyalin tana da zama a wata ƙasa, mijinta ya ƙone takardar aurensu, ya sallami matarsa da take da ciki lokacin, da ɗansu mai shekara goma, domin shi ya zama firist. Sa’ad da aka karanta mata Filibbiyawa 4:6, 7 da Zabura 55:22, tare da talifofi na Nassi daga Hasumiyar Tsaro da Awake!, a ƙarshe ta sami ta’aziyya da ma’anar rayuwa.
12. (a) Wane sauƙi ne Nassosi suka ba wa waɗanda suka matsu game da tattalin arziki? (b) Ta yaya wata Mashaidiya a Asiya ta taimaki wata mai ciniki?
12 Tattalin arziki ya yi wa rayuwar mutane da yawa lahani. Wani lokaci wannan ma saboda yaƙi ne da sakamakonsa. Wani lokaci, dokokin gwamnati da haɗama da rashin gaskiya na waɗanda suke iko sun haɗa sun cinye kuɗi da mutane suka tara kuma sun tilasta musu su yi hasarar dukiyarsu. Wasu ba su taɓa samun kaya mai yawa na wannan duniya ba. Irin waɗannan za su iya samun ta’aziyya cewa Allah ya tabbatar cewa zai kawo sauƙi ga waɗanda suka dogara gare shi da kuma duniya ta adalci da mutane za su more aikin hannuwansu. (Zabura 146:6, 7; Ishaya 65:17, 21-23; 2 Bitrus 3:13) Sa’ad da wata Mashaidiya a wata ƙasar Asiya ta ji wata mai ciniki tana furta damuwa saboda yanayin tattalin arziki a wajen, ta bayyana mata cewa abin da yake faruwa a wajen, abubuwa da suke faruwa a dukan duniya ne. Taɗi a kan Matta 24:3-14 da Zabura 37:9-11 ya kai ga nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai.
13. (a) Sa’ad da mutane sun yi sanyin gwiwa don alkawuran ƙarya, ta yaya za mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki mu taimake su? (b) Idan mutane suna jin cewa munanan yanayi ya nuna cewa babu Allah, yaya za ka yi ƙoƙari ka taimake su?
13 Sa’ad da mutane suka wahala shekaru da yawa ko kuma sun yi sanyin gwiwa don alkawuran ƙarya, suna iya zama kamar Isra’ilawa a Masar waɗanda “domin zafin da su ke ji a rai” ba su saurara ba. (Fitowa 6:9) A irin wannan yanayi, zai fi amfani a taƙaita hanyoyi da Littafi Mai Tsarki zai taimake su su bi da matsaloli na yanzu kuma su guje wa haɗari da ke ɓata wa mutane da yawa rayuwa. (1 Timothawus 4:8b) Wasu suna iya ɗaukan munanan yanayi da suke ciki cewa tabbaci ne babu Allah ko kuma ba ya kula da su. Kana iya magana a kan nassosi da sun dace, ka taimake su su fahimta cewa Allah ya yi tanadin taimako amma mutane da yawa ba su amince da shi ba.—Ishaya 48:17, 18.
Sa’ad da Kake wa Waɗanda Suka Sha Wahalar Hadari da Girgizar Ƙasa Ta’aziyya
14, 15. Sa’ad da wani bala’i ya sa mutane da yawa cikin yanayin baƙin ciki, ta yaya Shaidun Jehovah suka nuna sun damu?
14 Bala’i yakan auku domin hadari, girgizar ƙasa, gobara, ko kuma hargitsi. Mutane ko’ina ƙila suna baƙin ciki. Menene za a yi don a ta’azantar da waɗanda suka tsira?
15 Mutane suna bukatar su sani cewa wani ya damu. Bayan farmakin ta’addanci a wata ƙasa, mutane da yawa suna baƙin ciki. Yawancinsu sun yi hasarar waɗanda suke cikin iyali, masu kawo abinci a iyali, abokai, aiki, ko kuma kwanciyar rai da suke tunani suna da shi. Shaidun Jehovah sun taimaki waɗanda suke yankinsu, suna nuna juyayi domin hasara mai girma da suka yi kuma ba da kalmomin ta’aziyya daga Littafi Mai Tsarki. Mutane da yawa sun yi godiya domin damuwa da suka nuna.
16. Sa’ad da bala’i ya faɗa wa wani yanki a El Salvador, me ya sa hidimar fage na Shaidu ta yi amfani?
16 Girgizar ƙasa da kuma taɓo mai yawa da ya biyo bayan ya kashe mutane da yawa a El Salvador a shekara ta 2001. Ɗan wata Mashaidiya mai shekara 25 da ƙannen budurwarsa biyu mata sun mutu. Mamar saurayin da budurwarsa nan da nan suka shagala cikin hidimar fage. Mutane da yawa suna ce musu Allah ne ya ɗauki waɗanda suka mutu ko kuma nufin Allah ne. Shaidun suka ambata Misalai 10:22 don su nuna cewa Allah ba ya son mu ji ciwo. Sun karanta Romawa 5:12 don su nuna cewa zunubin ’yan Adam ne ya jawo mutuwa, ba nufin Allah ba ne. Sun yi nuni ga saƙon ta’aziyya da ke Zabura 34:18, Zabura 37:29, Ishaya 25:8, da kuma Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4. Mutane sun saurara sosai, musamman da yake mata biyun su ma sun yi rashin wasu cikin iyalinsu a bala’in, kuma an soma nazarin Littafi Mai Tsarki da yawa.
17. A lokacin bala’i, wane irin taimako za mu iya bayarwa?
17 Sa’ad da bala’i ya auku, kana iya tarar da wanda yake bukatar taimako nan da nan. Wannan zai ƙunshi kirar likita, taimakon mutum ya je asibiti, ko yin abin da zai yiwu a yi tanadin abinci da wurin kwanciya. A shekara ta 1998 a irin wannan bala’i a Italiya, wani manemin labarai ya lura cewa Shaidun Jehovah “suna aiki a hanya mai amfani, suna taimakon waɗanda suke wahala, ba tare da damuwa game da addini da suke bi ba.” A wasu wurare, abubuwa da aka ambata don kwanaki na ƙarshe suna kawo wahala da yawa. A waɗannan wurare, Shaidun Jehovah sun yi nuni ga annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki, kuma sun yi wa mutane ta’aziyya da tabbaci na Littafi Mai Tsarki cewa Mulkin Allah zai kawo kwanciyar rai ta gaske ga ’yan Adam.—Misalai 1:33; Mikah 4:4.
Ba da Ta’aziyya Sa’ad da Wani Cikin Iyali Ya Mutu
18-20. Sa’ad da aka yi rasuwa cikin iyali, me za ka iya faɗa ko yi a ba da ta’aziyya?
18 Kowacce rana mutane da yawa suna makoki domin mutuwar wanda suke ƙauna. Za ka iya sadu da masu makoki sa’ad da kake sa hannu cikin hidimar Kirista ko kuma sa’ad da kake harkokin rayuwar yau da kullum. Menene za ka ce ko kuma yi da zai kawo ta’aziyya?
19 Mutumin yana baƙin ciki sosai? Ɗakin yana cike da dangi da suke makoki ne? Wataƙila kana da abubuwa da yawa da za ka so ka faɗa, amma yana da muhimmanci a yi tunanin kirki. (Mai-Wa’azi 3:1, 7) Wataƙila abin da ya dace shi ne a nuna juyayi, ka bar littafi na Littafi Mai Tsarki (mujalla, jarida, ko kuma warƙa), sai ka koma bayan wasu kwanaki ka ga ko da taimakon da za ka yi. A lokacin da ya dace, ka ba da wasu furcin ƙarfafa daga Littafi Mai Tsarki. Wannan zai sa su natsu kuma yi lafiya. (Misalai 16:24; 25:11) Ba za ka iya ta da matattu ba, yadda Yesu ya yi. Amma za ka iya faɗan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da yanayin matattu, ko da wannan ba zai zama lokacin ƙaryata ra’ayoyi da ba daidai ba. (Zabura 146:4; Mai-Wa’azi 9:5, 10; Ezekiel 18:4) Kuna iya karanta tare alkawuran Littafi Mai Tsarki game da tashin matattu. (Yohanna 5:28, 29; Ayukan Manzanni 24:15) Kana iya tattauna abin da wannan yake nufi, ka yi amfani da labarin tashin matattu a Littafi Mai Tsarki a yin haka. (Luka 8:49-56; Yohanna 11:39-44) Ka kuma jawo hankali ga halayen Allah mai ƙauna da ya ba mu irin wannan begen. (Ayuba 14:14, 15; Yohanna 3:16) Ka bayyana yadda wannan koyarwa ta amfane ka da abin da ya sa ka amince da ita.
20 Gayyatar wanda yake makoki zuwa Majami’ar Mulki zai taimake shi ya san mutane da suke ƙaunar maƙwabtansu da gaske da waɗanda suka san yadda ake ƙarfafa juna. Wata mata a Sweden ta ga cewa wannan abin da take nema ne dukan rayuwarta.—Yohanna 13:35; 1 Tassalunikawa 5:11.
21, 22. (a) Menene ake bukata a gare mu idan za mu ba da ta’aziyya? (b) Ta yaya za ka yi wa wanda ya riga ya san Nassosi sosai ta’aziyya?
21 Sa’ad da ka sani cewa wani yana makoki, ko a cikin ikilisiyar Kirista ko a waje, wani lokaci kana gani ba ka san abin da za ka faɗa ko kuma yi ba ne? Kalmar Helenanci da sau da yawa ake juya “ta’aziyya” a cikin Littafi Mai Tsarki a zahiri tana nufin “jawo mutumin gefenka.” Zama mai ta’aziyya na gaskiya na nufin ba da kanka ga masu makoki.—Misalai 17:17.
22 Idan mutumin da kake son ka yi masa ta’aziyya ya riga ya san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mutuwa, fansa, da tashin matattu fa? Ganin wanda yake da imani ɗaya a wurin abin ta’aziyya ne. Idan yana son ya yi magana, ka saurara da kyau. Kada ka ji kana bukatar ka ba da jawabi. Idan ka karanta nassosi, ka bi da wannan furci ne na Allah da ke ƙarfafa zukatanku biyu. Ka nuna tabbaci mai ƙarfi da ku biyu kuke da shi na alkawarin nassosi. Ta nuna juyayi na Allah da tattauna gaskiya mai tamani da ke cikin Kalmar Allah, za ka iya ka taimake masu makoki su samu ta’aziyya da ƙarfi daga “Allah na dukan ta’aziyya,” Jehovah.—2 Korinthiyawa 1:3.
[Hasiya]
a Ka dubi waɗannan littattafai Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, babi na 8; Reasoning From the Scriptures, shafuffuka 393-400, 427-431; Is There a Creator Who Cares About You?, babi na 10; da mujallar nan Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
Mecece Amsarka?
• Waye mutane da yawa suke ɗora wa laifin bala’i, kuma ta yaya za mu taimaka musu?
• Menene za mu yi domin mu taimaki wasu su amfana sosai daga ta’aziyya da Littafi Mai Tsarki ke bayarwa?
• Waɗanne yanayi ne suke kawo wa mutane da yawa a yankinka baƙin ciki, ta yaya za ka yi musu ta’aziyya?
[Hotuna a shafi na 29]
Ba da saƙo na ta’aziyya a lokacin wahala
[Inda aka Dauko]
Sansanin ’yan gudun hijira: UN PHOTO 186811/J. Isaac
[Hoto a shafi na 30]
Kasancewar aboki wajen da ake makoki ta’aziyya ce