Darasi na 1
Yadda Zamu San Abinda Allah ke Bukata
Wane muhimmin sanarwa ne Littafi Mai-Tsarki ke ɗauke da shi? (1)
Wanene mawallafin Littafi Mai-Tsarki? (2)
Don me zaka nazarta Littafi Mai-Tsarki? (3)
1. Littafi Mai-Tsarki kyauta ce mai-girma daga wurin Allah. Kama ya ke da wasiƙa daga wani uba mai-ƙauna zuwa ga yaransa. Yana gaya mana gaskiya game da Allah—wanda ya ke da kuma mizanansa. Yana bayyana mana yadda zamu jure da matsaloli da kuma yadda zamu sami farinciki ta gaskiya. Littafi Mai-Tsarki ne kaɗai ya gaya mana abinda zamu yi tilas don mu faranta ma Allah rai.—Zabura 1:1-3; Ishaya 48:17, 18.
2. Mazaje 40 ne suka rubuta Littafi Mai-Tsarki a cikin shekaru 1,600, somawa daga 1513 K.Z. Tarin ƙananan littattafai 66 ne. Allah ne ya hure waɗanda suka rubuta Littafi Mai-Tsarki. Sun rubuta tunaninsa ne, ba nasu ba. Saboda haka Allah da ke sama, ne Mawallafin Littafi Mai-Tsarki, ba wani ɗan-Adam da ke duniya ba.—2 Timothawus 3:16, 17; 2 Bitrus 1: 20, 21.
3. Allah ya tabbata da cewa an kofa Littafi Mai-Tsarki daidai kuma an tsare shi da kyau. An rigaya an buga Littafi Mai-Tsarki fiye da kowane littafi. Ba kowa ne zai yi farincikin ganin cewa kana nazarta Littafi Mai-Tsarki ba, amma kada ka sa wannan shi hana ka yin haka. Madawwamin rayuwanka na har abada da ke gaba ya danganta ga sanin Allah da kuma yin nufinsa ko da minene hamayyar.—Matta 5:10-12; Yohanna 17:3.