Ka “Yi Wa Dukan Masu-makoki Ta’aziyya”
“Ubangiji ya shafe ni . . . in yi wa dukan masu-makoki ta’aziyya.”—ISHA. 61:1, 2.
1. Mene ne Yesu ya yi wa waɗanda suke makoki, kuma me ya sa?
YESU KRISTI ya ce: “Abincina ke nan, in yi nufin wanda ya aiko ni, in cika aikinsa.” (Yoh. 4:34) Sa’ad da Yesu yake aikin da Allah ya ba shi, ya nuna halaye na musamman na Ubansa. Ƙaunar Jehobah ga mutane tana cikin waɗannan halayen. (1 Yoh. 4:7-10) Manzo Bulus ya yi magana game da hanya ɗaya da Jehobah ya nuna wannan ƙaunar sa’ad da ya kira shi “Allah na dukan ta’aziyya.” (2 Kor. 1:3) Yesu ya nuna irin wannan ƙaunar sa’ad da ya yi abin da aka annabta a cikin annabcin Ishaya. (Karanta Ishaya 61:1, 2.) Yesu ya karanta wannan annabci a majami’a a Nazarat kuma ya yi waɗannan kalaman ga kansa. (Luk 4:16-21) A duk lokacin hidimarsa, Yesu ya yi wa masu makoki ta’aziyya kuma ya sa su samu ƙarfafa da kwanciyar hankali.
2, 3. Me ya sa mabiyan Kristi suke bukatar su yi koyi da shi wajen yi wa mutane ta’aziyya?
2 Dukan mabiyan Yesu suna bukatar su yi koyi da shi ta wajen yi wa waɗanda suke makoki ta’aziyya. (1 Kor. 11:1) Bulus ya ce: “Ku yi ma junanku ta’aziya, ku gina juna.” (1 Tas. 5:11) Muna bukatar mu ƙarfafa mutane musamman domin ’yan Adam yanzu suna fuskantar “kwanaki na ƙarshe” da za a sha wuya ƙwarai. (2 Tim. 3:1) Ƙarin mutane masu zukatan kirki a dukan duniya suna zama cikin waɗanda kalamansu da ayyukansu suna sa mutane makoki da ciwon kai da kuma baƙin ciki.
3 Kamar yadda annabcin Littafi Mai Tsarki ya faɗa, a waɗannan kwanaki na ƙarshe na wannan mugun zamani, mutane da yawa sun “zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai, masu-zagi, marasa-bin iyaye, marasa-godiya, marasa-tsarki, marasa-ƙauna irin na tabi’a, masu-baƙar zuciya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, masu-taurin kai, masu-kumbura, mafiya son annishuwa da Allah.” Irin waɗannan halayen sun fi muni yanzu fiye da dā, domin ‘miyagun mutane da masu-hila sun daɗa mugunta gaba gaba.’ —2 Tim. 3:2-4, 13.
4. Mene ne ya faru ga yanayin duniya a zamaninmu?
4 Bai kamata dukan waɗannan su sa mu mamaki ba, tun da yake Kalmar Allah ta bayyana sarai cewa “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaitan.” (1 Yoh. 5:19) “Duniya duka” ta ƙunshi rukunin siyasa da addini da ɓangarorin kasuwanci na wannan duniya, da kuma hanyoyin da Shaiɗan yake amfani da shi don yaɗa ra’ayoyinsa. Babu shakka, ya dace da aka kira Shaiɗan Iblis “sarkin duniya” da “allah na wannan zamani.” (Yoh. 14:30; 2 Kor. 4:4) Yanayi a dukan duniya ya ci gaba da taɓarɓarewa domin Shaiɗan yana fushi sosai, domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan kafin Jehobah ya halaka shi. (R. Yoh. 12:12) Yana da ban ƙarfafa mu san cewa Allah ba zai ƙyale Shaiɗan da mugun zamaninsa ya daɗe fiye da haka ba kuma za a yi maganin batun da Shaiɗan ya ta da game da ikon mallakar Jehobah!—Far., sura ta 3 da Ayu., sura ta 2.
Ana Wa’azin Bishara a Dukan Duniya
5. Ta yaya annabci game da aikin wa’azi yake samun cikawa a waɗannan kwanaki na ƙarshe?
5 A wannan zamani mai wuya na tarihin ’yan Adam, abin da Yesu ya annabta yana cikawa. Ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Mat. 24:14) Kamar yadda Yesu ya ce, mutanen Jehobah a dukan duniya suna wa’azin bishara game da Mulkin Allah. A yau, Shaidun Jehobah fiye da 7,500,000 da suke cikin fiye da ikilisiyoyi 107,000 a dukan duniya suna wa’azi game da Mulkin Allah, kamar yadda Yesu ya sa ya zama jigon wa’azinsa da koyarwarsa. (Mat. 4:17) Ta wurin aikin wa’azi na zamani, muna yi wa mutane da yawa masu makoki ta’aziyya. A cikin shekaru biyu na kwanan baya, an yi wa mutane 570,601 baftisma a matsayin Shaidun Jehobah!
6. Mene ne za ka iya ce game da ƙaruwa da ake samu a aikinmu na wa’azi?
6 A yanzu Shaidun Jehobah suna fassara da kuma rarraba littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki a fiye da harsuna 500. Babu wanda ya taɓa yin irin wannan aiki a dā. Ko da yake suna cikin duniya da Shaiɗan ke mulki, mutanen Jehobah suna ƙwazo a hidimarsa kuma sun ci gaba da ƙaruwa. Da ba za a iya cim ma hakan ba, da ba don ja-gorar ruhu mai tsarki na Allah ba. Domin ana wa’azi a dukan duniya, mutane da suka karɓi saƙon Mulkin za su iya samun ƙarfafa da mutanen Jehobah suke da shi.
Yi wa ’Yan’uwa Ta’aziyya
7. (a) Me ya sa bai kamata mu yi zato cewa Jehobah zai kawo ƙarshen dukan abubuwan da suke sa mu baƙin ciki ba? (b) Ta yaya muka sani cewa zai yiwu mu jimre da tsanani da kuma ƙunci?
7 A wannan duniya da take cike da mugunta da wahala, dukanmu muna fuskantar wasu yanayi da za su sa mu baƙin ciki. Ba ma zaton Allah ya cire dukan abubuwan da suke sa mu baƙin ciki kafin ya halaka zamanin nan. Yayin da muke jiran wannan ranar, tsanani ne zai gwada ko muna da aminci ga Allah kuma mun amince ga Mai ikon mallaka ta dukan sararin samaniya. (2 Tim. 3:12) Amma da taimako da ƙarfafa daga wurin Ubanmu na samaniya, za mu iya zama kamar Kiristoci na Tasalonika na dā, waɗanda suka nuna haƙuri da bangaskiya.—Karanta 2 Tasalonikawa 1:3-5.
8. Wane tabbaci na Nassi ne ya nuna cewa Jehobah yana yi wa bayinsa ta’aziyya?
8 Babu shakka cewa Jehobah yana tanadar wa bayinsa ƙarfafar da suke bukata. Alal misali, sa’ad da Sarauniya Jezebel take son ta kashe annabi Iliya, ya ji tsoro kuma ya gudu. Ya yi rashin gaba gaɗi kuma ya gwammace ya mutu. Maimakon Jehobah ya tsauta wa Iliya, ya ƙarfafa shi kuma ya ba shi gaba gaɗin ci gaba da yin aikinsa a matsayin annabi. (1 Sar. 19:1-21) Wani misalin da ya nuna cewa Jehobah yana ƙarfafa mutanensa shi ne yadda ya taimaka wa ikilisiyar Kirista ta ƙarni na farko. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar lokacin da “Ikilisiya fa ta sami salama, tana ginuwa, cikin dukan Yahudiya da Galili da Samariya.” Bugu da ƙari, “tana tafiya cikin tsoron Ubangiji, bisa ga ta’aziyar Ruhu Mai-tsarki kuma, sai ta yawaita.” (A. M. 9:31) Mu ma muna godiya cewa muna da “ta’aziyar Ruhu Mai-tsarki”!
9. Me ya sa koyo game da Yesu zai ƙarfafa mu?
9 A matsayin Kiristoci, koyo game da Yesu Kristi da kuma bin sawunsa sun ƙarfafa mu. Yesu ya ce: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗaukar wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma marar-nauyi.” (Mat. 11:28-30) Sa’ad da muka koya yadda Yesu ya bi da mutane da kirki da ƙauna kuma muka yi ƙoƙari mu yi yadda ya yi, za mu samu sauƙi daga matsi da muke fuskanta.
10, 11. Su waye ne suke iya ba da ta’aziyya a cikin ikilisiya?
10 ’Yan’uwa Kiristoci suna iya ƙarfafa mu. Alal misali, ka yi la’akari da yadda dattawa a cikin ikilisiya suke taimaka wa waɗanda suke fuskantar yanayi mai wuya. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Akwai mai-ciwo [na ruhaniya] a cikinku? sai shi kira dattiɓan ikilisiya su yi addu’a a bisansa, suna shafe shi da mai cikin sunan Ubangiji.” Mene ne sakamakon? “Addu’ar bangaskiya kuwa za ta ceci mai-ciwo, Ubangiji kuwa za ya tashe shi; idan kuma ya yi zunubai, za a gafarta masa.” (Yaƙ. 5:14, 15) Mutane da suke cikin ikilisiya suna iya ƙarfafa mu kuma.
11 Yakan yi wa mata sauƙi su tattauna da wasu mata game da matsaloli dabam-dabam. Mata tsofaffi da waɗanda suka manyanta suna iya ba ’yan’uwa mata ƙanana shawara mai kyau. Wataƙila waɗannan tsofaffi mata Kirista sun taɓa fuskantar irin wannan yanayin a rayuwarsu. Ta wajen saurarawa da kulawa, suna iya taimaka wa ’yan’uwa mata ƙanana sosai. (Karanta Titus 2:3-5.) Hakika, ya kamata dattawa da wasu su “ƙarfafa masu-raunanan zukata” tsakaninmu. (1 Tas. 5:14, 15) Kuma yana da kyau mu tuna cewa Allah ya yi “mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu, har da za mu iya ta’azantarda waɗanda ke cikin kowane irin ƙunci.”—2 Kor. 1:4.
12. Me ya sa yake da muhimmanci mu halarci tarurruka na Kirista?
12 Hanya mai muhimmanci da za mu samu ta’aziyya ita ce halartar tarurrukan Kirista, inda tattaunawar Littafi Mai Tsarki yake ƙarfafa mu. Mun karanta cewa Yahuda da Sila “suka yi wa ’yan’uwa gargaɗi da zantattuka da yawa, suka ƙarfafa su.” (A. M. 15:32) Kafin lokacin tarurruka da kuma bayan hakan, waɗanda suke cikin ikilisiya suna tattaunawa mai ban ƙarfafa. Saboda haka, ko idan muna shan wahala domin wata matsala, ya fi kyau mu kasance tare da ’yan’uwanmu, domin ware kanmu zai sa yanayin ya daɗa muni. (Mis. 18:1) Maimakon haka, ya kamata mu yi abin da manzo Bulus ya ce: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗadda juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.”—Ibran. 10:24, 25.
Kalmar Allah Tana Ta’azantar da Mu
13, 14. Ka nuna yadda Nassosi za su iya ƙarfafa mu?
13 Ko mun yi baftisma ko kuma ba mu daɗe da soma koyo game da Allah da nufe-nufensa ba, muna iya samun ta’aziyya a cikin rubutacciyar Kalmar Allah. Bulus ya rubuta: “Iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyar littattafai mu zama da bege.” (Rom. 15:4) Littafi Mai Tsarki yana iya ƙarfafa mu kuma ya sa mu “zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.” (2 Tim. 3:16, 17) Sanin gaskiya game da nufe-nufen Allah da kuma kasancewa da tabbataccen bege za su ƙarfafa mu sosai. Saboda haka, bari mu yi amfani da Kalmar Allah sosai da littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da za su iya ƙarfafa mu da kuma amfane mu a hanyoyi da yawa.
14 Yesu ya kafa mana misali mai kyau ta wajen yin amfani da Nassosi don ya koyar da kuma ƙarfafa mutane. Bayan ya tashi daga matattu, Yesu ya bayyana ga almajiransa biyu, kuma ‘ya bayyana musu littattafai?’ Babu shakka hakan ya ƙarfafa su sosai. (Luk 24:32) Manzo Bulus ya bi misali mafi kyau da Yesu ya kafa don ya ‘yi mahawara daga cikin littattafai.’ A Biriya waɗanda suka saurare shi “suka karɓi magana da yardar rai sarai, suna bin cikin littattafai kowacce rana.” (A. M. 17:2, 10, 11) Ya dace mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum kuma mu samu ƙarfafa daga shi da kuma littattafanmu!
Ƙarin Hanyoyi na Yi wa Mutane Ta’aziyya
15, 16. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu taimaka da kuma ƙarfafa ’yan’uwanmu?
15 Da akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi don mu taimaka wa ’yan’uwanmu da kuma ƙarfafa su. Alal misali, za mu iya taimakon ’yan’uwanmu tsofaffi ko kuma marasa lafiya wajen yin cefane. Za mu iya taimakon ’yan’uwa wajen yin ayyuka a cikin gida, hakan zai nuna muna ƙaunarsu. (Filib. 2:4) Za mu iya gaya wa ’yan’uwanmu yadda muke son halayensu masu kyau, kamar su ƙauna da gaba gaɗi da kuma bangaskiya.
16 Wani abin da za mu iya yi don mu ƙarfafa tsofaffi shi ne mu riƙa ziyartarsu kuma mu saurare su sa’ad da suke ba mu labarin rayuwarsu da albarka da suka samu a yin hidimar Jehobah. Hakan zai iya ƙarfafa mu kuma ya ta’azantar da mu sosai! Za mu iya karanta Littafi Mai Tsarki ko kuma littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki da waɗanda muka ziyarta. Wataƙila muna iya karanta wani talifi daga cikin Hasumiyar Tsaro na Nazari na mako-mako ko kuma abin da muka koya daga Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya na makon. Muna iya kallon wani faifai na DVD a kan wani jigo na Nassi tare da su. Ko kuma, za mu iya karanta ko ba da wasu labarai masu ban ƙarfafa da muka samu daga littattafanmu.
17, 18. Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai tallafa da kuma ta’azantar da mu amintattun bayinsa?
17 Idan mun lura cewa wani ɗan’uwa mai bi yana bukatar ta’aziyya, za mu iya ambata sunansa ko sunanta a cikin addu’o’inmu. (Rom. 15:30; Kol. 4:12) Yayin da muke jimrewa da matsalolin rayuwa da kuma yi wa mutane ta’aziyya, za mu iya kasancewa da bangaskiya da kuma tabbaci irin na marubucin wannan zabura da ya rera waƙa: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka: ba za ya yarda a jijjige masu-adalci ba daɗai.” (Zab. 55:22) Hakika, Jehobah zai riƙa ba da ta’aziyya da kuma taimaka mana kuma ba zai taɓa yasar da bayinsa masu aminci ba.
18 Allah ya gaya wa masu bauta masa a dā: “Ni dai, ni ne mai-yi maku ta’aziya.” (Isha. 51:12) Jehobah zai yi mana haka, kuma zai albarkace ƙoƙarin da muke yi na yi wa masu makoki ta’aziyya. Ko muna da begen zuwa sama ko kuma begen zama a duniya, bari dukanmu mu samu ta’aziyya ta wurin kalaman Bulus ga ’yan’uwa Kiristoci shafaffu: “Ubangijinmu Yesu Kristi da kansa, da Allah Ubanmu wanda ya ƙaunace mu, ya ba mu ta’aziya madawwamiya kuma da nagarin bege ta wurin alheri, shi ta’azantar da zukantanku ya ƙarfafa su cikin kowane kyakkyawan aiki da zance.”—2 Tas. 2:16, 17.
Ka Tuna?
• Yaya aka yaɗa aikinmu na ta’azantar da masu makoki?
• Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu ta’azantar da mutane?
• Wane tabbaci muke da shi daga Nassi cewa Jehobah yana ta’azantar da mutanensa?
[Hoto a shafi na 28]
Kana saka hannu wajen ta’azantar da masu makoki kuwa?
[Hoto a shafi na 30]
Matasa da tsofaffi za su iya ƙarfafa wasu