Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • we pp. 26-31
  • A Sure Hope for the Dead

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • A Sure Hope for the Dead
  • Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Li’azaru, Ka Fito”
  • Ashe ya Faru Kuwa da Gaske?
  • ‘Allah Zai Kasance da Marmari’
  • Bege na Gaskiya ga Ƙaunatattunka da Suka Mutu
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • “Danꞌuwanki Zai Tashi”!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Begen Waɗanda Suka Mutu Shi Ne Tashin Matattu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
we pp. 26-31

Tabbataccen Bege Ga Matattu

WATA mace mai-shekaru 25 ta rubuto haka: “Cikin 1981 uwata wadda ta goye ni ta mutu daga ciwon cancer. Mutuwarta ya taɓe ni ƙwarai har da ɗan’uwana wanda take goyon mu tare. Ni shekaru 17 ne, ɗan’uwana kuma 11. Na yi rashin ta ainun. Tun da shike an koyad da ni cewa tana sama, to dai, na so in kashe kaina don in kasance tare da ita. Ita ce abokiyata mafi-kyau.”

Ba shi da kyau cewa mutuwa yana da iko ya ɗauka wani wanda ka ke ƙauna. Kuma yayinda ya faru fa, tunanin sāke yin magana, yin dariya da, ko kuwa riƙe hannun ƙaunatacce naka yana da wuyan jimrewa. Ba a kawas da zafin nan ta wurin gaya maka cewa ƙaunataccenka yana cikin sama.

Amma dai, Littafi Mai-Tsarki, yana kunshe da bege da ke dabam sarai. Kamar yadda mun lura da shi ko, Nassosin sun nuna cewa yana yiwuwa ka sāke haɗuwa da ƙaunatacce naka da ya mutu nan gaba bada nisa ba, ba cikin sama da ba a sani ba ne amma a nan duniya ne ƙarƙashin yanayoyin salama, adilci. Kuma a lokacin yan-Adam zasu kasance da zaton more kamiltaccen lafiya, kuma ba zasu taɓa mutuwa kuma ba. ‘Amma lallai wannan zakin tunani ne kawai!’ wasu su a iya faɗa haka.

Minene ake bukata don a tabbatas da kai cewa wannan tabbataccen bege ne? Don ka gaskata da wani alkawali fa, kana bukata ka tabbata cewa wanda ke alkawalin yana shirye da kuma zai iya cika shi. To, wanene fa, da ya yi alkawalin cewa matattu zasu rayu kuma?

A somawar 31 A.Z., Yesu Kristi ya alkawarta da gabagaɗi cewa: “Gama kamar yadda Uban yana tada matattu, yana rayadda su, haka kuma Ɗan yana rayadda waɗanda yake nufa. Kada ku yi mamakin wannan; gama sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru zasu ji muryatasa [Yesu], su fito kuma.” (Yohanna 5:21, 28, 29) I fa, Yesu Kristi ya yi alkawalin cewa miliyoyi da yanzu haka matattu ne zasu sāke rayuwa kuma bisa wannan duniya kuma samu zaton zama bisanta har abada ƙarƙashin yanayoyi na salama, ta aljanna. (Luka 23:43; Yohanna 3:16; 17:3; gwada da Zabura 37:29 da kuma Matta 5:5.) Tun da shike Yesu ne ya yi alkawalin, yana da kyau mu zaci cewa a shirye yake ya cika shi. Amma zai iya yin haka kuwa?

Ƙasa da shekaru biyu bayan yin alkawalin nan, Yesu ya nuna a hanya mai-girma cewa a shirye yake kuma zai iya tafiyadda tashin matattu.

“Li’azaru, Ka Fito”

Yanayi na ban tausayi ne. Li’azaru yana rashin lafiya sosai. Yan’uwansa mata biyu, Maryamu da Martha, sun yi aika zuwa ga Yesu, wanda ke ketaren Kogin Urdun: “Ubangiji, ga shi, wanda kana ƙaunatasa yana ciwo.” (Yohanna 11:3) Sun sani cewa Yesu ya ƙaunace Li’azaru ainun. Ashe Yesu ba zaya so ya ga abokinsa mai-ciwon ba? Da son bincikewa fa, maimakon tafiyar Bait’anya nan da nan, Yesu ya zauna a inda yake na kwanaki biyu kuma.—Yohanna 11:5, 6.

Li’azaru ya mutu bada daɗewa ba bayan da an aikadda saƙon ciwonsa. Yesu ya san lokacinda Li’azaru ya mutu, kuma yana da nufin yin wani abu game da shi. Lokacinda Yesu ya kai Bait’anya fa, ƙaunataccen abokinsa ya mutu ko kwanaki fudu. (Yohanna 11:17, 39) Ashe Yesu zai iya rayadda wani wanda ya mutu ko da daɗewa haka?

Da jin cewa Yesu yana zuwa fa, Martha, mace mai-kuzari, ta ruga ta saɗu da shi. (Gwada da Luka 10:38-42.) Da ya taɓu da baƙincikinta fa, Yesu ya tabbatar da ita: “Ɗan’uwanki zaya tashi kuma.” Yayinda ta furta bangaskiyarta cikin tashin matattu na nan gaba fa, Yesu ya gaya mata sarai haka: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya bada gaskiya gareni, ko ya mutu, za shi rayu.”—Yohanna 11:20-25.

Yayinda ya kai kabarin, Yesu ya umurta cewa a cire dutsen da ke ƙofar kabarin. Sa’annan, bayan yin addu’a da ƙarfi, ya umurta: “Li’azaru, ka fito.”—Yohanna 11:38-43.

Kowa ya zuba ido ga kabarin. Sai kuma, daga cikin dufu, wani siffa ya fito. Ƙafafu da hannayensa a ɗaure da tsummoki, fuskarsa kuma ɗaure yake da tufa. “Ku kwance shi, ku sāke shi,” in ji Yesu. Sa’annan likafani na ƙarshe ya faɗi zuwa ƙasa. I fa, Li’azaru ne, mutumen da ya mutu kwanaki fuɗu ko!—Yohanna 11:44.

Ashe ya Faru Kuwa da Gaske?

An nuna labarin tashiwar Li’azaru cikin Lingilan Yohanna kamar tabbataccen tarihi ne. Daki-dakin sarai suke da ya zarce wani ƙage kawai. Don a tuhume tabbacinsa na tarihi fa zai nufi tuhumar dukan mu’ujizai na Littafi Mai-Tsarki, haɗe da tashiwar Yesu Kristi kansa. Kuma musunci tashiwar Yesu daidai yake da ƙin yarda da imanin Kirista sukutum.—1 Korinthiyawa 15:13-15.

Lallai fa, idan ka yarda da wanzuwar Allah, bai kamata gaskata da tashin matattu ya zama wata matsala gareka ba. Bari a misalta shi: Mutum zai iya karanta wasiyyarsa da kuma abinda yake so na ƙarshe cikin bidiyo, kuma bayan ya mutu, ɗangoginsa da abokansa su a iya gani kuma jinsa, kamar yadda yake, yayinda yake bayyana yadda za a lura da gidansa. Shekaru ɗari can baya, irin abin nan ba wanda ake tsammaninsa ba ne. Kuma ga wasu mutane da suke zama cikin manisantar ɓangarorin duniya, fasahar ɗaukan hoto na bidiyo ya zarce fahimtawarsu kamar wani mu’ujiza. Idan yan-Adam zasu iya amfani da ka’idodin kimiyya da Mahalicci ya kafa don su sāke nuna a fili da kuma murya irin fagen nan, ashe Mahaliccin ba zai iya yin abu fiye da haka ba? Ashe ba daidai yake ba, cewa Wanda ya halicce rai yana iya sāke halicce shi kuma?

Mu’ujizan mayas da Li’azaru ya sāke ƙarfafa bangaskiya cikin Yesu da tashin matattu. (Yohanna 11:41, 42; 12:9-11, 17-19) A hanya mai-taɓuwa fa, ya bayana niyya da kuma sha’awar Jehovah da Ɗansa don tafiyadda tashin matattu.

‘Allah Zai Kasance da Marmari’

Martanin Yesu ga mutuwar Li’azaru ya bayana juyayin Ɗan Allah sarai. Juyayinsa mai-zurfi a lokacin nan ya nuna sarai misalin sha’awarsa na ƙwarai don tashe matattu. Mun karanta: “Maryamu fa, sa’anda ta iso wurin da Yesu ya ke, ta gan shi kuma, sai ta fāɗi a ƙasa a ƙafafunsa, ta ce masa, Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana baya mutu ba. Sa’anda Yesu ya gan ta tana kuka, Yahudawa kuma waɗanda suka zo tare da ita suna kuka, ya ji haushi cikin ruhunsa, yana jin zafi a ransa, ya ce, Ina kuka ajiye shi? Suka ce masa, Ubangiji, ka zo, ka gani. Yesu ya yi kuka. Yahudawa fa suka ce, Ku duba yadda ya ƙaunace shi!”—Yohanna 11:32-36.

An ga juyayin Yesu a nan ta wurin furci uku: “ji haushi cikin ruhunsa,” “jin zafi a ransa,” da kuma “yi kuka.” Asalin kalmomin harshe da aka rubuta aukuwa na taɓuwar nan ya nuna cewa Yesu ya motsu ƙwarai da mutuwar ƙaunataccen abokinsa Li’azaru da kuma ganin yadda yar’uwar Li’azaru take kuka har da Idanunsa suka ciku da hawaye.a

Abin ban mamaki shine cewa Yesu ya rigaya ya mayas da wasu zuwa rai. Kuma a shirye yake sosai ya yi abu ɗaya da Li’azaru. (Yohanna 11:11, 23, 25) Duk da haka, ya “yi kuka.” Saboda haka fa, mayas da yan-Adam zuwa rai, ba mataki ne kawai ga Yesu ba. Juyayi da jiye-jiyensa mai-zurfi da ya nuna a lokacin nan ya nuna sarai girman sha’awarsa don ya kawas da barnan mutuwa.

Jiye-jiyen Yesu mai-zurfi a lokacin tashed da Li’azaru ya nuna zurfin sha’awarsa na kawas da barnan mutuwa

Tun da shike Yesu shine ‘asalin kamanin Jehovah Allah fa,’ daidai ne cewa ba mu a zaton kaɗan daga Ubanmu na samaniya. (Ibraniyawa 1:3) Game da niyyar Jehovah don tafiyadda tashin matattu fa, mutum mai-aminci Ayuba ya ce: “Idan mutum ya mutu zaya sake rayuwa? . . . Zaka yi kira, ni ma in amsa maka: Zaka yi marmarin aikin hannuwanka.” (Ayuba 14:14, 15) A nan asalin kalmar harshe da aka sa “zaka yi marmarin” aikin hannuwanka yana nuna son Allah na ƙwarai da kuma sha’awarsa ne. (Farawa 31:30; Zabura 84:2) Lallai fa, Jehovah ya jira tashin matattun da marmari.

Ashe zamu iya gaskata da alkawalin tashin matattun da gaske? I fa, babu shakka cewa Jehovah da Ɗansa duka a shirye suke kuma su a iya cika shi. Minene wannan ke nufa gareka? Kana da zaton sāke haɗuwa da ƙaunatattu matattu naka a nan duniya amma ƙarƙashin yanayoyi da suka bambanta ƙwarai!

Jehovah Allah, wanda ya soma mutane cikin gadina mai-kyau, ya yi alkawalin sabonta Aljanna bisa wannan duniya ƙarƙashin sarautar Mulkinsa na samaniya cikin hannayen Yesu Kristi. (Farawa 2:7-9; Matta 6:10; Luka 23:42, 43) A cikin Aljanna da za a sabontan nan, iyalin yan-Adam zasu kasance da zaton moriyar rai babu iyaka, yance daga dukan ciwo da cuta. (Ru’ya ta Yohanna 21:1-4; gwada da Ayuba 33:25; Ishaya 35:5-7.) Dukan ƙiyaya, wariyar fata, nuna ƙarfi na kabilai, da kuma zalunci na tattalin arziki ma zasu ɓace. A cikin irin tsabtaccen duniyar nan ne Jehovah Allah ta wurin Yesu Kristi zai tashe matattu.

Tashin matattu, mai-tushi bisa haɗayar fansa na Kristi Yesu, zai kawo murna ga dukan al’ummai

Begen mace Kirista da aka ambata a somawar wannan sashe kenan. Shekaru da dama bayan mutuwar uwarta, Shaidun Jehovah sun taimake ta ta yi nazarin Littafi Mai-Tsarki mai-kyau. Ta tuna haka: “Bayan koya begen tashin matattu fa, na yi kuka. Abin kwashe hankali ne sanin cewa zan sāke ganin uwatta kuma.”

Idan zuciyarka yana marmarin ganin wani ƙaunatacce kuma, Shaidun Jehovah zasu yi farincikin taimake ka ka koya yadda zaka iya maida tabbataccen begen nan naka. Sai ka nemi su a Majami’ar Mulki da ke kusa da kai, ko kuwa ka rubuta zuwa ga adireshi da ke jere a shafi na 32.

a Kalmar Hellenanci da aka juya “ji haushi cikin ruhunsa” daga wani fi’ili ne (em·bri·maʹo·mai) wanda ke nuna zafi ƙwarai, ko kuwa motsu, da zurfi. Wani ɗalibin Littafi Mai-Tsarki ya lura haka: “A nan zai iya nufin cewa jiye-jiye mai-zurfi ya riƙe Yesu har da haushi na babu shiri ya motsa Zuciyarsa.” Furcin da aka juya shi kamar “jin zafi a ransa,” ya fito daga kalmar Hellenanci na (ta·rasʹso) da ke nufin hanzuga. Bisa ga wani mai-ilimin kalmomi, yana nufin “ya jawo tashin hankalin wani na ciki, . . . ya taɓa da zafi ko kuwa baƙinciki mai-girma.” Furcin nan “yi kuka” ya fito daga fi’ilin Hellenanci na (da·kryʹo) wanda ke nufin “zub da hawaye, yin kuka a hankali.”

Tambayoyin Yin Bimbini

  • Lokacinda abokinsa Li’azaru ya mutu, ina yadda Yesu ya nuna cewa a shirye Yake kuma zai iya tafiyadda tashin matattun?

  • Don me zamu amince da labarin Littafi Mai-Tsarki na tashin matattu na Li’azaru kamar lazun tarihi?

  • Ina yadda labarin da ke Yohanna sura 11 ya bayana zurfin sha’awar Yesu na kawas da barnan mutuwa?

  • Minene ya nuna cewa Jehovah Allah yana jiran tashin matattun da marmari?

Matani da Suke Ta’azantarwa

Sau da sau, cikin bayyana yadda suka jure da baƙincikinsu fa, amintatttun Kiristoci sun ce: “Bari in gaya maka matanin Littafi Mai-Tsarki da na fi so.” Idan kana baƙinciki, kila wasu cikin waɗannan nassosin zasu iya taimake ka.

“Albarka ga . . . Uban jiyejiyenkai, Allah na dukan ta’aziya; shi da ke yi mana ta’aziya cikin dukan ƙuncinmu.”—2 Korinthiyawa 1:3, 4.

“Kana buɗe hannunka, kana biya ma kowane mai-rai muradinsa.”—Zabura 145:16.

“Da shi ke [Allah] ya sanya rana, inda za ya yi ma duniya duka shari’a mai-adilci ta wurin mutum wanda ya ƙadara; wannan fa ya bada shaidassa ga mutane duka, yayinda ya tashe shi daga matattu.”—Ayukan Manzanni 17:31.

“Ni dai, ni ne mai-yi maku ta’aziya.”—Ishaya 51:12.

“Kamar wanda uwatasa ta ke yi masa ta’aziya, hakanan zan ta’azantadda ku.”—Ishaya 66:13.

“Wannan shi ne ta’aziyata cikin ƙuncina: gama maganarka ta rayadda ni. Na tuna da hukuntanka na dā, ya Ubangiji, na kuwa ta’azantu. Bari jinƙanka ya zama abin ta’aziya a gareni, ina roƙonka, bisa maganarka ga bawanka.”—Zabura 119:50, 52, 76.

“Gama sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma: waɗanda sun yi nagarta, su fito zuwa tashi na rai.”—Yohanna 5:28, 29.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba